Butulu...part 41&42

38 2 0
                                    

  

            BUTULU........

By Maryam Abdul'aziz
            (Maryam Abdoul)


Wattpad @Maryamad856

Part......41&42




...........Gyara zama tai ta kalleshi kan tace" ni ina ganin basai ka bar garin ba anan ma zaka iya neman wata sana'ar tunda gamu da sana'o'i da yawa"

  Yasan dalilinta Na yin maganar, amma shi kam yanaso yaga yayi NISA da garin ne, kuma ba iya sana'a yakeso yayi ba hatta karatu yakeso yaga ya cimma wani Abu akansa, duk da yanzu yana da d'an iliminsa dai-dai gwargwado.


   "Mama bawai zanje nayi sana'a bane Kawai, a'a zanjene harda neman ilimi Wanda Saida shi ake komi yanzu, kinsan rayuwar ta juya, Dan Allah kar kice a'a". Ya qarasa yana me riqo hannayenta.

  Saida tayi dan jimmm kan tace" to amma yanzu wani garin zaka?"

  " Yawwa Mamata, *KANO* zanje kano Dan naji hankalina yafi karkata ga can, kuma naji ajikina cewa sauyina zaizo da yardar Allah, Kano akwai San mutane inada yaqini bazan sami cutuwa acanba"


  Saida ta sauke nunfashi kan tace" shikkenan Ammar ubangiji yasa albarka, ya tsare duk inda kake, inafata zaka maida hankali kuma sosai kayi abinda yakaika?"


  Farin ciki matuqa yaji aransa da ta yarjemasa cikin d'oki yace" insha Allahu Mama, zan baki mamaki matuqa"

 
  "To Allah yasa"

Ya amsa da " ameen".








*********
............Kamr yadda suka tsara Yau ZAI kaita take taga daddy batare da SANIN Abdallah ba hakance ta faru, Dan koda ya koma Ce masa yai "be sametaba"





  "Hajiya dai nakeji kamar ba wani daddyn ta da yazo"

Murmushi hajiyar tai kan tace" a'a Na'ima, kullum ina cemiki kina kyautata zato Na alkhairi GA mutane, idan har da hasken NE kinsan IRIN farin cikin damu kanmu zamuyi balle ita Fatiman, bare GA aurenta yazo ai kodan auren kyaje"


  Gyad'a kai tayi kan tace" to Hajiya sai na dawo"


Ta qarasa tana me ficewa daga d'akin.


Jin gine yake jikin motarsa fitowarta Kawai yake jira, tana fitowa ya bude mata motar ta fada ta zauna, shima ya koma mazaunin driver yaja sukabar harabar gidan.



Address din hotel din yake bi wnda daddy yabawa Abdallah, hakan ya temaka musu har suka iso hotel din.



  Lambar wayar ya shiga Kira yai sa'a ringin biyu aka d'aga, nan ya gabatar da kansa da abinda ya kawoshi,izini ya musu dasu shigo Dan bai kulle qofar ba.


Shiga sukai nan suka taddashi zaune ya dube-dube a laptop nasa da alama wani aikin yakeyi.



Sosai Na'ima Tai murna da ganin daddy duk da batasanshi a fuska ba ,amma daka ganshi kaga fuskar Abdallah hakan yatabbatar mata da cewa"shi d'in mahaifinsa NE, kuma qani ga mahaifin Fatima, ALHMDULILLAH" shine abinda tace.



  Nan suka shiga gaidashi tare da gabatar mai da abinda ya kawosu.


Yaji dad'i matuqa Jin Fatima Na nan kuma tana garin, rufe laptop d'in yai ya miqe tare da neman izininsu da sumai jagora zuwa gareta.






*********

.........Abdallah kam ya matuqar damuwa da halin da yake ciki, musamman da yaji cewa Sabir be sami Na'ima ba daman yasan hakan zai faru, to amma ya zai yi dole shi yafaro lamarin kuma shi zaisan yadda zai ya qarqare abinsa, ya kuma nad'e da tabarmar kunya, amma ta ina? Ita me mai jagirar ta tsaneshi kuma itama Saida ya bata kamashan wulaqanci, ya zaiyi yanzu?



Miqewa yai tare da zura takalmansa ya ficen daga gidan gaba d'aya Dan jiyake yai masa zafi.


  Company ya wuce, yana shiga yaga dandazon mutane, tunani ya shigayi meyafaru kuma? Koma dai menene tau bazai saurare kowaba.


Sai da ya huta sannan ya neme Fa'iza sakatriyarsa, nan ta shiga gabatar mai da jadawalin da ake dasu tun satin da ya ganata, sai kuma albashi da besa asakarwa ma'aikataba, gashi Yau wata har 10 shine suka kawo kukansu."



Shi harga Allah ya manta da albashinsu ,innalillahi Kawai yace, kallonta yai yace" kowa asakarmai kudin sa aqara ma kowa 10k akai, akuma basu haquri"


" to ranka shidad'e, sai kuma........."



" No banason damuwa kibawa KOWA haquri akan harqalla yanzu bana Jin zan iya aiwatar da komi"


"Yes boss" tace tana me juyawa ,Dan yasan tunda yace haka ba abinda ZAI kuma saurara, "ohhh oga akwai shima chakwakiya" ta fad'a.




Kifa kansa yai akan tebur d'in, gaba daya qwaqwalwarsa ta toshe, ya rasa ta ina ZAI fara damuwa kansa mafita, ga daddy ya matsamai lallai 'yarda yakeson gani.







*Mrs.Abdoul ce*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now