page 25

2.5K 277 18
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

   Wattpad @ 68billygaladanchi.

          25

Idansa ya k'ura mata amma ya gaza furta wata kalma, buqatarta ta masa nauyi sosai baze tab'a iya rabuwa da ita ba musamman yanzu dayake tana dauke da ciwon dabesan inda ze tsaya ba baya fatan mata mugun abu, tunda ance infection ne amma ze watse da magani inshaa Allah, matsawa yae sosai kusa da ita ya d'aura kanshi saman cinyarta ya kwanta ya lumshe idanshi batare dayace mata komai ba, ganin yayi shiru ya sanya bata matsa ba, batasan sanda ta d'aura hannunta asaman sumar kansa ba ta soma shafa a hankali, cikin k'aramar murya tace

"Ina neman afuwarka, ban kyauta ba iyayena sun haneni akan neman saki awurin ka, kayafeni" murmushi kurun yae yace

"Kici gaba da shafan kaina bacci nakeso inyi kinji" Batayi magana ba sedai ci gaba da tae da abinda takeyi tana k'ara zurfafa cikin dogon tunani.

************
    Zagayar d'akin Sarauniya Hassy keyi tana nazarin bubuwan ban tsoron da Meenal ke mata, anya yarinyar nan ba aljana bace kuwa? Banda haka yaya zata rik'a aikata abubuwa sekace me yawo da rauhanai, a ina take samo bayanai akanta? Da ace agidane kurun take samun bayanan datake setace ko cctv camera tasanya mata cikn sirri, amma itada waziri dake fita wajen gari a ina ma zata samu bayanai, tayi tunani har kanta yayi nauyi amma babu wata mafita.

**********
    Yau shiri me tsafta meenal tayi ta d'auki hanyr zuwa B'angaren hajiyar Rusau,  suna zuwa part d'in bayi da kuyangi suka zube k'asa suna yarfo gaisuwa, seda suka gama duk ta watse su sannan tai zaman tamutela, ta hard'e k'afafuwanta guda biyu gu d'aya ta mik'a hannunta ta d'auki soyayyen chicken breast dake cikin bowl na naman kajin da Hajiyar Rusau keci sannan tace

"Tsohuwa me ran k'arfe kink'i ki gangara mu huta" kallon mamaki Hajiyar rusau ta wurgwa meenal cikeda zargi tace, kan tace

"Mun soma wasan jika da kakane nikam Meenal? Naman ta kaiwa cizo seda  ta had'iya sannan tace

"Ina matuk'ar son akirani da sunan daya dace dani wato Sawun takawa, karfa ki nuna kishinki a fili, koda yake kefa sam ba'a gane halinki ko?" Mmakinta hajiyar ke k'arayi amma batace komai ba dai

"Tsohuwa kinsan mesa naci wannan naman?" Girgiza mata kanta tae kantace

"Ina kuwa zan sani Ameena" murmushi meenal tae

"Sabida dai Nasan mutum sakawa kanshi maganin daze rik'a mantar dashi komai ba" Da sauri ta d'ago ta kalleta, amma yanda zuciyar tsohuwar ta buga bazanyi k'arya ba takai jaka da rabi a hawan jini, muryar ta yana rawa ta furta

"Ban gane ba" Dariya meenal tae har duk'a hak'waranta suka bayyana tace

"Yazaki gane kuwa tunda bake bace acikin hak'on d'an adam a b'oye kusan shekaru 33, ai gaskiya wannnan tarihin ya girgizani" Mik'ewa tae cikin tsananin tsoro jikinta na k'yarma tace

"Ina kika jiyo wannan labarin kekam" mik'ewa Meenal tayi tana dariya tace

"Daga bakin waziri naji komai, ciki kuwa hadda Yanda aka k'arasa tsohon sarki mu'az, kokinsan mutuwar guba akwai azaba" Dukda jikin tsufa irin na  hajiyar rusau sedabta cafko wuyan rigar meenal

"Shi wazirin shine yaketa gaggaya miki maganganun banza da k'arya ko?" Mumushi tayi kanta zare hannunta ta dire k'asa

"Kinga dai ko a muji na kasaki ko, yanzu nice 'yar gaban goshi, kibi a hankali ko kuma duniyar masarautar Hankaka ta d'auki labarin yanda kike amfani da mujinki wurin hanawa hajiyar Kilisa haihuwa, yakamata ki gane waziri fa ya gayamun komai, kuma idan kika kuskura kika masa wani abun to asirinku duka zan tona, sabida inada Audio na hirarrakinku, da bubuwam dakuke k'ullawa, Bari in barki da wannan" ta ajiye mata wata k'aramar waya k'irar Itel a k'asa

