Part....55&56

31 2 0
                                    

  *ZAFAFA WRITERS FORUM*
          Z.W.F

           *******BUTULU........

         NA
MARYAM ABDOUL.
    (MAI_K'OSAI)

     WATTPAD@MARYAMAD856.


PART.....55/56

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

      

     *Inawa kowa barka da sallah, fatan anyi sallah lafiya......ubangiji ya amshi ibadinmu......ya nuna mana RAMADAN KAREEM Na gaba da rai da lafiya........ameen........hppy Eid_mubarak.*





___________Kwanan Ammar biyu agidan da ya sauka, wato gidan Inna Rabi, fita suke yi tare dasu, duk da cewa "har yanzun be sami wata sana'ar yiba za'bamin wankin takalman da yake yi, amma alhamdulillah yana samu sosai.

   Dan wani sa'in kudin sa yake bawa Inna Rabi ayi girki .hakan ba qaramin Jin dad'in zama sukeyi ba, dan suna mutunta junan su.

      %
Yau ma kamar kullum, sun fita wajen sana'ar su.

    Ammar ne tsaye gefen wata mota yana neman dako, hannunsa d'auke da abin wankin takalmin sa.

    Cike da mamaki hannun sa yakai kan wata lalita, mai d'auke da hotan wani mutum mai cikar kamala.

   D'auka yai ya koma wajen 'yan uwan sa, nuna musu yai, cikin mamki suke bin hannun nasa da kallo.

   Halliru ne yace " wannan ai babbr lalita ce, ga dukkan alamu me ita wani babba"

    Tijjani yace " k'warai kuwa, abinda za'ayi kuzo muje gida, Inna ta gani"

   "Haka kwa za'ayi" suka fad'a a tare .

   Nan suka tattara yanasu-yanasu suka juya gida batare da lokacin tashin nasu yayi ba.

   Koda suka isa, bana ta nan duk da bawani nisa tai ba.zama sukai har Saida ta riskesu.

   Nan suka shiga yimata bayani kamar yadda Ammar ya musu.

   Kar'ba tai, nan ta fidda kayan dake jikin lalitar .

   Passport guda shida, sai ATM ACIKI guda hud'u, sai kuma complement Na me lalitar, da yake da lambar sa ajiki ,aikwa suka d'auka.

   A wayar Tijjani aka hau kiran wayar me lambar..........

       %

Koton tayi tsit sosai, kai ka rantse ba Kowa acikin ta.

    Kamar ko yaushe , Shari'a ake saurari akan wani da yaci dukiyar marayu.

   Kowa al'ajabin mutumin yakeyi, ashema qanin mahaifin yaran ne, kuma tun uban nada rai baya musu komi, amma ya rasu yanzu kuma ya cinye musu hakkin su.

    Bayan angama ne aka gabato da shari'ar su Abdallah.

    Nan magatakarda ya mik'e  ya gabatar da abinda ake k'arar akai.
     " akan Ana zargin Daddy da raba auren Abdallah da Fatima"

   Nan alk'ali yai magana game da fad'in " Malam Yusif kaji akan abinda ake qarar ka akai, ka amince?"

Murmushi Daddy yai, Dan tunda aka fito dashi abin yake ta dada BASHI dariya .

    "Ehh Na amince ranka shi dad'e"

  Nan aka shiga gabatar da Shari's yayin da lauyan da Abdallah ya d'auka yake jefama  Daddy tambaya akan " yaje har gidan sa ya d'akko Fatima matar Abdallah, anyi haka ko a'a"

    Daddy ya gyara tsayiwar sa ,kana yace " Nine Mahaifinta kuma mahaifinsa, ni na bashi auren ta, kuma ni nace su taho wannan garin, dan alokacin mahaifiyarsa bata son auren, su kuma suna san juna ,muma munasan auren su."

   Ya d'an tsagaita kan ya  d'ora da fad'in " bayan tahowar su , na bibiyesu sai dai wani zuwa da nai Na riske basanan tunda lokacin Muke neman su, neman duniya mun rasa su, Ana haka mukazo nida mahaifinta anan muka zauna tsawon mako biyu amma ba labarinsu, a k'arshe Na yanke shawarar ya koma ni naci gaba da zama.ina nan garin na k'ulla kasuwanci da wani company ashe ma nasa ne, sai Allah ya had'a ni dashi, daga nan nasa shi a gaba akan lallai ya fiddo min da d'iyata, lokacin da abokinsa yamin jagora har na sadu da ita alokacin naji mummunan labari wai ya sake ta, har ta kawo mu yanzun da ake magana, to kaji ranka shi dad'e "

    Daddy ya sauke nunfashi ,tare da kallon inda Abdallahn yake.

