page 3

3.3K 267 0
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                    03
"Zulfah wai kinsan sosai moh yakeda kafiya, wannan da kika gani wlhy da kafiri ne se yayi wuyar musukunta, wasu abubuwan danake sakawa yana siyamun  wlhy badan nai amfani dasu bane ba, amma mutumin baya tab'a nunamun gajiyawar sa, wani zubin daya fara zuba wa'azin sa zam dirza rashin m seyace toshi kenan, ke bama wannan ba zan ambaci abun dubu d'ari uku seya ce banda shifa? Akwai wani abu ya masifar k'ular dani" murmushi zulfa tai

"Lallai ma Meenal, tukunna baki gama ganewa halin man d'in naki ba, shifa koda komai nashi ze k'are akanki toze miki lalura ne, jarabace Allah yamai akanki, amma yanzu ke me kika gani, nifa bawai muni yakeda shiba indai kyakyawane kyakkywane ajin farko ma kuwa, matsalar sa d'aya k'auyanci kofa k'ananun kaya baya sakawa kullum da manyan kaya sekace babban malamin izala, ranar wata juma'a segashi hadda rawani da wandon sa a d'angale sekace limamin k'auye, iyaka dai shikam yadin nan na jikinsa fari ne k'al se k'amshin turarensa na oud al arab ke tashi duk inda yabi, sannan se tsafta har gulman motanshi nakejin student nayi ko lokacin damina bata datti wai sekace me wani isimin" Dariya suka sanya a tare tace

"Iyakaci dai suce yanada tsafta kuma kyakyawa ne, to se meye? Nifa wlhy na tsani k'auyancinsa"

"Nima haka, semun tara friends na auren 'yar sharad'a builder's azo aga wani bak'auyen miji" murmushi tai ranta yana sosuwa amma batai magana ba, kasancewar zancensa ya isheta haka...

**************
     Abubuwa sunwa Muhammad yawa ainun, yarasa sukuninsa kwana biyu  ma beko lek'a b'angaren na Meenal ba, kuma ko wata waya basui ba sosai  sabida ayyuka sun masa yawa ga skul gakuma harkan kayan wayoyinsa da suka iso yana clearing komai da kanshi, yana tsakiyan aikinsa wayansa ya k'ara, yasha mamakin ganin meenal ce aranshi yace "Meena!" Yasani Meena sam bata kiransa a waya seda wata babbar buk'ata, d'auka yai ya amsa kiran

"My Meena" d'an gajeran tsoki taja

"Yaa moh bafa meena ake cewa ba kace Meenal mana yanda kowa ke fad'a" murmushin sa me sanyi yae

"Ni kuma ina zan iya fad'an wani Meenal, ni bazan fad'a ba danban iya ba" kwab'e fuska tai

"To kaika sani" ta fad'a a fusace, gyaran zaman sa yai yana murmushi

"Meena nine kuma nina sani yau? Wayene ya fusatamun ke kike k'ok'arin saukewa akaina" harara ta chillawa wayayr tamkar yana ganinta

"Yau kusan kwanan 4 bakazo munba, na jejje office baka school nakira wayoyinka a kashe se jiya na samu baka picking ba, baka kuma kira misd col nawa ba kozan iya sanin mesa?" Nisawa yai dama yasani akwai rigima kwance a qasa inhar muddin suka had'u

"Auu dama yousufa dana aiko bazoba, wayan ne fa ya lalace mun kuma kinga wlhy nace ya sanar dake, tafiyan dole ya kamani"

"Haba mana yaa moh, yanzu fisabilillah duk fad'in abuja a gunka suke siyan waya amma kace dami wayanka ya samu problem na tsawon kwana hudu, wane irin tsiyane wannan" kalmar ta tsiya ta daki k'irjinsa seya wayance kurin

"Akwai wayar danakeso ta kampanin samsung kurun sena tsaya jiran isowar ta, kuma se jiyan ta iso, sanda kika kira bata guna ana sakamun abubuwa" Shiru tai kantace

"Nima akawomun idan tanada kyau" be kula zancen ba yace

"Yau bayan isha inshaa Allahu zanzo na ganki my meena" batace masa komai ba ta yanke call d'in gaba d'aya tana mejin zafin sa, yau idan yazo zasuyita ta k'are....tana nan junior ya shigo

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now