BUTULU...PART..24

62 3 2
                                    

💫 *DA BAZAR-MU WRITER'S ASSOCIATION* 💫

     We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all....... *DA BAZAR-MU MUKE TUNQAHO*💃💃💃💃💃

     

              *BUTULU*
   

   
By
   *Maryam Abduul*

*wattpad@maryamad856*

*Daga Marubuciyar:-*
    *BIYAYYA*
   

*Part.....24*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


*************Hisham kam sosai yake cikin damuwa, yanzu ko abinci bai iya samu yace, duk wata hanya da zaibi dan ganin yasami nasara awajen fatima abin ya faskara, hakan ya dad'a tayar masa da hankali sosai.

Kwance yake yayinda idanuwansa ke alumshi, jikinsa yayi mugun zafi wata juwa yakeji duk da cewar ba atsaye yakeba, jiyake tamkar ansa masa wuta ajikinsa, ga kansa da yake mugun sara masa, kuka mai tsananin gaske ya kubcemasa sunanta kawai yake ambata.

Ummi ce ta turo qifar tashi dan acewarta tagaji da ganinsa agida lallai yau sai ya wuce wajen aikinsa, sai dai halin data taddashi sai ya bata tsoro ainun, qarasawa tai inda yake tare da tallafo kansa, sai dai jitai ina sam bazat iya d'aukar kan nasaba sabida tsananin zfin dake jikinsa.

Jin sunan dayake ta ambata yasa ta fahimce inda mataalar tasa ta dosa ahankali tasoma kiran sunansa tare da fad'in "wai catai bata sonakane da kazo kake cutar da kanka haka?"

D'aga mata kaiyai alamar" ehh" duk da cewa baiji amsartaba amma wannan shirun da yaji daga gareta ya san hakan take nufi.

Ummi ta sauke ajiyar zuciya azuciyarta fad'i take" wannan wace irin masifaffiyar soyayyace haka" a fili kuwa catai" to ai saikai haquri ko, kasani ba'a matsawa mutum akan wani abu musamman ma soyayya"

Ya miqe ahankali tare da jingina da jikin fuskar gadin d'akin kan yace" kema Ummi kin goyi da bayan hakan kenan kamar tadda Auwal yace min, wllh zan iya rasa raina akan soyayyarta, idan bansami Fatima ban san halin da zan iya fad'awa ba, dan Allah ki temakamin " daga nan kuma sai ya miqe da sunbatunsa wanda daman kamar jira yake afama mai inda yake mai qaiqayi.

Ummi kam tausayin d'an nata kawai take da irin kalat soyayyarsa tabbas wannan jarrrabawa ce daga Allah, Allah kuma yasa ya iya cinyeta. Nan dai ta lalla'bashi yasha ruwan tea tare da yin wanka, sannan ta bashi maganin zazza'bin dake damunsa kan ta fice daga d'akin.


........To yau tsawon kwana biyu da faruwar haka, sai dai wannan kwanakin yazowa da Hisham da babbar matsala wacce har tasa dashi da asibiti.

Duk da cewa Fatima taji batun rashin lafiyar tasa amma bata kawo cewar yakai hakanba, sai dai aranta tana mai addu'ar samun lafiya tare da kuma Allah ya cire masa sonta acikin zuciyarsa."

Zaune take tana had'a kayanta zuwa sif da mai wanke ta kawo mata d'azu. Na'ima ce ta shigo da saurin wacce daka ganta kasan bata cikin hayyacinta.

Cikin sauri Fatima ta miqe tare da riqota ta zaunar da ita gefen gadon kan tace" Na'ima lafiya me yafaru na ganki haka a rude? "

Na'ima ta kalleta idanta sunyi jajur kan tace" kin kyauta Teema burinki zai cika ayanzu, kinsan kwa me kikai wllh muddin ya mutu to kisani kinyi kisan kai, kuma bazamu yadda ba meyasa kikeso ki salwantar da ran bawan Allah ne iyyye?"

Fatima ta ajjiye rigar dake hannunta tare da juyowa ta fuskanci Na'iman sosai kan tace" Na'ima dan Allah kisabar dani meke faruwa bansan ina zancanki ya dosaba, meyafaru ki fad'an "

             BUTULU.....Where stories live. Discover now