page 26

2.5K 279 44
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

   Wattpad @ 68billygaladanchi.

          26

Tajima sosai acikin bathub d'in tana wanka, lumshe da ido kurun take tanajin dad'in yanayin ruwan datake ciki ga d'umi ga kuma k'amshi me sanyaya zuciya, watak'il Allah ya tsara mata hakanne tunkan zuwanta duniya, watakil dama cen kuma muhammad bazata rayu dashi rayuwa me tsayi ba, inama ace wata tarayyar aure ta tab'a shiga tsakanin ta da muhammad, daya bar mata koda jininsane da zata rage rad'ad'i da azabar rashinsa datake ji, gashi mutuwar sa ta jefata cikin rigingimu iri iri, yanzu batada tabbas akan rayuwarta ac8kin wannan gidan, kuma bazata gusheba komai azaba seta aikata wani abun alkhairi a rayuwarta, a k'alla idan ta kuskurewa muhammad a matsayinsa na mijinta to ta kyautatawa Mu'az kota samu rabauta, tana mamakin wannan masarautar inda zaku iya b'oye d'an adam awurin da babu rana babu haske shekaru kusan 33, batada  detailes akan wa suke nufi amma yanzu data auna maganar da mahaifin mu'az taga yanda suka razana ta tabbatar wa kanta cewar sarkin da ake nema ne suke b'oyewa, wasu abubuwan k'walwarta seta gagara d'aukar su... Haka tayi kusan 30mnt a toilet d'in kanta sako mathrobe ta fito da wani towel d'aure akanta tana kokarin tsane ruwan sumar kanta data wanke har ita, anan d'akin ta sameshi inda ta barshi, d'auke kanta tae gefe d'aya kamar bata gansa ba sannan ta zauna ta soma shirinta cikeda nutsuwa bece mata komai ba dai harta kammal ta saka doguwar rigar material mara nauyi bayan data busar da gashinta da hand drayer, kwanciya tae sabida kanta yayi zafi bacci takeso tayi tad'anyi rebooting brain d'inta, muryar sa cen k'asa yace

"Inzo muyi Bacci Meenaly?" Murmushi tyi jin sunn daya kirata dashi tace tana murmushi

"Ea mana, idan kanajin bccin kazo muyi tare" rage kayan nauyin dake jikinsa yae sannan ya ragewa d'akin haske ya kwanta tare da rufa musu duvet dake kan bed d'in.

************

     Hajiyar Rusau da waziri sun gama firgicewa akan wannan lamarin, sabida haka waziri dare yabi yaje gunta, zaman tattaunawa sukayi su duka biyu hankulansu a tare

"Waziri Nakasa gaskata da kanka kake shirin tona mana asiri, tunda yake dasa hannunka muka b'oye tsohon sarki, yaya zaka gayawa sawun takawa wannan maganar bayan kuma ksani cewar ita d'in matace awurin d'ansa d'aya tilo" Murmushin takaici waziri yae yce

"Allah ya baki Nasara na rasa dalilin dake sakawa mata kuke da raunin tunani, bakya ganin maganganun mu damukyi nida ke dake da recording akansu, aini ba yaro bane ba nasani cewar bakya kik fad'a ba dukda cewar cewa tamun ke kika gaya mata, takuma fad'i maganar da a d'aya b'angaren ke baki masan da itaba, wannan itce waw tarta ta farko, batasan waye waziri ba wasa take dani, aljanu ne ke aika mata saqon maganar mu tabbas, kuma zanyi amfani nima da nawa aljanun inga kasheta mu huta" Nisawa tayi

"Waziri kafasan ni bana sha'anina da kisa sam, bazan kashe kowaba akan maganar nan, zamu dai nemo mafita, kokuma kasa a rufe mata baki kurun" Nisawa yae

"Zan saka gardawa su datse mata harshe da 'yan yatsun hannayenta duka goma, kinga babu magana kuma babu zancen rubutu ko?" Murmusawa tae

"Hakan za'ayi, nizan umarci Me likimo data sanyawa kuyangi da masu gadin b'angaren ta abu me sanya nauyin bacci, kaga daganan semu lula a aiwatar da aikin" jinjina kanshi yae

"Wannan yarinyar da shirinta tazo wannan masarautar, kuma ta Allah ba tata ba" haka sukaita tattauna mugayen abubuwan dasuke k'ullawa.

********

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now