BUTULU...part 28

60 2 0
                                    

*BUTULU*

By
*Maryam Abduu*

*Wattpad@maryamad856*
*My face book@maryam Abduul*

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫

Daga marubciyar
*BIYAYYA*

*Part...... 28*

Bisimillahir rahmanir raheeem.

****************" hmmmm Na'ima kenan najima da sanin cewa lallai akwai abinda kike 'boyemin sai dai bazan tilas tamiki akan ki fadan ba amma kisani daga yau kada ki qara nuna cewar kinsan ne balle magana ta had'a mu har kice zaki fahimtar dani wani abun kisani akan hanya"

Na'ima ta kalleta cikin sanyin jiki cikin zuciyarta na gayamata cewar" kata sanar da ita, dadin dad'awa ma agaban qanwarsa" danne hawayen da suka maqale mata tai kan tace" nifa ba abinda yake damuna duk kunbi kun sani atsakiya, inma akwai me zaisa na 'boye muku, kufa d'in 'yan uwanane abokanan shawarata mezaisa na 'boye muku damuwata"

Fatima tai yaqe wanda iya kacinsa fatar baki kan tace" haka dai kika ce, amma karki manta ni dake kar tasan kar ce dan haka nasan damuwarki da kuma rashinta"

Na'ima ta matso kusa da ita da zunmar riqo hannayenta cikin zafin nama Fatima ta janye hannayen nata tare da miqewa tai waje.

Ganin hakan yasa jikinta yai sanyi tabbas tasan Fatima tasan damuwarta amma bazata iya gayamata ba sam, yanzu ya zatai.?"

Salma ce ta dafata kana tace" aunty koni kwana biyun nan da kikai na fahimce cewa kina cikin damuwa, dan Allah koni baki gayanba ki daure kisanar da aunty Fati nasan ko bata miki maganiba zata taya ki da addu'a kuma nima zan miki, maza kije ki rarrasheta."

Jin hakan yasa Na'ima sakin murmushi tabbas tasan kowa zai iya fahimtar ta dan gaba d'aya yanzu bata da wani kuzari ko walwala, tunani ne kawai aikinta.

Ahankali tayi falon cikin gidan, zaune ta taddata tana waya da alam cigaba tai da wayar ta tata.

Kusa da ita ta samu ta zauna tare da tiqo hannayenta cikin nata, ganin hakan yasa Fatima d'aukar uzuri wajensa.

Kallonta tai kan ta kauda kanta gefe , murmushi Na'ima ta saki kan tace" kiyi haquri sisy nasan nayi laifi amma kisani sam bayin kaina bane kuma na kasa gaya mikine shiyasa amma plz bazan kuma ba"

Fatima tai qwafa tare da bankamata harara kana tace" aini daman bance kinmin laifi ba balle kizo kiban haquri, maganar kasa gayamin kuma ban tunanin akwai abinda zaki iya 'boyen hakaba, amma tunda kin za'bi hakan to kije ki riqe kayanki banason sani"

Na'ima ta sauke ajjiyar zuciya kan tace" dan Allah ki fahimceni Teema banyi haka dan 'bata rankiba kodan wani abu ba a'a dan Allah ki tausayamin mana"

Fizge hannunta tare da miqea dan barin falon ba kuma tare da tace mata" ci kanki ba"

Ganin hakan yasa itama Na'ima miqewa tare da kamo hannayen Fatiman ta maidata kan kujerar, ido cikin ido sukai kan Na'ima tace" nasan daman bazaki fahimceni ba yanzu amma hakan inaso kisani banyi hakan dan 'bata ranki ba na barki lafiya" tana qarasa fad'a ta miqe tare da barin gurin.

Fatima kam sai da tashe mintina goma zaune awajen tana tunani kan daga bisani ta miqe zuwa sashen Ammi.

Na'ima kam tana shiga d'aki taji zaman gidan ma gaba d'aya ya gundereta sosai, hakan yasa ta tattara kayanta cikin akwatin datazo dashi tare da zugesa.

Salma na ankare da ita harta gama had'a kayan, ganin tana qoqarin barin d'akin saurin shan gabanta tace" aunty lafiya kuwa, ina zaki da kaya haka?"

Na'ima ta janyeta gefe kan tace" gwara nabar gidan Salma banason 'bacin ran Teema ki kad'an, zan tafi na bata waje dan tasha iska ko ta huce"

Salma tai sautin dawowa inda take da farko kan tace" wllh ba inda zaki aunty haka tace miki tana fushi dake?"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now