page 37

3.1K 312 19
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad 68billygaladanchi

      37

Tun shigowarsu napep d'in hankalin Takawa be kwanta da me napep d'inba, ya tsorata sosai da yanayin sa yakuma san a yanayin fitowarsu ta babbar k'ofar fadar masu jiran shigowar su komai zasu iya aikatawa tunda daga b'angaren sane kurun yakeda k'ofar sirri amma ata cikin masarautar dole yabi main gate, wannan ne ya sanya ya rufewa meenal hanci da d'ankwalin kanta dama kuma ta sanya nik'af, sannan ya mayarda ita abayanshi, ya kakkare gaban, wurgo k'yallen dayae yayi daidai dama Takawa ya shirya tarar kowane irin abu yazo masa shisa da bindigogi har biyu ya fito,hannunsa ya sanya ya rik'e hanky d'in ya shak'awa fuskar me napep d'in take ya sume, keke napep tasomayin hanyar daba titi ba, da wannan ya diro ya janyo meenal suka sauka sedai seda ta bige k'afar ta🤥, a bayan sa sakata, yanaushi hanyar dama dare bawai yayi wani nisa bane akwai yalwar mutane jefi jefi, Ganin mota agabnsu ma ya k'ara fad'ar masa da gaba sosai, ja yae da baya ganin haka ne ya sanya Tahir fitowa yana mamakin ganin Takawa dukda yanayin shigarsa be fasa ganeshiba yarone awurin magatakar da na masarautar kuma tare suka tashi da Takawa sedai shi ba Niger ma yake zama ba yana paris Takawa bemasan yazo ba
" Mu'az ya haka ne, yada yawo da k'afa kasan yanayin garin?" gumin goshinsa ya sharce da hannu d'aya

"Bamuda lokaci Tahir mushiga mota kawai dan Allah"  haka shida ita duka baya ya sakasu, Tahir yace

"Ina muka nufa ne Takawa?" Cikin takaici yace

"Wuri me sirri Tahir koma inane inda ka yadda dashi" murmushi tahir yae, "Bari mushiga gidan bak'ina ta gate d'in gaba, semu fita k'ofar baya da k'afa, semu je sabon gidana akwai hadimai tunda Fareedah tana nan ai" Murmushin Takaici Takawa yae, bashida zab'in dayafi yabi shawarar Meenal tunta farko, dama seda tace abar masarautar kafin a karb'i sarautar yak'iji, yanda tahir ya fad'a hakan akayi,dankuwa biye ake dasu shi mamaki yake yanda kwata kwata gidan sarauta babu kwanciyar hankali to suma dai da sarautar tasu bawai ta wani taka kara ta karya bane amma hakan be hana k'ananun maganganu da bak'ar hasada tashi ba.

***********
   B'angare d'aya aka basu dukda gake k'ofar shiga parlor d'ayace sedai akwai sassa daban daban agidan, Meenal gaba d'aya a tsorace take a wannan ranar abinda yaso faruwa dasu ta sani adu'ar datace suyine kafin subar gidan Allah ya karesu.

"Sannu Babyna, k'afan sosai yake miki zogi? Kiyi hakuri nasan ban kyauta miki ba, kina zaman ki lafiya na wurgoki acikin shirgin dabe shafeki ba k'addarar rayuwata ce tazomun da haka nima....hannunta ta sanya ta rufe bakinsa

"Ka dena fad'ar irin wannan maganar, nima kaina k'addarar kace, ka baiwa su Hidar tsaro sosai yanzu shine agabanka, kaga yau alhamis dukkanin shirin dazamuyi muyishi kafin saturday inyaso ranar semu tinkari fad'a da k'arfin mu, ka kwantr da hankalinka inshaa Allahu abubuwan nan yanda sukazo haka zasu tafi" Nisawa yae

"Shikenan Meenaly nagode sosai daso da k'auna ta taimako" murmishi yae

"Nima nagode da kulawa yanzu ni kazace agabana" Murmushi yae

"Tahir ze kawo miki karki damu" Haka suka d'anyi hira ya shafa mata man zafin da tahir ya aiko dashi sannan suka duk'ufa yin shirin su.

**************
  *Inter-mission*

*Asabar*

     Ranar asabar tunda safiya suke shirin tinkarar Fada duk wata masarautar daya dace sarki ya gayyata ya gayyaceta a asirce, Su waziri sunsha mamakin Tawagar daketa shiga fada ga kuma filin wasa yasha gyara na musamman, tsegunguma se tashi sukeyi zuwa k'arfe 10:am masarauta tacika fam da jama'a, a d'aya b'angaren ma Meenal tasha shirinta tsaf irin na sarauniya tayi kyau harta gaji, Mu'az yasha nad'i irin na sarakuna yayi kyau ainun, sojoji me sukai masu rakiya zuwa filin da aka tanada dama cen domin su, Tu da labari ya riski sarauniya hassy se hankalinta ya tashi haka ta shirya ta nufi filin haka kowama su sarauniya daurama, manyan fada duk sun rikice sabida rashin sanin manufar sarki akan aikata hakan, koda taro ya soma se bayanin sarki ya tafi akan zeyi murabus ya baiwa d'anshi, yarima fu'ad se wani fad'i yakeyi ya zata shi ake nufi se katsam yaji sunan Mu'az take awurin sunaso basaso aka Bashi matsayin sarkin garin me mulkin masarautar ta hankaka!!!! Zukata sun raunana sarauniya hassy a wurin ta sume tsabar shiga tashin hankali haka sarki be damuba aka shiga shagulgulan dasuka dace waziri kamar ze mutu gashi carbinsa dayake juya sarki da ita ta b'ata itace makaminsa shekara da shekaru dasuka gabata. Fada ta rikice kowa ya rud'e yarima Fu'ad in hankalinsa yayi dubu toya tashi be tab'a zaton haka ba shida matar sa anshiga tashin hankali basu gushe agunba seda aka nad'a Meenaly matsayin Sarauniyar sarki Takawa Mu'az na II, HAUKACEWA  shine zamu kira abinda ya biyo bayan rabi da kwatan 'yan masarautar basuda wata hanyar k'ara cutarwa ga takawa sabida yanzu komai nasa keb'antacce ne, hankalinsu be k'ara tashiba seda suka dawo masarautar k'ofar Gabas ilahirin kayan sarauniya dana sarki ana kwasarsu zuwa k'ofar yamma, Ciki kuwa hadda gimbiyar Rusau da d'anta ya gayawa baze yi biyayya agareta ba yaci zalin wasu ba.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now