    Nan alk'ali yayi d'an rubuce-rubucrnsa kan yace" ko wanda ya shiga da qara yana da abin cewa? "

    Cikin hanzari Abdallah yace " yalla'bai Wllh ban Saki matata ba ,inason ta na yadda duk abinda yace hakane, kuma naji tsoron kar mahaifiyata ta rabamu, dan kullum mukai waya sai tace na rabu da Fatima Kota tsinemin, wannan dalilin yasa na hana kanmu saduwa da iyalanmu, har lokacin da tasa aka fara mata bincike akaina, Wanda ni kaina ban San taya tai hakan ba, dan Allah kar ku rabamu"

    Ya k'arashe kamar zaiyi kuka.

Alk'ali yai magana cikin salon shari'arsa yace " ko zamu iya ganin malama Fatima?"

    Nan ta mik'e  tare da fitowa, nan tayi rantsuwar zata fadi gaskiya abinda aka tamvayeta akan sa.

      Alk'ali yace " sin zaki iya bayyana mana gaskiya al'amarin?"

   Kamar yadda alk'ali ya buqata, haka fatima ta fara bayaninta tiryan-tiryan , duk abinda ya faru tsakanin si har rayuwar ta da su Dr. sai da ta fad'a.

    Take jama'ar koton aka fara kace-kace, Kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

       Nan alqali ya neme Jin ta bakinta game da zaman ta dashi, duk da cewa a yanzun auren ma babu, amma in tanaso za'a iya maida auren"

    Murmushin gefen baki Tai, tabbas taso cigaba da rayuwa da ya Abdallahn ta amma bazata iya rabuwa da Hisham din ta ba.

     "A'a ranka shi dad'e ,inada Wanda nakeso a yanzu an kusa auren"

    alk'ali ya kada baki yace " to kaji Malam Abdallah, dan haka babu kai babu Fatima, zaman ku ya qare ,maganar 'ya kuma in kaso ganin ta zaka iya nemanta wajen ahlin ka"

   Nan ya buga gudumar sa, tare da yin wasu rubuce-rubuce, ya miqe, nan Kowa ya miqe har alk'ali ya fita.

     Daddy kam murmushin Nasara yai, lallai Abdallah ya cika butulu, dan sai a Yau da Fatima ke fad'in wani abun suka sani, ko takanshi basu biba SUKA bar koton.

      Abdallah kam jiyake zuciyarsa Na masa zafi da suka, wani maqwallaton bakin ciki ne ya tsaya masa a makoshi, ya zaiyi da wannan iftila'in da ya aiki masa ,idan ma yace zai daukaka qara yasan tabbas shine a qasa, ya zaiye?

    Motarsa ya bude ya fad'a da gudu ya figeta, kotakan lauyansa da ya dauka bebi ba.

   Yana isa gidan ya haye sama dan samun hutun da zai sa kansa yayi normal Na zafin da ya d'auka.

    Murya da motsin  da ya jiyuwone daga 'bangaren  Latifa yasashi tsayawa, duk da cewa yana cikin rad'ad'in abinda ke faruwa.

    Nan ya tsinkayo muryata na fad'in " kai dai bari aini  yanzu saura kiris in yashe shegennan in yaso kaga auren mune Kawai ya rage, bai sanni bane har yanzu sunana kawai yakeji, a zatonsa na aureshi dan son da nake mai, sabida kasan shi jahiline, "

   Dariya aka kwashe da ita tare da fad'in " well done babyna, shiyasa kullum nake qara jinki a raina, to amma taya zamu sami abinda mukeso?

  Dariya itama tai, kan tace "  Na kwashe duk wasu ATM nasa, da duk wasu takardunsa Na madarorin sa, harta wannan gidan , jiran sa hannunsa Kawai nakeyi ,kuma yau din nan na maka alqawari zai sa mana, dan wannan lemon dakake gani na ajjiyeshi dan biyan buqatarmu, wannan shi zai sanya ya sa mana hannu."

    Jiyai wata kuwa na debansa, kafin su sakya wata maganar zuciyarsa ta debeshi akan yanuna musu shidin ba jahili bane kamar yadda ta fad'a........

      *Tofa me zai faru, kar fa......uhmmm....ba ruwana .*


   *Real Mai_k'osai........*

   

             BUTULU.....Where stories live. Discover now