page 28

4.1K 309 57
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

    Wattpad @ 68billygadanchi.

           28

Kallon ta yakeyi yanda ta lumshe idanta yasani fuskarnan tana mata azaba, magani ya d'akko ya mik'a mata, ta karb'a tasha lapia lau, yace

"Meenal?" Ya furta sunan tamkar shiya rad'a mata cikin wata murya dabata tab'a sanin yanada irin shibama, mu'az me izzar nanne dajin kai da wannan muryar dayake slow sekace mace ma tsabar yanga yau shine da wannan muryan data kasa ma fassara wace iri ce? Murmushi ta sakar masa da bata shirya zuwan saba amma batace masa komai ba yace

"Ki daure mu kwana anan mana inyaso da safe semu tafi gida" murmushi tayi

"Banida kayan sakawa fa Takawa, haka zan zauna" ledar daya shigo da ita ya janyo ya ware ta

"Na siyo miki kaya mana, yakamata ki sauya ma" kayan daya ciro ne ya bata mamaki, doguwar riga d'aya sekuma  riga da wando da kuma bingilalliyar riga, se turaruka da kayan bacci biyu" kallon sa tae

"Duk wannan a kwana d'aya Mu'az" murmushi yae, mahaifiyar  Abbansa  kurun ke kiransa da Mu'az kai tsaye se meenl kuwa, besan dalilin sa najin dadin hakan ba kuma

"Kije da saura gida manax yanzu dai ki saka wannan rigar" ya mik'o mata daidai lokacin da yake mik'ewa tsaye, kallon sa ta tsayayi bata karb'i rigar ba, b'ingilalliya gata ita kad'ai, yamutsa fuska tae

"Nikam sedai na sanya doguwar, wannan a 6ingile" murmushi yae

"Nikuma wannan nakeso ki saka" ya nuna mata b'ingilalliyar rigar dake hannun sa, baki ta tura tana k'unk'uni yakai yatsansa ya d'alli bakin dafe bakin tae ta tabare fuska tamkar zatayi kuka

"Abu Hidar da zafi fa" murmushi yae na kugunta

"Gobe ma kya k'ara, maza tashi ki saka wacce nace d'in" Bata gushe ba seda ta gama doddoka k'afa a k'asa tukunna, dariya yae lokaci d'aya wushiryar bakinsa me fad'i ta bayyana yace

"Kya daiji dashi".

Wannan daren manne da juna suka kwana, kaika rantse sace masa ita za'ai a gudu, har mamakin kansa yakeyi shikam, sabida harga Allah duk soyayyar sa da Salma basa kwana d'aki d'aya, kai idan ma a masarautar suke kowa yana part d'in sa, kamar yanda sarki keyi seya buk'aci mace take zuwar masa har sarauniya kuwa, haka ma takawa sedai amasa zuwan sirri turakarsa, kuma yana gamawa ze cilla ki out, yanzu gashi tsakanin jiya da yau kurun jiyake yi idan ma babu Meenal akusa dashi toda matsala, wata iriyar nitsuwa yin bacci ajikinta ke sakashi ji.

***********
   Tunda suka shigo masarautar ake kallon su, ajiyar waccen motar yakai sannan yaje ya nemo taxi ita ta kawo su, kai tsaye part nata ta wuce sannan ta kimtsa sosai domin gabatar da abinda take shirin gaba tarwa.

Kamar yanda ta saba haka taje ta gabatar da shirinta tsaf tare da kuyanginta ta nufi hanyar part d'in Sarauniya hassy, sarauniya na ganinta hankalinta ya tashi ta sani tabbas seta k'irk'iro wani abun daze tada mata hankali gaba d'aya, zama tayi k'asa ta soma wurga mata gaisuwa cikeda girmamawa, kallon mamaki take seda ta watse kowa sannan Meenal tace

"Yake wannan sarauniya me adalci ki tallafeni, wasu azzalumai ne suke neman raina, jiya ban kwana a masarautar nan ba, lallai nayi babban kuskure shiga huruminki, ashe kece gatana, Allah ne kadai ya tserar dani, Takawa bashida wani banbanci da lusarin bawa a wannan masarautar, nafi buk'atar gawarsa dashi kanshi, sabida be damu dani ba, kece kike damu dani dole in damu dake(⌒▽⌒, ki tlafi maraicina zan miki dukkan biyayya" Wani murmushin kinma rainani Sarauniya  tayi kan tace

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now