page 10

2.6K 261 2
                                    

[6/18, 12:36 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

           10
Idansu ne ya gauraya da juna, lokaci d'aya k'irjinta ya doka, Hidar ne ya katse tunanin da dukkansu keyi

"Daddy karik'a kiramun mom, kaga inafa missing nata sosai" da murmushi Takawa ya kallesa

"Zan kirata idan bama tare karka damu, sekuyi magana ko?" Murmusawa kurun yaron yae, daganan suka k'arayin shiru, da k'yar ta tattaro courage d'inta, gayen yana mata k'warjini sosai tace

"Abu Haidar nace dan Allah ko jiyan a motanka na bar wayana?" K'ura mata ido yanzu kam yae

"Ea amma sedai na siya miki wata, cox wannan tafad'i a hannuna kuma ta fashe" yak'e tayi

"Laa haba ba komai, ka bani ita a hakan kurin zan cire layin cikin, ai ba'ayi ranko ba tsakanin mu" Bace k'ala ba itama kuma ta kame bakinta, so yakeyi yace ta bashi number wayarta amma sam yakasa sabida tsabar jinkai da mulkin dake kansa.....Hmmm TAKAWA kenan.

************
     Tunda Meenal ke rayuwa aduniya babu abinda ta tab'a k'wallafawa arayuwarta kamar son auren yusuf, kwanakin nan har mafarkai takeyi da Muhammad, tana tsananin son ta cika masa burinsa, kiran duniya tawa yusuf be d'aukaba shi kuma, batasan wane kalan tsana yake mata ba haka, a asibitin bayan an barta daga ita se Ameena ma se kiransa a waya taketa yi amma rejecting ma yakeyi, abin yana matuqar damunta, Ganin ba kowa a d'akin ya bata damar sadda kanta a k'asa ta soma rero kuka mara sauti me tsananin tsuma zuciyar me sauraronta, sosai takeyin kukanta, ashe kulawar da take samu daga gun Muhammad abune me matuk'ar muhimmanci arayuwa abune kuma tsananin tsadar gaske, ba'a siyan so akasuwa, ayanda take da tsananin kyawun nan bata tab'a zata akwai namijin dazece baya sonta, tayi danasanin abubuwa da dama a rayuwar ta, ta wofintar da damar da Allah ya bata, bata ankare da ni'imomin Allah a kanta ba, seda TA FARU ta kuma K'ARE wa rayuwar ta....bata manta wani lokaco cen baya da Muhammad yazo gunta zance.....

"Ba kyau abinda kikeyi My Meena, kayi bak'o kuma kaine kazo ka taddashi a wuri bakayi sallama ba, ya maka kaki ka amsa masa, kinsan muhimmancin sallama kuwa? Yanada kyau ja daidai ta tsayuwr lahirar ka kafin lokaci ya k'ure maka, sam wannan ba tarbiya bace kace kai baka sallama" shek'ek'e ta kallesa

"Kaifa yaa muhammad na kula d'an bak'in cikine wlhy, daga zaran kaga ina cikin walwala na sena b'atamun rai, awurinka sallama take dole adai wannan lokacin bawai wurina ba, haka kurun zaka addabeni da tashin hankali, daga isowana ka soma mun Tafsiri da miyagun kalamanka mara dad'in sauraro? Ni kaga sefa in koma ciki abuna" ta k'arashe maganar da murgud'a masa bakin ta....kallonta yae

"Bazan bari se gobe k'iyama a tambaya mafarin zama dake ba nayi turu turu dole nane na gaya mikk gaskiya dan sadakina ne akanki, idan kuma gaskiyar ce bakyaso to kin huta, danni dole nane in sanar dake itan koda zakifi haka fashewa da takaici na" tsaki taji ta tashi tawuce abinta, ya dinga kiranta da baki bata waigo ba, bayan taje gidama ya dinga kiranta awaya tak'i d'agawa har tana rejecting, se yanzu take ayyana kalan zafin dayakeji a lokacin, ita kenan daya keso,ita kuwa bako son yusuf takeyi ba amma tana jin zafin sa sosai akan k'iyayyar dayake nuna mata k'arara.....kukanta takeyi har sanda takawa yashigo d'akin da sallama d'auke a bakinsa cikin wata irin murya dake matuk'ar bata mamaki.....share hawayenta tayi tana k'ok'arin basarwa kaman ba'ayi ba, koba abinda yake damunta, sarai kuwa ya fahimci kuka takeyi, amma tun d'azu shi hankalinsa yana gun Ameenan sa, yamatsu yaga ta kwana lapiya lau......ganin ta k'urawa Meenal ido ya sanya yaje ya tsaya kanta

