BUTULU...part 29

54 4 0
                                    

*BUTULU*


By
*Maryam Abduul*

*Wattpad@maryamad856*
*Face book@Maryam Abduul*


💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫


Daga Marubuciyar
*Biyayya*


*Part......29*


BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


********************Sanda ta fita har takai wajen motarta tana shirin tada ta, cikin azama ta qarasa wajen tare da qwanqwasa mata glass d'in motar.

Kallon glass d'in tai kan ta d'auke kanta, cikin sanyin murya Fatima tace" ki bud'e qofar nan" duk da bataji me taceba amma ta fahimta ta kallon bakinta datai, hakaan yasa ta bud'e qofar ba tare data fitoba.

Hannu Fatima tasa ta janyota alamar ta fito hakan yasa ta zuro qafafuwanta tare da fitowa daga cikin motar sai dai ko kad'an fuskar tata ba fara'a sam atare da ita.

Murmushi Fatima tai kan tace" wai to duk wannan had'a ran na menene?"

Ba tare data kalli inda takeba tace" nima haka na gashi"

Murmushi dukansu sukai banda Na'ima, nan ta maida murfin motar ta rufe.ciki suka shiga Ammi kam data gansu sai sukama bata dariya.



Ko a d'aki ma zuba junansu ido kawai sukai kaf ba wanda yace uffan sai da Fatima ta saukewa Na'ima tagumin datai kan tace" wai dan Allah sisy meye damuwarki ne da nayi alwashin bazan sake tuntubarki ba akan wannan batu sai dai hankalina ya gaza kwanciya dan Allah ki daure ki sanar dani komene"

Sauke ajiyar nunfashi tai kan tace" kiyi haquri ni kaina bansi har takai hakan ina me 'boye mikiba sai dai ba yadda zanyi hakan shine mafita amma yanzu inajin nima in ban gaya mikiba hankalina sam bazai kwanta ba"

Ta d'ora da fad'in" Teema ina cikin wani hali na san maso wani, zuciyata ta dad'e da kamuwa da san dr. Sai dai ban san ya zanyi ba, wannan ne kad'ai damuwata"

Murmushi Fatima tai kan tace" haba sisy dan wannan kawai shine kika bi kikasa kanki cikin damuwa, ki kwantar da hankalinki insha Allah zaki aute dr da yardar Allah zai soki fiye da yadda kike tunani"


Kallonta tai kan tace" taya hakan zai faru kinsan dai bai ce yana sona bare har nasa ran zai auren?"

Fatima tace" kwantar da hankalinki sisy komi yazo qarshe"

Cikin sauri Na'ima ta riqo hannayenta kan tace" a'a sisy banaso kije masa da tayin soyayyata garesa dan Allah karma ki soma haka"

Fatima tace" ai nima ba haka nace miki zanyiba kedai ki cigaba da addu'a ki kuma sanya ido kawai"

Na'ima ta sauke ajjiyar nunfashi kan tace" shikkenan zanyi duk yadda kikace"


Fatima tai dariya kan tace" ah kaga su dr da kanta, wai wayaga"

Cikin sauri Na'ima ta jefeta da filon dake kan gadon da take zaune gaba daya sukasa dariya tare da kallon junan su.

Suna haka Salma tashigo da yake ita bata biyosuba sanda sukayo d'akin, ganinsu cikin haka yasata itama tuntsitewa da datiya tare da nunasu da dan yatsa, kan kacemi tuni sun tuntsire da wata sabuwar dariyar wacce sukansu suma basuyi tunanin hakanba.




*******Rayuwa nata garawa yayinda da take juyawa dasu Ammar sam basa samun nutsuwa da kwanciyar hankali zaman gidan na neman ya gagresu duk ta dalilin Tabawa ta takuramusu matuqa.

Malam Audu kam baya takansu shidai burinsa kullum ya ganshi tare da Tabawa, a yanzu kam baisan cinsu da shan suba, ba abinda yake musu kwata-kwata.


Kamar ko yaushe Ammar ne gaban Mama Suwaiba idansa cike taf da qwallah, sai dai gudun kar maman nashi ta shiga cikin damuwa yasanya shi dole shanyeta badan ransa yasoba.


Sauke nunfashi yai kan yace" yanzu mama haka zamu zuba musu ido muna kallo sun maida gida kamar ba gadan mu a ciki"


Mama Suwai ba tabkalleshi cike da murmusawa kan tace" to yazamuyi Ammar haka zamu cigaba da haqurin da mukeyi dai wata rana sai labari"


Cikin fushi yace" mama wai meyasa da anyi abu sai ace haquri haquri shikkenan kuma sai adake bawa a hanashi kuka haka rayuwa ta gada"


Mama suwaiba ta dafa kanshi kan tace" hakane Ammar amma kamar yadda nace ma wata rana sai labari zaka gani kai dai kaci gaba da addu'a Allah zai kawo mafita, yanzu maza kaje wajen sana'ar taka"


"Ai mama ni yau ba inda zani ma gaskiya tunda in nama fita ba ciniki nakeba kinga jiyama haka na dawo ko sisi ba aiba"


Batare da tace masa qalaba ta jinginar da kanta jikin banhin dakin tare da furta" hasbunallahu wabi'imal wakilu"

Ganin hakan yasa shima jinginar danasa tare da lumshe idanuwa nan bacci yai awon gaba dashi.


Mama suwaiba kam tsura mai ido tai tana mai nema musu sauqi wajen Allah.





********Abdallah zaune cikin falon nasu gabansa system ce sai dai azahirin gaskiya sam ba aikin yakeyi ba tunani kawai yakeyi cikin zuciyarsa, "wannan wace irin rayuwa ce haka, ayi mutum ba zama cikin gida, tabbas ko sanda suke da Fatima bata wannan yawon duk inda zata sai da izininsa idan yace" a'a " to kwa ba inda zata, amma ita wannan sam bata damu da fushinsaba , idan ma yayi fad'an abanza"



Turo qofar da akaine yasashi d'aga kansa sai dai ganin Sabir yasashi fuskantar abinda yakeyi dan ko kadan baisan yasan yana cikin wata damuwa, domin kwa yasan dariya ce kawai zaisha ta wajensa.



"Ah aboki yau ba office kenan naganka gida?" Sabir ya tambayeshi cikin zolaya.


"Uhmm waya sani" Abdallah ya bashi amsa ataqaice.


Cikin had'e fuska Sabir yace" kaga dakata ni bance kamin wannan banzan halin nakaba, ina matar hidan ne nifa yau wllh gara nazo dauka"


Ba tare da yace" masa uffan ba" yabtattara komi nasa ya haura sama, shima Sabir din miqewa yai tare da mara masa baya, cikin zuciyarsa kuwa yana zargin abubuwa da yawa.




*Kuyi haquri fans wllh ciwon ido ya matsamin bana iya typing sosai hakan yasa nace zan rage yawan page insha Allahu dan samun damar kawo muku cigaban littafina*

*Ina barar addu'ar ku gareni, fatan alkahiri gareku masoyan asali*

Comment and Share......

*Mrs.Abduul ce*.........

             BUTULU.....Where stories live. Discover now