Part......67&68

39 2 2
                                    

   *ZAFAFA WRITERS FORUM*
            Z.W.F.......


          ______BUTULU_____


       NA
Maryam Abdul'aziz.
   (Mai_k'osai).

Wattpad@maryamad856.




Page.....67$68.

Bisimillahir Rahmanir Raheem.



__________Ganin yadda ta rikici sai kuma Saliha taji wani iri, meyasa ta aikata haka?

  Dai-dai lokacin da Na'ima ta shigo, ganin halin da take ciki ya sanyata isowa gareta, saidai kafin ta qaraso abinda suke gudu ya rigada ya faru, dan jinine ya 'balle mata, duk yadda taso shawo kan lamarin ya gagara, hakan yasa bashiri ta d'au  wayarta ta Kira Aunty Aysha akan gasunan zuwa asibitin.

   Suna ISA suka wuce da ita d'akin operation dan abin ya wuce tunani, nan aka sanya mata robar oxygen, tare da bata agajin gaggawa dan ceto ta da abinda ke cikin nata.

   Alhmdulillah anyi Nasara Dan an ciro mata yaranta biyu mace da namiji.

   Nan aka maidota d'akin hutu, su su Na'ima ne suka gyara babies dan sunqi bari a ta'ba su, tunda Na'ima ta d'au namijin take cewa "Hisham na biyu" Dan kamarsu d'aya sak kamar an tsaga kara.

  
     Awarta hud'u kafin ta farfad'o, a hankali take bud'e idanuwanta , Na'ima dake gefenta zaune ganin ta farka yasata matsowa tare da fad'in "sannu Teemah"

  Yink'urin mik'ewa take Na'ima ta dakatar da ita, kukane ya kubcemata itakam lallai akaita wajen Hisham d'in ta.

   Sai a lokacin Saliha ta kuma ganin wautarta da ta tafka tabbas tayi babban kuskure matuqa.

 
   Na'ima ce ta shiga qoqarin ganin ta kwantar mata da hankali cikin lallashi tace " kiyi haquri Teemah , ki yadda da qaddara, sannan ke musulma ce kinsan akwai rayuwa akwai mutuwa, sannan kowanne mai rai mamacine, zaki tafi ,nima zan tafi kowa zai tafi, dan Allah ki daina kuka a halin yanzu Hisham addu'arki yake buqata bawai kukanki ba dan Allah "

    Bata iya cewa komiba, illah kawai gyad'a mata kai da tayi, juyawatai ta koma ta kwanta.


   Ba ita ta farka ba sai bayan awa d'aya, koda ta farka bata ce komiba illa shafa cikin ta datai, cikin sauri tace " ina cikina?"

   Murmushi Na'ima tai tare da d'ora mata babies d'in duka akan cinyoyinta.

   Binta tai da ido tare da neman qarin bayani, sakya murmusawa tai kan tace " duka nakine"

    Kallon yaran Kawai take, take kalaman Hisham suka fad'o  mata "Fatima duk rintsi duk tsanani da wuya kar ki barni, nima bazan ta'ba barin kina, kina nan d'ina " yamata nuni da saitin zuciyarsa.

   Murmusawa tai tare da sakin marayan kuka, "shikkenan Na'ima yarana zasu taso marayu, basu da uba??"

   "Wayace miki basu da uba, ni nan nine babansu koda wasa karki kuma fad'in haka"

  Dr.Auwal ke fad'in haka yayin da yake k'arasowa cikin d'akin.

Gaba d'aya darawa sukai, yaran ya amsa tare da fad'in " ya kamata abani yaran nima na gansu ko"

   'Daukarsu yai nan ya musu hud'uba, inda ya sanyawa yaron Hisham, macen kuma yasa mata Fatima.amma za adinga ce musu hassan da hussaina.

   Sunji dad'i sosai da sunan da ya sanya musu, suna haka akawa Na'ima waya an k'arasowa da gawar.

  Ita dai a yadda ake fad'a mata " ciwon cikin kwana daya ne ya zama silar tafiyarsa" daman hakane kowa da inda hanyar ajalinsa take.

    Batare da ta bari ta fahimta suka neme sallama a 'boye aka sallamesu, suna zuwa ana qarasowa da gawar cikin gidan su Hisham d'in.

             BUTULU.....Where stories live. Discover now