part....15

129 5 0
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
〰〰〰

Story...writing by
  *Maryam Abduul*
  
Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

*Marubuciyar:
   *BIYAYYA*

   

*page....15*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

Hdithi yazo mana daga bakin Annabi Muhammad (SAW) inda yake gayama cewa" imanin d'ayan ku bazai ta'ba cikaba har sai yasowa d'an uwansa abinda yasowa kansa"

Ma'ana imaninka bazai ta'ba cikaba sai kasowa d'an uwanka abinda kasowa kanka, misali ka somasa farin ciki kamar yadda zakasowa kanka samun farin ciki, kasoma alkhairi kamar yadda zaka somawa kanka, zaka iya haqura da abinda ranka yakeso shi ka bashi dan samar masa da farin cikinsa.

Dan Allah muso junanmu musowa kawunan mu abinda zai anfana damu ranar gobe alqiyama.

--------- Firgigit ya farka daga duniyar tunanin daya afka, murmushi yai yace" kai Allah yayi halittafa anan, wannan kuma a ina aka samu mana ita, dan nasan ba sister d'in kabace"

Dr.Auwal ne yai tsaki yace" kaifa dad'ina dakai kenan wallahi bada mutane, to wannan bata bayarwa bace"

Har ya bud'e baki zai magana, dr.Auwal ya katseshi da fad'in " kaga muje ciki, yanzu ba lokacin wannan maganar bace"

Koda suka shiga a falo suka sauka, nan Dr. auwal ya kira Ummi suka gaisa dayake tasanshi sosai kuma yayi zaman gidanta dan da suna seondary nan ne wajen zamansa har kwana yanayi, hakan yasa take matuqar sansa, ta maidashi tamkar d'anta, duk abinda zataiwa Auwal to zatamai.

Lokaci d'aya yayi musu hijira zuwa egypt wanda da farko tare suka tafi da Auwal amma shi sai yadawo shikuma yazauna acan.

Suna cikin gaisawa su Salma da Fatima suka shigo nan suka qara gaidashi, cikie da fara'a ya amsa yana sakin wani lallausan murmushi, wanda dr.Auwal ne kad'ai ya lura da hakan.ganin hakan yasaahi jansa zuwa d'akinsa.

Suna shiga ya kalli Dr. Auwla yace" gaskiya wannan ko a ina ka samomana ita tayi fa "

Dr.Auwal yaja tsaki kan yace" dalla malam ka nutsu ita d'in matar wanice ma'ana ina nufin tana da aure kagane"

Hannunsa yasa ya dafe qirjinsa kan yace" dagaske kake ko kowa kana zolayatane?"

Dr.Auwal yace" da gaske nake dan haka ka cire ranka gareka tun wuri kasan inda dare yama"

Kallon Dr. auwal yai yace" zuciyata tayi zurfi bazata iya jurin rashin abinda takesoba, na roqeka kasanar dani gaskiyar abinda kasani akanta dan Allah"

Jin yadda duk yabi yayi wani iri yasashi kallonsa tare da gyara zama yace" ahikkenan, zan gayama komi amma kamin alqawari bazaka ta kuramataba akan wani abu naka"

Cikin sauri ya riqo hannunsa yace" namaka indai nine kada kadamu dani"

Girgiza kai yai yace" well, gaba d'aya labarin da Fatima tabasu da had'uwarsu da ita yabashi"

Cike da tausayawa yashiga jujjuya kai," lallai ba shakka ta had'u da azzalumin na miji kuma cikakken *butulu*, sai dai ya akai yabari zuciyarsa tai rauni akan san dayake mata, meyasa zai bari shaid'an ya ribaci zuciyarsa haka?"

Yaqara rausayar dakai tare da kallon Dr. Auwla yace" dan Allah kabani dama na nemi soyayyarta duk da nasan ba lallai ta aminta daniba, amma kasani tashin farko naji kawai zuciyata ta kamu da sonta, dan Allah kada kacemin a'a"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now