page 36

3.8K 304 13
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

  Wattpad 68billygaladanchi.

                36

---------------------
       Zainab ce ta fara zuwa akai mata gwajin DNA d'in, ta dawo ta kafe kaman ba komai ta adana result d'inta ta kuma barwa asibiti nasu ta dawo abinta, daganan sarki ya shirya ya shirya tafiyar sa da matarsa da uwarsa da harma da waziri aciki, haka sukaje binciken lafiyar su haka kurun se jikin gimbiya ke bata akwai wani abu amma ya zatayi batada zab'in daya wuce ta kame  bakinta tunda yake inma akwai wani abun itadai batasan ko meye ba, tunda yake sharrin dasuke k'ullawa mafiya yawan Abdurra'uf be san dashiba, haka dai akai kusu gwajin harna ciwon sugar da komai ma kan daga bisani su juya masauki.

   Tun shigarsu hotel d'in nan idan khamal system yana kansu, burinshi haris yae dabarar dayace komai ya kammala, yana nan tsaye a harabar hotel d'in har k'arfe goman dare harma ya sare seya tsinkayo su susu biyu wato waziri da haris driver, komawa yae kusada motar su ya watsa wannan powder aciki dama haris ya barmasa ita abud'e ne akan da zaran sunzo shiga kurun zasuyi zuwa time d'in shi kuma seya d'an tsagaita basaso shi powder ta kamashi, Suna zuwa ya bud'ewa waziri gidan baya ya shiga tsaigon zagowa seda aka d'anyi some seconds koda ya zago ya bud'e gaban motar seya toshe hancinsa da hanky, ya lek'o gani yae wazirin sharkaf yae bacci, fita yae ya d'aure fuskar sa ta wurin hanci yanda abin baze buge shiba sannan ya shiga ya tashi motar direct zuwa inda aka umarcesa yakai shi, kusan time d'aya suka isa da khamal system, tare suka kwashe da Haris zuwa cikin gidan, seda sarki ya zauna sosai sannan suka tashi waziri da abin tayar da mutane idan an shaqa musu wancen abun tare da sanya haris baccin k'arya dankar a zargeshi akan wani abu. A razane ya farka ya soma kame kame beko kula da sarkin ba seda Kamal ya sanya rufaffun takalminsa ya murje masa yatsunsa k'ara ya k'wallah don azaba ya janye hannun ya kalli inda haris yake kwance sannan ya soma rarraba idanshi zuwaga mutanen dake palor d'in d'aya bayan d'aya cikeda tashin hankali idanshi na sauka akan SARKI JALAL ya zabura ya mike ya soma salallami, k'afarshi kamal ya bige ya fad'i agun ya wankesa da lafiyayyen mari

"Kai ka nutsu agaban sarkin gaskia kake tsohon munafukin Allah" khamal ya fad'a yana me k'ara murza manya manyan takalmin sa akan yatsun k'afar ta waziri, rasa me zeyi yayi yahau kiran sunan Allah murmushi irin na manya Sarki jalal yae kanyace

"Waziri gani kuke kamar kullum duniyar a hannunku take ko? Gani kuke kamar Allah baze tab'a kub'utar dani ba ko? Gani kuke kamar kunshige agabana kummun zarrah ko, to kunyi kuskure kaida Gimbiyar Rusau kun tsokalo tsuliyar dodo, shekaru 33 dakuka azabatar dani kai sena azabtar dakai acikin kwanaki uku kacal, ko yanzu sak'o ne zan baka idan kaje masarauta ka gayawa sarauniya hassy nace Ina gaisheta itada gimbiyar Rusau ka kuma sanar musu cewar nace Nanda d'an lokaci k'ank'ani zanzo domin na karb'i mulkina, bokan su dasuke cewa zezo ya kasheni ka sanar dasu nace sun manta da littafin Allah ne? Dashi nake tak'ama kuma duk dare bacci na nake shak'a sabida nakanyi adu'oin tsari ubangijina yana tare dani daga k'arshe ka sani wlhy ka kawomu  zobuna na!!! Idan har ka bari kwana uku tacika bakaje ka kaisu wurin hajiyar kilisa ba sena kashe ka, kayi wani yunk'uri akaina kasha wahala mahaifiyata ma tana k'ark'ashin kulawa me yawa krkace zakayi wani garaje" Murya na rawa waziri yace

"Base naje cen ba kullum suna hannuna gasu nan ranka ya dad'e bari in cire maka su in bayar yanzu dan Allah karka kasheni" Murmushin yak'e Sarki Jalal yae

"Cire ka ajiye, sannan idan kaje gida ka sanarwa Sarki Abdulra'uf ina gaisheshi" Da sauri ya kalleshi cikin tashin hankali dariya yae

"Bazaka iya fad'aba? Sabida kasan zece ka kawoshi nan kuma kaima bakasan ina ne nan ba" Waige waige ya shigayi kan yae wata magana har kamal ya shak'a masa hanky atake ya k'ara zubewa wurin a sume, zobunan sarki suka cire suka caje aljihunsa kai tsaye suka zare wayoyin sa da wani tsohon carbi da sarki yasanshi dashi tun suna yara yana mamakin waziri me yake da wannan carbin ta mugun ta..haka suka kwashesu shida driver khamal ne yaja motar duk suna baya yakaisu harabar hotel d'in ya ajiye motar yae tahowar sa.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now