part.....20

72 2 0
                                    

*BUTULU*

Writing by
      *Maryam Abdul*

Wattpad@maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫

We are here to make you happy, smile, and educated to realized that we are the best among all.......*DA BAZARMU MUKE TUNQAHO*

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
     *BIYAYYA*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

*PART......20*

................Sanda ya fito tana zaune tana ta ta danne-danne awaya, saida yagama siryawa kan yazauna cin abincin

Ba laifi abincin yayi dad'i, kallonta yai yace" Allah yasa yadda abincin nan yai dadi haka kika iya dafawa"

Murmushi tai kan tace" haba ai yamafi wannan, kaidai kajira randa zan dafama zaka banbance ai"

Yai murmushi kan yace" banda zuga kai dai"

Itama murmushin tai kan tace" dagaske bazauga kai na nakeba, Allah dai yakaimu lokacim"

Amsa mata yai kawai da "ameen".


............Na'imace gaban Hajiya tana gyara mata farcen qafar ta, kallonta tai kan tace" hajiya in badamuwa inason yau na leqa wajen Fatima, dan akwai muhimmiyar magana danakeso muyi da ita"

Hajiya ta d'anyi murmushi irin nasu na manya kantace" Na'ima kenan wace maganace haka, amma ina fata ba akan Auwal bane ba ko?"

Na'ima tai saurin dagowa ta kalli Hajiya kan tace" kai hajiya ni ba wannan bane, jiyane mukai magana da shi awaya yake cemin wani abokinsa yana son Fatiman amma sam taqi bashi hadin kai taqi yarda dashi , shine yace dan Allah na temaka musi da wani abun mana"

Hajiya ta sauke ajjiyar zuciya kan tace" amma naji dad'i sosai, sai dai kinsan Fatima yanzu sai anmata uzuri dalilinkwa abinda ya faru da ita, sabida kina gani jininta shi yamata butulci ya gujeta to tana ganin bawanda ma bazai mataba, amma kije din ki gayadda abin zai kasance"

Na'ima tace" hakane, nima inafata hakan yafaru dan na tabbata dr.Auwal bazaiso abinda zai cutar da itaba, shiyasama nace masan zanzo insha Allahu"

Hajiya tace" to Allah yatemaka dai, amma ki tafi da Basma inyasoma ki barta tadanyi kwana biyu acan"

Na'ima jin ance tatafi da Basma yasata yin jim, harga Allah batason abinda zai rabata da Basma ko nan dacan, gashi Hajiya nacewa takaita tayi kwana biyu tana matuqar son yarinyar sosai"

Kallon hajiya tai tace" shikkenan ba komi"

Ba ita tabar gidanba sai wajen sha biyu na rana, sanda taje Fatima na d'aki dan Salma bata nan taje yin siyayya.

Bayan sun yi sallah ne take yimata d'an tsokaci akan zancen da yakawota.

Fatima ta kalleta tace" Na'ima wllh ko kad'an banajin zan iya saka yin wata soyayya bayan wadda nai, kinsani dai an zaluncine iya zalunta ina tsoron sake fad'awa cikin wani halin"

Na'ima ta harareta kan tace" to angaya miki soyayyar dake kai abaya iri dayace da wannan, wllh na tabbata bazai ta'ba cutar dakeba dan Allah Fatima ki aminci da soyayyar sa badan muba sai dan Allah"

Fatima tanisa kan tace" Na'ima bazaki ta'ba ganewa ba amma ayanzu banda tsarin wata soyayya arayuwata"

Na'ima tace" ai kam har abada bazan ta'ba ganewar ba, nidai nagaya miki ki zauna kiyi tunani kinsan dai bazaki ta'ba zama bakiyi aureba, to ba gwara ki aure wanda kikasan saba kinsan wazaki aura nan gaban, kodai kina son kicemin kinason komawa gidan tsohon mijinki?"

Fatima tace" haba Allah ya kiyaye, meyakawo wannan maganar ke kuma, naji zanyi tunani akai"

Na'ima tace" ah to gwara dai kisan inda yake miki ciwo dai"

Fatima takai mata duka kan tace" au da bansaniba kenan"

Na'ima tace" da alama kam"

Nan suka cigaba da hirarsu, suna haka Salma ta fad'o, nan tashiga aka cigaba dayi da ita.

