Butulu...6-7

201 9 0
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
   〰〰〰
        

Story...writing by

*Maryam Abdul*

Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all..
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

   Wannan shafin nakune *'yan Da BAZARMU WRITERS ASS*

    Masoyana ina matu'kar ALFAHARI DAKU sosai da sosai.


*DAGA MARUBUCIYAR:-*
    *BIYAYYA*



*page...6-7*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

-------Bakin Titin layin nasu tafito ta sami waje ta zauna, ganin Titin kamar zai Iya fallasamata asiri dan batason Na'ima tasan halin da take ciki ko kad'an, hakan ya sanyata komawa wani lungu share hawayen dake kan fuskarta takeyi zuciyarta na mata d'aci " lallai ba shakka na miji ba Dan goyo bane , lallai na yarda d'an Adam Butulune " wai ita yau ya Abdallah ya kora daga gidansa sabida kawai larurar dake  tare da ita, ita yaiwa wannan cin kashin har da saki.

Wannan tunanin da takeyine yasa har batason yamma ta kawo kaiba, mi'ke watai ta fito bakin layin wta trader tagani nan ta 'karasa tare da rokarsa ruwa zatai alwala. Ba musu ya d'auka ya bata. Nan ta koma ma'buyarta tare dayin alwalar kana tayi sallar.

Sam kwata-kwata batason d'orawa wani nauyinta hakan yasa ta fara tunanin inda zata, sai dai kuma wa tasani agarin nan "babu" tavawa kanta amsa.

Ganin dare nayine ga garin ya yi duhu duk da cewa bawani sosai bane, sai dai unguwar shiru kasancewar unguwar masu dashine hakan yasa kowa na cikin gidansa kuma dayake ba wani yawane garesu ba, takye Fatima ta fara jin wani tsoro ya d'arsu a zuciyarta.

Ganin hakan ne yasanyata fitowa bakin Titin layin kan wani dutse ta samu ta zauna tare dayin ta gumi.

Ganin dare na dad'a yi ga duhu na da'a mamaye wajen yasa tsoro dad'a kamata, take taji wasu zafaffan hawayen sun sauka akan kuncinta nan kuma tunanin tilon 'yarta da tarage mata wato Basma ya fad'o mata arai, sai yanzu take da nasin rashin tsayawa ta d'akko ta, yanzu batason awani hali takeba amma ba makawa ta tabbata tanacan tana aikin kuka kuma tasan bawani mai rarrashinta, sai dai bazata ta'ba komawa ta d'akko ta Dan Sam batason abinda zai sadata da Na'imarta.

Wajen 'karfe goma na dare ta na nan zaune sai dai cikin zuciyarta fal cike yake da d'unbin tsoro, duk motar da tazo wucewa kam sai dai ta wuce a guje hakan ya dad'a tabbatar mata da bawanda zai temaketa, lallai in tace" anan zata kwana tana cikin had'arine Dan batason dawa zata had'u ba" wannan shine tashin hankalina da ba'a samasa rana.

Wata motace naga tajuyo bacin wucewarta, fitowa akai daga cikin motar, har mutumin ya 'karaso inda take amma batason yazoba, sai dai jin tsayuwar kamar wani abun yasata saurin d'ago kanta Wanda ta cusa tsakani cinyoyinta.

Karaf sukai ido hud'u dashi, bakowane ba face Dr.Auwal.cikin murya ta nutsuwa yashiga rok'onta da tabishi zuwa ga Amminsa Dan tabbas yasan tana cikin wani hali..

Da farko taso 'kin amincewa amma duba datai da in dare ya sakya yimata anan tana cikin babbar matsala yasanya ta amincewa da bu'katarsa, gashi batason inda zata ba batason kowa ba.

Ya Abdallah ne kad'ai Wanda tasani acikin garin Kano shine mutumin da yakawota wannan garin, kuma tunda suka zo  ya amshe wayarta ko gaisawa zasuyi da ahlinta sai dai yabata wayarsa daga bayama in tanema sai yace mata" ai suna gaisheta" ko kuma ya hanata acewarsa " wata rana zataji tausayin su tasanar dasu inda suke shi kuma baiso kodan Mahaifiyarsa da batason auren" haka nan ta ha'kura ta zubawa sarautar Allah ido.

             BUTULU.....Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin