Part...51&52

47 5 14
                                    


     ******BUTULU




      NA
Maryam Abdoul
   *(Mai_'Kosai)*




   Wattpad@maryamad856.


Part.....51/52


Typing.........



Bisimillahir Rahmanir Raheem.



_______Tace " ka rigada ka makara ya Abdallah, banjin sonka ko kadan a cikin zuciya ta, koda ace Saki be shiga ba to tabbas sai ka sake ni na aure burin zuciya ta, ka rigada ka yar da damar ka, ka manta sanda nake roqonka Allah da Annabi amma kai burus dani, sai yanzu da na sami lafiya kasan da rayuwa ta , dan Allah kafita daga rayuwa ta"

Ta qarashe tana me had'a hannayen ta biyu.

  Kan yai wata magana Daddy ya rigashi da fad'in " to kadai ji da kunnen ka, wllh koda Fatima ta haqura ni bazan haqura ba cin zarafi da akawa ya ta ba, dan haka kaje KAYI rayuwar ka muma ka manta damu a rayuwar ka"

" Ku tashi muje " Daddy yace ransa na qara quna, zuciyar sa na tafasa.

   Daf da zasu fita ya riqo hannun Fatima lokacin su Daddy da granny sun fita, cikin zafin nama tasa hannu ta make hannun nasa, "ka manta nidin mazinaciya cea bariki nake yawo, kar na shafa ma qanjamau "

   Ko kalma daya bata bare yace ba tai maza ta fice daga falon.

Naima ce tace " yallabai alaramma sai a qara haqori, dan Teemah ta ta wuce gaban ka sai dai kallo" ta qarashe tana dariyar mugunta.

Saliha kam ko kallon inda yake batai ba itama tasa kai tabar falon.


Wani gumi ne ya shiga keto masa duk da sanyin falon amma hakan be hana zufar ketowa ba, "ina Wllh bazai yiwuba, ba Wanda zai rabani da matata" ya fad'a yana dukan bangon falon.

Sabir me ya dafa shi cike da San magana, cikin zafin nama Abdallah ya ture hannunsa ransa a bace fuskar nan tamkar an daure damo ya kalleshi yace "dallah da kata munafiki, duk abinda ya faru ba Kaine sila ba wayasan me kaje ka kulla sannan ka shigo dasu, Wllh ko zanyi yawo tsirara sai na dawo da mata ta "

Shi dariya ma maganar taso bashi amma ya dake yace " nida kai aga munafikin, Wanda ya fara ta'assasa laifukan , tabbas inaga kuwa zaka fara yawo ba kaya dan Fatima ta rigada ta ma nisa"

  Yana fad'in haka yasa kai ya fice ,yana jiyoshi yana fad'in " munafikin banza me raba kan iyali Allah ya isana kuma sai kasan Wanda ka tabo"

  Shidai dariya Kawai yake yana mamakin irin qarfin halin Abdallah, yayi dukan amma shine da kuka.



       %

******Tas ya cinye abincin, yana gama ci  ya neme ruwa ya sha, nan ya koma inda ya fara zama Dan dorwa daga inda ya tsaya, sai dai kuma tunanin sane ya tsaya akan inda zai samu ya kwana gashi besan Kowa ba.

Mazan da ya tambaya inda zai sami abinci, su ya kuma nufa " Dan Allah ina zan sami gidan hayar da zan kwana a cikin na biya??"

  Kallon sa sukai tare da sakin murmushi daya daga cikin sune yace " da alama kai baqo ne ko"

  "Ehh " ya basu amsa.

"To gaskiya dai Babu gidan hayar kwana daya anan, amma in bazaka damu in zaka bemu gidan mu wajen maman mu sai ka kwana in yaso sai asan abin yi"

Shiru yai bece komi ba har tsawon wasu mintina.

  "Nasan ba lallai ka aminta damu ba amma inaso kayarda da Allah, tunda muka ganka mukaji ka kwanta mana arai, mu biyune amma kowa mahaifiyarta daban kuma haka Muke zaune wajen maman mu ita take dawainiya da mu, mukan fito mune me abinda zamu dinga temaka mata, muna zaune a nam Zoa road cikin hausawa, in ka gamsu bisimillah muje"

Ya qarasa yana nuna masa hanya.

Tunda ya soma magana sai yaji Kawai zuciyar sa ta aminta da su, "Na amince" yace a hankali.

Kayan sa ya  d'auka, nan suka tsaida me napep suka hau, suna tafe suna hirarsu amma shi tunanin halin da zai tsinci kansa nan gaba Kawai yakeyi.





      %

*******Ai wllh naso  bada su Daddy muka je ba, Allah sai na gaya mai magana masu zafi"

Saliha ta fad'a cike da bacin rai.

Murmushi Fatima tai kan tace " ai hannun ka be rubewa ka yar, ko bakomi shidin Dan uwane agaremu kuma yayan mune, banjin zafin SA dan nasan giyar shedan ce ta debeshi amma........"

  Gaskiya Fatima baki mana adalci ba, wato ke karesa ma kike sanyi ko well ai sai ki koma gidan nasa "

  Na'ima ta fad'a a harzuqe.

Kyaleta Aunty Na'ima ga dukkan Aamu ta manta abubuwan da suka faru, inaga ta manta ciwon ya mace nata na kanta"

  Saliha ta fad'a.

Kallon su kawai tai tasan komi za tace laifinta zasu gani, tabbas tana son Abdallah amma ita kanta batajin zata iya cigaba da zama dashi koda ace da auren.

   " wai ku akawa abun nan koni haba kun Hana bawan Allah sakat"


   " ke akawa Teemah amma kisani kozanyi yawo tsirara bazaki ci gaba da zama da Abdallah koda da auren bare yanzu Babu, wllh kun rabu kenan " Na'ima ta fad'a cike da tsantsar fushin ta.

  Dariya maganar ta bawa Fatima ma " a'a bama zakiyi ba nima da wasa nake ya Isa haka"

Ita kam Na'ima qwafa tai tare da ficewa a d'akin.




Salma ce ta shigo tare da fad'in " Aunty Fati kije inji ango"

"  Wato  ya rannan kun rai nani ko?" Ta fad'a.




Vote and Share.....

*Mai_'Kosai ce......*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now