"Meenal yaya dai? Ya jikinki?"  Kwab'e fuska tai

"Daddyna mom kuka takeyi, ka ganta nan ko yanzu kuka takeyi , tun d'azu take kuka kanta ze mata ciwo kaman naka ko?" Waigawa yae ya kalli Meenal

"Oum Hidar yada kuka kuma, wani abinne yake damunki" Sosai meenal ke neman wanda zata zauna tayita kuka ya rarrashe ta, wannan ne ya sanya ta kasa tsayar da k'wallan ta wuri d'aya koda batayi masa magana ba, hannayensa  duka biyu ya zura a aljihunsa ya k'ura mata ido bece mata ci kanki ba, tafi mintuna biyar tana kukanta yanzu kamma me sauti amma bece komai ba, har sanda tayi shiru dan kanta, shida Small Meenal se kallonta sukeyi tanata kukan, share k'wallanta tayi da bayan hannunta shi kuma ya tako a hankali har inda take ya zaro hanky a aljihunsa ya mik'a mata, ba musu ta karb'a ta share hawayenta sannan tace

"Kaina yanamun ciwo, dan Allah kozaka sanya a saukeni a gida" Bece komai ba se kansa kurin daya d'aga mata alamar to.....matsawa tai gun Meenal tace

"Name sake zanje gida, kaina ne yaketa ciwo kinga ai se kuka nake ko? Gobe zan dawo banida school gobe so tunda zafe zanzo kinji?" Mak'e kafad'a tai ta shagwab'e fuska

"Mom dan Allah ki kwana mun, bana son wannan Jakadiyar tazo nan" murmushi tai

"Kiyi hakuri my Meenal, goben zan kwana miki kinji, gayamun me kikeso na taho miki dashi gobe?" Shiru yarinyar kamar me tunani, Meenal ta k'ara cewa

"To tunda bakida zab'i kona miki donuts cake ne da julaibi, zanma had'a miki da favorite d'inki milkshake, nida kaina zan miki kinji" murmushi yarinyar tai

"Nagode mom, ki kawomun kalan chicken na yau yayi dad'i, mom kuma kizo da wuri kinji" gyad'a kanta tai

"Karki damu zanzo da wuri inshaa Allah" Hannu ta d'aga mata ta juya, shi kuma d'an mulkin ya murtuk'e fuskar nan, kallon sa tae

"Dan Allah Abu Hidar ka sanya a dire ni mana, kaina ne yakemun tsananin ciwo" shi dama so yakeyi  ya gano inane gidansu amma yana tsoro kar had'in bakine na masu neman cutar dasu...amma haka yace

"Muje" itane tashige gabansa shi kuma yana baya yana tafiyar mulki da isa har suka zo harabar asibitin, da motoci sunfi goma suka jeru, a motar rannan suka shiga shida ita, suna zama wayanta message ya shigo tana dubawa yusuf ne......

"Kina damuna da yawa Ameena, na sanar dake bazan tab'a aurenki ba, bana sonki wlhy na tsani me sanki ma, ki dena damuna dan bazan tab'a aurarki ba, koda zaki mutu kuwa, idan kuma kika takura mun sena mayar dake abar kwatance a gari mayya kawai, me mugun hali, kin kashen yaya na yanzu kuma ni kike shirin zaki kashe, wlhy sena illata rayuwar ki idan baki fita a harka naba"..... Sosai ta kasa controlling kukan ta, takuma shigayi ba k'akk'autawa kallonta yakeyi, yarinyar tana bashi mamaki komai nata sekace wata jinjira, idan ma akanshi take wannan kukan gwarama ta dena, idan akanshi  take abubuwan dazasu janyo ra'ayinta akansa gwarama ta dena, wannan abin yana dad'a  tunzura zargin sa akanta, tabbas tasan wani abu game da mutuwar matarsa dama bibiyar rayuwarsa da akeyi, sun sanshi da rashin son kukan mace, abun  yana d'aga masa hankali idan yaga ana kuka ma ba mace, bece komai ba har suka direta agidan da dama so yake yaga inane.....

****************

     Wayarsa ya zaro daga aljihunsa ya danna lambar talented Nusy, bugu biyu ta d'aga ya furta

" Maitama house 12 A......Amina Almustapha....a dubamun tarihin rayuwarta, inda take zuwa, dawa take mu'amala? Menene komai nata a social media, dawa take hurd'a kuma su waye take da alaqa dasu a masarautar Hankaka......

Mom Nu'aiym.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now