Butulu....10-11

131 7 0
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
   〰〰〰
         *(Return)*

Story...writing by

*Maryam Abdul*
Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

*Marubuciyar:
*BIYAYYA*
*WANI YANAYI*
   
*page....10-11*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

-------Abbana ya had'u da mahaifiyata(wato Maimuna amma muna cemata Mami) acikin kasuwa wajen siyan nono da fura, Dan ita d'inma fulanice.

Nan suka qulla soyayya mai qarfi hartakaisu ga are.lokacin kuma daddy d'ansa d'aya wato ya Abdallah Dan yana da shekara biyu ma alokacin.

Shekararsu hud'u da auren amma Miami na ko 'bayan wata bata-ta'ba yiba, wannan dalilinne yasata kullum cikin damuwa, ga gorin da aunty zubaida keyimata matar daddy.

Tun abun bai damunta har yafara damunta, Dan yanzu har Granny kanyimata shagub'e idan suna tare wannan dalilanne yasa mamina kullum cikin damuwa dabtunani danma Iran Abbana na gari yakan dunga qoqarin kwantar mata da hankali.

........

Bayan wata d'aya tsakani Granny ta tasa Abba agaba akan" suje asibiti adubasu Dan tanason taga jikanta daga tsatsonsa"

Wannan magana da tafad'a kam hakan kwa akai Mami da Abba suka ziyarci likita na musamman nanfa yayi duk wani binciki da yakamata.amma cikin ikon Allah ba'asami wata matsala daga garesuba kawai dai haihuwarce Allah bai kawoba.

Koda suka koma gida nan Abbana yaiwa Granny bayani akan abinda likita yace.

Nanfa tahau darun saidai ya qara aure ko Allah zaisa adace.

Ba yadda Abbana ya iya haka ya haqura ya amshe batun Granny, dan da dafari yaqi amsa saida Mami tamasa magana tare da magiya danuna mai Cewar" Granny zataga kamar itace tahanashi" badan yasoba ya amshe batun nata dan shi yace" atsarinsa baida niyyar auren mace fiye da d'aya, kuma yasan kowa ya aura bazaisota sosai ba sabida Mamice agabansa"

Cikin abinda baifi wata biyuba ta naimamai auren wata nan maqotansu.nan akagama komi akai biki aka kai amarya gidan mijinta.

Shekara biyu dayin auren nanma shiru bawani cigaba da akasamu nanfa hankalin Granny yamugun tashi saida Abbana da daddy suka dunga bata baki tare danunamata illar yin hakan dan kamar tana yiwa Allah butulcine.


......Bayan shekara d'aya amaryar Abbana tasa daru akan" itafa bazata zauna da juyaba.rashin mutunci kala-kala tadingayi, daga qarshedai saida tasa Abba yamata saki d'aya.rabuwar baran-baran sukai.

Rabuwar amaryar Abbana da Abbana wata biyu Mamina tadinga fama da wani iron zazzab'i mai zafi ganin halin datake cikin yasa Daddy kaita asibiti Dan alokacin Abbana baya gari.

Koda sukaje gwaje-gwaje akamata Wanda ananne kuma aka gani tana da shigar juna biyu har natsawon wata d'aya da Rabi(sati biyu).murna farin cikin Wanda ba'a musaltawa suka dingayi, tun a'asibitin daddy yadinga kyautar kud'i suna dawowa gida yakira Abbana yashaidamishi, wayyo zokuga murna wajen Abbana aranar ya nemi viza Dan dawowa gida.

Washe gari kam shigowar asuba yayi, nanfa Abbana yashiga bawa Miami kulawa ta musamman.

Ya Abdallah kam yana da shekara 9 alokacin tunda yatambayi daddy" me akeyi yaga kowa yana murna?"

Nanfa daddy yake shaidamishi" ai ankusa yimasa qanwa" shikkenan yaketa farin cikin, nanfa yadawo 'bangaren Mami yatare yace" shi yadawo wajen qanwarsa" badan aunty zubaida tasoba tabarshi dan data nuna Sam hakan bazai yiwuba nanfa tasha fad'an daddy" akanme zata hanashi" wannan dalilinne yasata rabuwa dashi badan  ranta yasoba. 

Alokacin kuma Ashe aunty zubaida na maqale da cikinta hat natsawon wata uku batare da kowa yasaniba sai ita d'aya. ganin yadda kowa hankalinsa yakoma kan Miami sabida cikin ta yasanya aunty zubaida jin haushe matuqa hakane yasata fallasa cikin fake jikinta tahanyar shaidawa daddy d'in.

Nanma kowa yai murna dahaka, koda tasami ya Abdallah take gayamai" itama zata masa qanwa" sai cewa yayi" shidai yafison ta Mamina" wannan kalamai NASA da yafad'a sun qonamata rai had said a tazaneshi Kuma ta gargad'she akan karya gayawa daddy ta dakeshi.

Cikin Mamina yazo da lauye kala-kala dan yana matuqar wahalar da it a, hartakai ga likita yahanata yin wasu ayyukan, hakane yasa Abba yace" zai d'akko mata 'year aiki" amma Mami taqi data qarshe dai sai Granny ce kemata wasu ayyukan, cikin kwa harda ya Abdallah.wannan Abu ya matuqar qona ran aunty zubaida.

Cikin aunty zubaida yasa ga wata tara, cikin dare tatashi da naquda mai wahalarwa Wanda hat said a akamata c.s India aka Ciro mata kyakkyawar 'yarta mai kama da ita sak, alokacin kuma cikin Mami na wata bakwai da sati biyu.

Ranar suna yarinya tace suna Ihsan, alokacin Abbana yashiryawa ya Abdallah tafiya Macca yin karatu acan daga kan aji biyar na primary zai zaunane awajen wani abokinsa, zasuyi karatun tare da 'ya'yansa biyu.

Dafari aunty zubaida tanuna battaso sai kuma daga baya taitunanin ai ita zataci mamorarsa kuma bakud'in tabane zaiyi aiki saita saki ranta.shikam ya Abdallah dakuka yabar gidan Wanda saida Abba yamai alqawarin zaizo yad'akkoshi idan an haifamai qanwar.

Bayan tafiyar ya Abdallah da wata uku alokacin Mamina cikinta yashiga wata goma, ga cikin ya qaramata nauyi sosai.

Likita sukaje suka gani nan aka mata gwaje-gwajen amma ba wata matsala haka suka dawo gida.

Ya Abdallah kwa duk sanda Abba yakirashi ko daddy sai yatambayesu "anhaifamai qanwar?"

Saidai suce masa" ankusa da saura"

Wasa-wasa har saida Mamina tashiga wata  na goma sha d'aya sannan tafara wani irin ciwo  Wanda a take naquda tazomata bagatatan.

Nanfa aka wuce da ita asibiti Dan Mami kam tafita hayyacinta sosai bama tagane waye akusa da ita, ganin hakane yasa likitan daya karb'eta yanke hukuncin amata C.S, nan Abba yasa hannu akan takardar.

Cikin hakane kuma yakira danginta yashaida musu halin da'ake cikin, nan wata qanwar mamanta da yayarta sukazo kasanceqar daman su biyune awajen iyayensu, babanta kam yarasu ahatsarin mota da sukai daga Adamawa zuwa garin Kano, Wanda ko gawarsa ba'agani ba, sunce kuka sun godewa Allah.

Yawan Comment yawan typing....

Editing is not allow....📵

Vote,
Comment,
Like and share....

*Mrs.Abduul ce*✍✍

             BUTULU.....Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora