butulu...part 13

112 8 0
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
〰〰〰

Story...writing by
*Maryam Abduul*
  
Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

*Marubuciyar:
   *BIYAYYA*

   
*page....12*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

.........Wad'annan qananun maganganun datake baisa kowa yabi takanta ba.nikam nida Saliha munata sabgoginmu har 'yar qaramar liyafa muka had'a dan tsabar mirnar data addabemu.

Shekara na sakya zagayowa na kammala karatuna na secondary hakan yayi dai-dai da kammala karatun ya Abdallah.

Batare da nasan dahakanbama saida Saliha take gayamin kuma yace" nanda gobe ko jibi zai dawo" baqaramin dad'i najiba sosai kuba komi zanga yayana wanda yadamu dani yake matuqar sona.

Baisamu dawowa kamar yadda yaceba sai da ya qara kwana uku akan hakan sabida sun tsya yin walimar kammala karatun nasu.

Ranar dayataso yayi waya da Saliha yace" mata yataso" nan muka shiga kitchen nida ita muka hau shiryamai abinda zaisa abaki,sosai muga zage wajen shirya abinci yayinda Saliha keta tsokanata wai" basabanba yaya zai dawo za'ahad'o"

Nidai saidai nai murmushi duk danasan bawai ta'ba ganinsane banyiba a'a ina ganinshi a wayar yaya Ihsan idan yaturi mata da pic d'inshi, saidai wani zu'bin bansamun gani dan baqin cikinta.

Wajen qarfe hud'u driver ya tafi d'akkoshi munso muje nida Saliha saidai aikin da mukai duk yagajiyar damu hakan yasa bamu bi drivernba.

Basu wani dad'eba suka qaraso, d'akinshi ya wuce wanda dama nagyara mishi shi sosai nasa turare na wuta mai dad'in qamshi.

Saida yai wanka ya d'an huta sannan ya fito dinning aunty zubaida kam sai wani rawar kai take wai ita d'anta yadawo, yayinda yaya Ihsan ke aikin tayata.

Yanacin abinci yana santi dan bayaban kaiba mun iya girke dan sosai Granny take koyamana wasu abubuwan.mudai dariya kawai muke mashi.

Bayan dayanutsune yazauna yafidda mana da tsarabarmu, amma ni bai baniba yace"bayanzuba" nanfa nadinga turo baki ina qunquni ni ala dole sai yaban tawa.

Salihakam sai dariya takemin, yayinda nahau binta ina saina maketa.nan fa muka hau 'yar zagaye har saida Granny ta tsawatarmana.

Aunty zubaida kam catai" bata yadda yabani kyautar da ba wacca yabawa 'yan uwansace"

Kowa yana mamakin halinta har yanzu takasa sauyawa.yaya Abdallah kam saida akai kwana biyu baiban tsarabata ba nikuma naqi zuwa na amsa dan wata kunyarsa nakeji soaai bansan daliliba.gashi yanamin kwarjini sosai.

Masha Allah ya Abdallah farine amma ba canba sannan yanada wadataccen kyau amma ba wanda yazarce kwatanceba.

Saliha kan takuramin akan wai naje na amso tsarabata, nikam saidai namata banza.

...........Zaune nake cikin riga da wandi na parkistan kayan sunmin kyau masha Allah abinka da farar mace kuma kayan kalar ruwan hudane wato pink, sun min kyau sosai.Salihace tashigo hannunta d'auke da cup tana shan ruwan lipton da yaji kayan qamshi wanda har yazame mata jiki, nima kuma na koya.

Kallo natai tace" wai aunty Fatima bazaki amso mana tsarabarmu bane ko kina baqin naganine?"

Harararartanai nace" bansaniba, wayasanima?"

Ajjiye cup d'in tai tace" nidai gaskiya kije ki amsomana haba dan Allah ni tawa har ta tsufa da ganinta"

Murmushi nai nace" shikkenan ya isa zani, yayi hakan ko"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now