Butulu...part39&40

32 2 0
                                    

                BUTULU

By Maryam Abdul'aziz
            (Maryam Abdoul)

follow me on wattpad @Maryamad856.

Part......39&40.

.............Daddy zaune kan kujera yayinda ya tasa computer d'in SA agaba magana naji yanayi, HAKAN ya tabbatar min da cewa"video call" yakeyi.

  "Da gaske daddy ,da gaske Aunty Fati ta bata, da gaske yaya ya koreta daga shinyarsa?"

   Tambayoyin da naji Ana ta jero mai, kallon na'urar nai fuskar Saliha Na gani, sai goge hawaye take, cikin zuciyarta kwa wani qololan abune ya taso yazo maqogwaranta ya tsaya.

    Saida ya dai-daita nutsuwar, tabbasa shima yasan wannan shine Abu mafi tashin hankali acikin family nasu tun bayan rasuwar *Maimuna* yanzu kuma *Fatima* ta bata 'ya gareta, wacca suke matuqar so da qauna.

   Kallonta yai cikin Ido kan yace"shiyasa naqi sanar dake sabida da dad'ewa Na Riga da nasan halinku, shine kuma kikemin kuka, kisani har yanzu ba Wanda yasan da zancan saini sai shi, Dan haka yanzuma inaso ki 'note maganar har lokacin da za'a ganota"

   "Amma daddy baka ganin......"

Da sauri ya taro nunfashinta, "bana ganin komi Saliha ,addu'a itace komi, kuma shima Na matsamai akan lallai inason ganin 'yata, anjima zan koma duk yadda ake ciki zamuyi magana, kada ki manta banason kowa yaji maganar nan"

Cikin sanyin jiki tace"to daddy insha Allahu, kuma zandage da addu'ar, Allah ya bayyana mana ita"

  "Ameen, ko kefa" ya fad'a shima a sanyaye.daga nan suka katse kiran.

Jitake inama zata iya zama tsuntsuwa tazo Tai Ido da yayan nata, wani IRIN baqin hali da *butulci* ya koyo haka, meyasa zai aikata wannan d'anyen aikin.

Daddy kam tattara komatsansa yai ya fad'a bayi, Dan yin wanka ya fita zuwa wajen maciyi amanar can.

............Affa kam koda ta shige gidan cille ta farayi da duk abinda taci karo dashi, hakan yaja hankalina aminiyarta fitowa Dan Mamansu bata nan.

Cikin azama ta riqo ta ganin ifiritan nata basu tsayaba yasata wanka mata lafiyayyan Mari a fuskarta "Dallah malama ki nutsu meyafaru"

  Batasan lokacin data fashe da kuka ba tare da sunbatun masifa" ni Ammar zai cewa amana, ni zai yaudara, Wllh daga kaina bazai kuma cin amanar wata ba"

  Murmushi Tai lokacin data gano mafarin lamarin, "yanzu akan wannan kike hauka Affa?" Muje daga ciki, hannunta ta ja sukai cikin d'akin.

  ........Da qyar yasamu ta fito Dan zuwansa hud'u taqi fitowa, wannan dinma Hajiya ce ta matsa mata sannan ta fito.

  Bata San shi Dan bata ta'ba ganinsaba sai Yau, hakan yasa taja dinga ta tsaya.

Murmushi yai kan yace" malama Na'ima ina fata ban takura miki ba?"

   Cikin qaguwa tace "kusan hakan"

Murmushi ya koma Saki kan yace"nazo nan ne ta hanyar mijin qaqarki kuma 'yar uwarki Fatima"

Jin zancan Tai wani yar, cikin zafin nama ta juya zata koma, shima cikin zafin nama yace" nazone ba Dan shiba sai Dan ahlinta, nazo nan NE amatsayin yaya agareta"

   Ba tare da ta juyoba taja daga ta tsaya, hakan yabashi damar tattakowa ya qaraso inda take.

  " Tabbas kamar yadda nace miki hakane ba sauye a zancena, nazo Dan ahlinta kuma mahaifi agareta Wanda ya Jima yana whalar nemanta ,daddy yana garin nan kuma shi yasa Na nemota, hakan yasa nabi dididigi wajen Abdallah nasan adreess Na gidanku har nazo gareki, ina fata zaki temaka min ki hutar da daddy wahalar da yake ya samu sa'ida"

  Goge qwallar data zubu mata tai bawai Dan komiba sai Dan yadda yace mata" ahlin Fatima na nan kuma suna ta nemanta" juyowa tai ta kalleshi kana tace" namaka alqawari had'aka da Teemanah, amma bisa sharad'i d'aya "

  "Duk abinda kikeso zan miki muddin be kauceea addiniba Mene sharad'in"

  Na'ima ta nunfasa kan tace"INASO ka fara Kaine wajen daddy nayi tozali dashi kan Na bayyana muku Teemanah"

  "Shikkenan indan wannan NE Na aminchi, yanzu in kin shirya bisimillah"

  "A'a kaje sai gobe, amma banaso maciyi amana yasan da zancan Fatima Na nan hallau"

  "Shikkenan godiya nakeyi" yana gama fada'ar haka sukai sallama akan gobe by 10 suna wajen daddy.

Sosai tai farin ciki da Jin cewa" wani ahli Na Fatima yana Kano, kuma yazo Dan ya ganta", to amma ko kad'an bataso Fatima tai nisa dasu, duk da nasan Hashim zai zama silar zaman ta tare dasu Na har abada.

 

............Ammar ne a waya ke sanar da Mansur abinda ya faru.

  Cikin rarrashi ya shiga bashi haquri da baki akan yai "haquri komi me wucrwa ne, tayo daman can ba matarsa bace, yayi addu'a Allah ys HK shine mafi alkhairi agreshi"

  Da haka yasamu kan Ammar, shima sosai yaji dad'in maganganun da Mansur ya masa, sai yaji kaso 60% Na damuwarsa ya ragu, amma tabbas dole yai nisa da garin shima zaije ya tsaya da qafafunsa, insha Allahu, alwala ya tashi yayi sannan ya hau sallah Dan kai kukansa ga mahaliccinsa.

Mansur kuwa farin ciki yai Dan shi daman Sam baison alaqar Ammar da Affa.sai dai yadda yaji Ammar d'in sai yaji inama hakan bata faruba, amma ya za'ai da hukuncin ubangiji.

   Da dare Ammar yajewa Mama Suwaiba da yadda sukai da Affa, itama haqurin ta shiga bashi tare da tausasa masa zuciya, kamar yadda Mansur yai d'azun.

  Nan ya shiga gaya Mata hukuncin da ya yanke game da barin garin nasu Dan neman abin yayi.

 

Vote........

*Mrs.Abduul ce*

 

             BUTULU.....Where stories live. Discover now