Part.......73

79 5 2
                                    

   *ZAFAFA WRITERS FORUM*
           Z.W.F...........


          ______BUTULU______

NA
  MARYAM ABDUL-AZIZ.
       (MAI_K'OSAI).

Wattpad@maryamad856.

Page......73 last page.


Bisimillahir Rahmanir Raheem.

____________Tunda Na'ima taji batun komawar Fatima gidan Abdallah a bakin hajiyarsu take ta faman hawa da sauka.

  Kawai ganinta tai a gidan Ammi cikin had'e rai tace " wai da gaskene abinda naji abakin Hajiya?"

  Murmushi tai kana tace " ehh mana, a tunanina yanzucba wani fushi da mutumin da baida lafiya"

  Sakya had'a rai tai kan tace " ehh mana tunda ga father baida lafiya, wai Fatima meyasa baki da zuciyane, yanzu mutumin da ya wulaqantaki yaci mutuncinki , ya gaza tallafa miki sanda kike neman temako shine ke yanzu har zaki iya komawa gareshi.?"

  Murmushi tai a karo na biyu sannan tace " wallahi Na'ima nafiki Jin zafi fiye da yadda kike ji, banayi hakan bane nan muradin raina, saidai banaso na rasa d'an uwa na kamar yadda na rasa Mijina, sannan uwa uba banaso na zama mace wacca batta da yafiya akan lamuranta, karki manta Allah ya son masu yafiya da kuma yawan tuba, ni zanyi ceto ne kawai ,dan Allah ki fahimceniba"

  Saida ta sauke ajjiyar zuciya kan tace " shikkenan yawuce, amma dai duk da haka ki rage rawar kan nan, gidan mara lafiya zaki ba lafiyayyeba"

  Dariya sukai gaba d'ayansu tare da rungume junansu.

  Ammi da ke tsaye tana Jin diramarsu sai itama duk suka bata dariya.




Lokacin da Saliha taji maganar komawar Auntyn nata gidan yayan nata baqaramin murna tayi, dan yanzu duk wani fushi da take dashi ya kau, itama burinta kawai ace hakan ta kasance.

  Nan fa suka fara shiri Na musamman, dan sunce biki zasuyi na musamman .

       %

Bari mu d'anyi wai-waye........

   Tun tahowar su granny Aunty Zubaida ke fama da kanta, kasancewar ciwon sugar da yakamata, ga damuwa  na irin maganganun da Ihsan ke janyo mata, duk da cewa ba wani abin Allah wadai take aikatawa ba , amma kuma Allah ya hore mata idan cin naira.

 
   Duk inda tasan mahaifiyar tata na ajjiye kud'i to ba shakka zata sa hannu ta d'aukesu, kuma ko ajikinta.

   Uwa uba tana ji tana gani zatai ficewarta ba tare da ta temaka mata da uffan ba, duk wani sintiri na asibiti ita kad'ai yakeyin kayanta, wanda a yanzu yaci ace tana temakamata tunda tana buqatar hakan.

    Ita abinda yafi damun ta ma irin rashin mashinshi ne ko d'aya, har yau ba  wanda yace " yana sallama da Ihsan" ko yake bibiyarta, duk da ita ma Ihsan d'in abin na damunta.

   Wannan ya haddasa mata, ciwon hawan jini, kuma yazo ya had'u da ciwon sugar.

  Duk wannan abun Abba ne kad'ai ya San da maganar kuma shi yake d'awainiya  da ita, wanda har Saida aka shafe tsawon wata shida.

  Daga bayanema yake bayyanawa Daddy abinda ke faruwa, hakan nema yasa granny komawa,dan ta zauna tare da ita.

     
           %

Tabawa kam abu goma da ashirin sun had'u sun mata zafi, 'bangare d'aya d'iyarta  da take fama da laulayin cikin da ta kwaso a yawan ta na kwararo, d'aya gefen kuma Taga dake kulle wanda ba'a da tabbacin sakin sama, wani gefen kuma bakin jama'a da ya taru yai mata katutuwa duk inda tasa qafa sai kaji ana gulmarta.

             BUTULU.....Where stories live. Discover now