Part.....49&50

34 1 0
                                    

          ******BUTULU



             NA
Maryam Abdoul
    *(Mai_'Kosai)*



   Wattpad@maryamad856.




Part 49/50


Typing........



Bisimillahir Rahmanir Raheem.






__________Haka Ammar ya miqe ya fara qoqarin neman dakon shima, cikin ikon Allah ya samu Dan har ya daukarsa mutane biyu kayan su.

  Yana nan zaune ba Wanda ya kuma nema Dan yinwa ce taciyo shi alhmdulillah tunda ma ya sakya samun wasu kudin dan 2k ya samu.

  Nan ya miqe ya shiga nemarwa kansa abinda zai sanya acikin sa, wasu maza ya gani tsaye gefensa nan yai musu sallama ya shiga tambayar su inda zai sami abinci ya siya.

  Cike da murmushi suka nuna masa wata mata da ta kafa rumfarta ta Saida abinci, nan yaje ya samu ya siye shinkafa da miya ya zauna gefenta ya soma ci tare da bisimillah abakin sa.

  Tunda ya musu magana suke kallon shi  "ga dukkan alamu baqone" inji d'aya daga cikin su.

" Nima dai haka nake tunani" dayan ya fad'a.



        %

******Abdallah kuwa koda ya rasa inda zai nufa haka ya haqura ya juyo gida duk da yanzun bawai San zaman gidan yake ba.

  Sai dai abinda ya bashi mamaki ganin motocin da suke fake a harabar gidan nashi ba, "su waye" ya ambata a cikin zuciyar sa.

   Qarasawa yai wajen me gadun Sanda ya kammala parking nasa, bayan sun gaisa yashiga tambayar SA su waye a gidan??

   " yallabai baqine ga dukkan alamu Na gidane dan tare suke da yallabai Sabir "

  Jin hakan yasan yashi fad'ada murmushin sa ba tare da ya sakya masa magana ba ya wuce ciki kai tsaye.


  Dukkan su zaune suke , granny ,Daddy ,Fatima, Hajiyar Na'ima, sai Ammi, Na'ima da Sabir.

  Kallon su yake cike da mamakin ganinsu, take yaji kuzarinsa ya d'auke "la haula" ya furta qasa-qasa.

    " 'Karaso mana yallabai"

Daddy ya fad'a cike da fara'a.

Ba yadda ya iya haka ya hau d'aga qafafuwan sa ya shiga takawa har ya qarasa inda suke, waje ya samu ya durkusa, sai dai idon sa na kan Fatima yadda yaga tayi wani fresh da ita sai yakeji ina ma ace suna tare da juna.

  " Bawai wani abune ya kawo muba, munzo ne dan tafiya da 'yar mu duk da cewa bata gidan ka yanzu, sannan munzo miqo godiya agareka yadda ka riqemana 'ya da amana batare da tasha wata halar rayuwa ba." Daddy ya fad'a yana kafeshi da Ido.

  Cikin qarfin hali yace " amma Daddy har yanzu Fatima matatace ai ni bance ........."

   " Babu aure tsakanin ku kai da ita Dan ka rigada ka sawwake mata tunda ka rigada ka gama cin moriyar ganga ai dole ka jefar da kwallon, koda da aure ni bazan sakya yarda ka cigaba da zama da Fatima ba Wllh kaji na rantse"

   "Dan Allah Daddy ku fahimceniba Wllh sharrin shedan ne ,ban mata haka ba dan cin zarafi ko wani Abu ba inason matata dan Allah karku rabani da ita". Ya qarasa cike da karyayyiyar murya kamar zai kuka.

   Caraf Saliha ta cafe da fad'in " Wllh yaya Sanda naji labarin Saida na qarya ta amma sanda nazo na ga Aunty na kuma yaya ta yar uwa ta sai na gasgata batun, ban ta'ba tunanin d'an uwa zai iya cutar da d'an uwa ba, haba yaya ina iqirarin San da kake mata, "Na Mike alqawari zan riqe Fatima da amana, ina son Fatima fiye da kaina, zan mata bauta kamar bawanta, zan rayu da ita irin rayuwar d'a da mahaifa, zan bata farin ciki fiye da na kaina" koba haka kake cewa ba, amma duk ina alqawarin meyasa yaya ka aikata haka meyasa"

  Ta fashe da kuka.

Granny ce tai qarfin halin magana, dan tunda suka fara maganganun su batace komi ba, tabbas tana hango tsantsar zallar qaunar da yake mata, amma ya rigada ya bawa shedan damar da har wannan abubuwan suka faru.

  " Abdallah muna kyautata zato daga gareka, nasan bazaka taba wulaqanta yar uwar ka ba, amma lokacin da naji maganar na girgiza ainun, meyasa zaka barmana ya ta wulaqan ta, yanzu da basu Hajiya kasan halin da zata fad'a, ina zata ? wazata hadu dashi san da ka koreta? duk baka sani ba amma ka zubawa idonka toka sabida San kai da zuciya, abinda daman mahaifiyar ka keso ku rabu to Alhmdulillah yanzu ka cika mata burin ta, Fatima kuma aure nan da wata guda me zuwa insha Allahu"

  Jiyai kansa ya wane sara, "aure kuma ,wllh ina son Fatima karku rabamu da ita"

  Cikin sauri ya karkata akalar sa zuwa gareta, cikin yanayin tausayi yace " Fatima kar ko bari a rabamu Dan girman Allah, ki sakya bani dama a karo na biyu na sakya nuna miki irin tsantsar qaunar da nake miki Dan Allah"

Kwallar da tataru a idon tane ya zubo mata, bakomi ta tuna ba sai sanda take roqansa akan ya dube halin da take ciki ya barta ta zauna, amma for yaqi, ya juye tamkar be ta'ba sanin ta ba.

  Cikin dakiya ta kalleshi tace"..........




*Mai_'Kosai ce.....*


             BUTULU.....Where stories live. Discover now