Na'ima bata bar gidanba sai bayan isha'i dan dr.Auwal nema yakaita.aikam baqaramin dad'i tajiba sosai.



............Malam Audu gaban mahaifiyarsa yana roqonta akan ta yarjemasa auren nan da zaiyi.

Kallonshi tai kan tace" ni bansan yaushe ka koma haka ba , waima to dame zakayi auren a ina kasamo kudin ?"

Ya d'an rassanar da murya kan yace" wani aiki nayi sosai shine nasami kudin, kuma daman ba wani kudi mai yawa muaki da ita akan sadakinba, nidai dan Allah kayarjemin Inna nai wannan auren"

Inna ta kalle shi tana jin jina hali irin na d'an nata kan tace" shikkenan zan yarda amma bisa sharadin cewa sai naji daga matarka inta aminci to inkwa bata aminceba to wllh bazaka yi auren nanba, ban kumace kaje kasata agaba ba inkai hakan zan sani danni ba qaramar yarinya bace, kuna fama da rashi kai kana qoqarin yin aure da wanne zataji"

Shidai baice komiba saima bata baki dayake akan tadai yarda da auren nasa"

Koda yabar gidan kaitsaye wajen bazawar tasa yawuce, nan suka shiga aikin hirar su.

A gida kam takanas Inna taje tasami Suwaiba akan maganar auten da Audun yazo mata dashi.

Iya kaduwa tayi sai dai ta danne hakan dan batason Innar ta fahimce wani abu, hakan yasa tace" da amincewarta ma, tasan damaganar auren"

Ita dai Inna badan wai asoba ta yarda itama, tare da sawa Suwaiba albarka.

Koda Inna ta bar gidan sosai tai kuka, kenan daman kudin da yasaida tumakin ba sana'ar zaiyi dasu ba, aure zaiyi Innalillahi wa'inna ialihir raji'un" shine abinda kawai take maimatawa, "tabbas lallai d'an Adam butulu ne meyasa zai mata haka, mai yasa zai ha'inceta, meyasa zai yaudareta haka?

Tana cikin wannan halin Ammar yashigo koda yashigo yaganta ahaka baqaramin tashi hankalinsa yaiba, hakan yasashi matsawa kusa da ita tare da riqo hannunta yace" mama mai yafaru lafiya kuwa?"

Cikin kuka tace" Ammar babanka aure zaiyi, aure zai qara"

Cikin rudu Ammar yace" aure kuma Mama, da wane kudin zaiyi muna cikin wannan halin na quncin rayuwa kuma?"

Suwaiba tace" qwarai aure zaiyi badan kufin kowaba sai wanda nace yasaida tumakaina yaja jari, ashe daman akwai abinda yataka, ashe daman duk kukan talaucin dayakeyi da walakin goro amiya badan Allah yakeyiba"

Ammar ya dafe qirji kana yace" tumaki kuma Mama, garin ya hakan tafaru, meyasa zaki bashi tumakinki ya saida?"

Suwaiba tace" tsautsayi shiyasa na bada, amma malam ya ci amabata ya cuceni, bakomi yaje dan kansa yaje shi da Allah"

Ammar yace" a'a Mama, kije ki gayawa Inna nasan zata yimai iyaka da wannan maganar"

Girgiza kai tayi kan tace" ai aikin gama ya gama Ammar itace ma take sanar dani aute zaiyi, yaje mata da zancen tace bazata amintaba sai taji ta bakina, kai ma kasani koda nace a'a to ba haqura zaiba, kuma da ace yau gashi awaje yana aikata badai-dai ba ba gwara na amince yai aurenba, shiyasa"

Ammar ya jinjina wannan al'amari kan tace" kiyi haquri mama, wata rana sai labari, komi lokacine kuma komi zai shige, kedai kicigaba da yiwa baba biyayya, in Allah yayarda zaki cimma burinki, koma nasan zaiyi alfahari dake, ki riqe wannan sirrin kada ki bari zufar mutane tasa kiyi abinda ba dai-dai ba dan Allah mama"

Suwaiba tace" naje d'an nan Allah yayi maka albarka, tashi kaje ka d'au abincinka kaci, kada kasa damuwa aranka"

Nan ya miqea tare da sake bata baki, wannan maganar kuwa Ammar da ita yakwana azuciyarsa ya dad'e yana jimanta wannan al'amari.

Editing is not allow....

Vote,
Comment,
Share and Like......

*Mrs.Abduul ce*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now