Part.......17

86 8 0
                                    

*BUTULU*

Writing by
       *Maryam Abduul*

Wattpad@maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
      *BIYAYYA*

*Part....17*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

................Kamar yadda yace mata zaizo kam bayan magrib yazo mata.bayan sungaisane ya kalleta cike da Murmushi kan yace" gaskiya Fatima naji dad'i sosai da naji saqonki akan cewar kin bani dama nazo dan naga batar miki dakaina, nayi farin ciki sosai matuqa, kuma nagode sosai"

"Sannan inafata soyayyata zata sami karbuwa awajenki, bawai saina tsaya yimiki kwana-kwanaba dan nidake dukk ba yara bane munsan me muke ciki me kuma rayuwa ta qunsa"

Fatima ta d'ago idanubta ta kalleahi kan tamaida su qasa kana tace" maganar gaskiya bawai nace kazo nan da na amshi tayin soyayyar ka bane, a'a nace kazo ne dan naroqeka wata alfarma guda d'aya "

"A zahirin gaskiya bana da buri ko murafin qara fad'awa wata sabuwar soyayyar balle tarihi yasake maimaita kansa"

Cikin sauri ya kalleta tare da fad'in " a'a Fatima kada kice haka, kuma ba duka aka taru akazama d'aya ba na rantse miki da Allah bazan ta'ba cutar dakeba"

Fatima ta sake kallonshi akaro na biyu kan tace" dan Allah kayi haquri bazam iya aurenka ba, bazan iya autenkaba kayimin wannan alfarmar ka fita daga rayuwata dan Allah"

Durqusawa yai bisa gwiwoyinsa kan yace" Fatima meye aibina? menene dani wanda bazaisa ki aurenba na miki alqawarin canzawa kamar yadda kikeso, ni dai dan Allah kiyarda dani kiyarda da soyayyata dan Allah Fatima kada ki cutar da zuciyata, ban taba son wata 'ya maceba bana kallon kowacce mace amatsayin wacce zanso sai akanki dan Allah ki dubi buqatata da idon basira"

Ta rausayar dakai gefe kan tace" kayi haquri bawai ina qinka bane, amma kasani zuciyata tayi rauni awannan bangaren banjin zan iya komawa cikin halin da nasata abaya, amma kaji zanyi tunani akan hakan"

Ba yadda yaso haka ya qyaleta bawai dan yagajiba amma yana fata ubanhiji yabashi nasara.sallama yamata kan yawuce.

Itakam Fatima koda ta koma d'aki zuciyarta tashiga saqa mata wasu abubuwa da dama saidai sam batason qara karbar wata soyayya ayanzu domin wacca tai d'in ma gashi yanzu bataji da dad'iba.

Tabbas tasan dr.Auwal bazai ta'ba kawo mata wanda zai cutar da itaba amma bazata iya kar'bar soyayyarsaba dankwa na jinin tama yamata kuma bataji dad'i ba.

Yanzu yazatai da shi, mema zata cewa dr.Auwal tunda shi tawatsawa qasa a idansa, yanzu ita meye mafita agareta?"

Da wannan tunanin ta fad'a bayi dan yin alwalar isha'i.

........Hisham kam ko takan dr.Auwal bai beba ya fad'a motarsa ya wuce gida, kaitsaye falonsu ya baje, zuciyarsa namasa ba dad'i, idan har Fatima taqi karbar soyayyarsa bai son yazai da rayuwarsaba, hawayene yashiga gangaro masa akan kumatunsa.

Maminsa ce ta dafashi ganin hawaye akan fuskar nata kan tace" my son meyake faruwa kuma, meyasa ka kuka haka?, meye damuwarka maza fad'a min?

Batare daya goge hawayen ba ya kama hannayenta kan yace" Mami na rasata tace bazata karbi soyayya taba, yazanyi mami ina cikin matsala taqi yarda dani"

Mamin tace" wace haka son?"

Hisham yace" Fatima nayi duk yadda zanyi taqi aminta dani Mami yazanyi wllh ina sonta sosai ke temakamin"

Mami ta nisa kan tace" shikkenan my sin ka kwantar da hankalinka sannan kullum ina gayama kar kamanta da addu'a aduk sanda wani al'amari yashigema gaba, katuna Allah shine maganin komi, yanzu inaso ka miqa komi gareshi zai baka mafita"

             BUTULU.....Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu