page 12

2.4K 252 15
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                  12

Tun jiya gaban Ameena ke yawan fad'uwa aduk sanda ta tuna hidar gashi kuma kwata kwata batada lambar wayan takawa, yau tana school kuma se 3 zata dawo, ana lecture amma sam hankalinta baya wurin lecture da akeyi, a gaggauce taga sha biyun rana tayi tabar school d'in, kai tsaye asibitin ta wuce inda ta taradda takawa a d'akin, seda ta wurga masa kallo na 'yan dak'ik'u kanta d'an russuna kad'an tace dashi

"Sannu Abu Haidar ina wuni" seda ya d'an ja fasali kanyace

"Lapia" bata kula da yanayin amsawar saba ta wuce gun Meenal, myrmushi tayi ta dafa goshin yarinyar ancire mata bandage dake kanta, ta furta

"Small meenal sannu, ashe kuna jiki yayi sauk'i" murmushi tayi sannan ta yunk'ura zata zauna, da kanta ta tayar da ita,yarinyar ta turo baki

"Mom kinga dad ko? Shine yace da Dr. Ya askemun suman kaina, kinga yanzu dukba rabin sumar"  rungumota tae

" karki damu, zamuje paris na siya miki man gashi me kyau, ze cicciko inshaa Allah"  murmushi tai batace komai ba....
Dubanta ta miyar gun TAKAWA tace "ranka ya dad'e dan Allah Haidar fa? Inaso na ganshi ina kewarsa sosai, kuma bana ganinsa anan, ko yana gun momyn sane?" k'ura mata ido yae yana tunanin maganar ta, batasan momynsu ta mutu ba kenan? Meenal ce ta katse tunaninsa da cewar

"Momynmu ta b'ata, tun randa ta b'ata  daddy kullum seyayi kuka, nima nida Haidar mukanyi kuka sosai, amma yanzu dakike nan na rage kukan, kuma rannan kikace zamu ganta inshaa Allah ko?" Shiru tana nazarin kalaman yarinyar ta kuma mayar da dubanta zuwaga TAKAWaa

"Inshaa Allah zamu ganta ne, karki damu kinji, daddyma zan bashi hakuri ya dena kuka, kina cewa Allah ya bayyanar mana da mommynki adu'a yanada kyau sosai, kuma idan kinawa mommynki adu'a zata dawo inshaa Allah indai tana raye, adu'ar yara karb'bbiyace" jinjina kanta tai  sanna ta qara cewa

"Kinga ranar da motar nan ya kad'eki, hadda rashin adu'a fitar daga gida, kinga idan da zakina karantawa kullum kafin ki fita  da babu abinda ze sameki inshaa Allah, idan ma an rubuto motan ze kad'eki sekiga sanadin adu'ar nan Allah ya kareki abun yazo da sauk'i, kinga amaimakon wannan karayar seki gurd'e kad'an, yanzun ma nasan adu'ar daddyn kine damu ya sanya ba'a goshi kikaji ciwo ba a baya, sumar kanan naki ze fitone inshaa Allah" Lafewa ajikinta yarinyar tayi

"Ni bansan wane adu'a bane ba mom"  koyar da ita tashigayi tana fad'a tana nanatawa, sunyi yakai so goma seda ta tabbatar ta hardace kannan ta mayar da dubanta zuwaga TAKAWA wannan yarinyar tana matuk'ar rikitar da   shi, me bibiyar ka da sharri baze tab'a cewa ka nemi kariyar Allah ba, danyasan ta shallake ta kowa, menene ainahin abinda ya had'ashi da wannan baiwar Allah ne wai? Maganar Ameenan ce ta katse masa tunanin sa

"Ranka ya dad'e yau haka kawai hankalina yake gun Hidar, dan Allah   ka kaini gun yaron nan na dubasa, kwana biyu kenan shiru ban ganshi ba" murmushi yae yanzu kam, betab'a ganin tayi irin saba yace

"Muje" rarrashin Meenal tae, sanda ta hakura sannan suka wuce akan zasuje su kuma dawo ba jimawa, da jakadiya suka barta sannan kai tsaye da kanshi yau yaja motar suka nufi gidansa, yanaso yakai k'arshen tunanin sa....baya fatan yawa mutum yankan hukunci ba bisa ga hakk'i ba....beko kalletaba, har suka isa a wurin wani tangamemen gate me asalin kyau zubin na turawa....tasha mamakin ganin duk girman filin gidan gidane very cute cen a laqe, ga korayen ciyayi dasuka farfajiyar gidan k'awanya yayi kyau matuk'a......fadawane da kuma securitie's tako ina, kai tsaye wani parking space ya tsaya suka fito, daganan batare da yayi magana ba yashige gaba tabisa a baya, a parlor suka taradda Hidar wanda a take ya rugo da gudun sa ya rungume mom d'insa, Murmushi TAKAWA yae yana mamakin yanda yaran ke tsananin son yarinyar, yama kula bazata wuce 17 yrs ba, ita kuwa meze kaita shiga dabgar daba nata ba?...... Wucewa yae a d'akinsa befi 12mns ba yafito  daga room d'in kai tsaye hanyar waje yae, sak'on Talented ne ya fito dashi d'akin a birkice

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now