"Kije ki saurara, gasunan aciki nake nasani ba lallai ki iya sarrafa wayaba yanda kika iya makirci" sororo Hajiyar tayi tana kallon ta harta fice tabar gidan gaba d'aya, mota ta hau zuwa masarautar hankaka ta kudu gidan Waziri ta nufa kai tsaye taje ta tayi sa'a kuwa yana gidan, Tarba me kyau ta samu dukda jikinsa a mace yake tun zuwanta, a keb'antaccen wuri aka kaisu, bayinta ta sallama bayan sun gaisa sannan yace

"Ranki ya dad'e Sawun Takawa ga abinsha kid'an taba babu yawa" kallonsa tae ta had'e rai lokaci d'aya, shi kanshi ya tsorata da yanayin kallon data sake masa seda hantar cikinsa ta  kad'a

Meze sa inci, nasani ko har kun karb'o maganin haukatani kida Sarauniya kun b'ad'amun anan, kokuma nima so akeyi abani manta gida akaini a adana a hak'on d'an adam, wama yasani ko ni sena shekara miliyan acen" Da sauri ya kalleta jikinsa se qyarma yakeyi cikin takaici tace

"Koda yake dole ne a tashi hankula, aketa k'ok'arin kashe Takawa tunda dai ka sani Yarima Fu'ad nakane bana sarki Abdulra'uf ba, koda hake inaga sena fargar da mutane dubu dake cikin masarautar nan acikin daqiqa dubu cewar kunafa d'ebar kamannni sosai da Yarima Fu'ad watak'ila babarsa farkar kace kokuma dai kunada wata alaqa daya tsallake duk danginsa yazo ya ebi kamnni dakai, idan fama komai yamun dad'i daddagewa zan in fad'i yanda akayi da rashin Haihuwar Sarauniya me murabus wato Amoh dazo" Mik'ewa ye tsaye itama ta mik'e tana murmushi

"Hajiyar rusau ta iya bada bayanai masu muhimmanci, ayi kuskuren tab'ani kuwa in fad'awa sarki labarin yayanshi danake dashi tsaf a wayoyoyi mabanbanta sunkai guda dubu, acikin seconda dubu, al'umma dubu su sani, kaima gashi idan kanada fahimta idan ka saurara so dubu zaka gane inda na dosa" Ta juya tana wata dariyar shaqiyanci bayan data ajiye masa wayar a k'asa ....mutuwar tsaye kurun yae tayi, ficewarta  itakam.

**********

    A bed room d'inta ta sameshi zaune yana nazarin wasu takardu gaidashi tae dukda tana cikin mamakin ganinsa a wurin.....
"zoki gani Menal" ya furta a hankali, zare kayan jikinta ta somayi ta d'aura towel sannan ta sako hijab tazo ta zauna kusa dashi ya karkato mata laptop d'insa sannan yace 

"Wannan bashi bane yusuf?" Kallon hoton tae, sannan da sauri taci gaba dayi gaba, pics nasune shida Nusy gasunan barkatai, kallo ta wurgawa Takawa

"Me kenan wannan Takawa?"

"A haka na tsinta nima, ina mamakin inda suka san juna, sabida nan hotel ne pics din" Nisawa tayi sannan ta d'akko madubin idanta ta sak'al, cikin gaggawa ta,jona modern dakeda sim direct me data ta zak'ulo number yusuf ta shiga wani bincike, Number talented ma haka ta d'akko, tafi 40ms tana abubuwan dasuka matuqar burge takawa, kai tsaye ta harbo bayanan sirrin dake tsakanin su, tasha mamakin yusuf, sedai babu wani daya shafeta acikin maganganunsu, batada nutsuwa dole tahi bincike, ture system d'in tayi gefe d'aya tace da Takawa

"Takawa inaso muyi aikin taimakon juna dakai, sedai dole seka jajirce ka nunawa duniya bakasan komai ba, zakayi mamakin  tulin tarin abubuwan danasani a yan kwanakin nan, zan baka labarin komai amma hakurin nan dakayi na kusan 33 yrs sekayi wanda ya ninkashi a yanzu, inba hakaba zaka wargaza mana shirin mu, zan maka bayanin komai dalla dalla, amma fa so nakeyi ka zama kurma, karka tab'a nuna kasan komai, kuma nasan banfika ilmi da hankali ba amma a wannan gab'ar seya zamana nice nake bayar da orders ka gane?" Murmushi yae

"Ko yanzu na fahimci keta dabance irin wannan haddace computer kai tsaye, kece boss, zanyi duk abinda kikace" tana murmushi ta juya, "yanzu na gaji gaskiya bari nayi wanka da salla, idan na tashi a bcci zan baka labari meban tsoro, al'ajabi daban hirgita dole seka daure" Jinjina mata kanshi kurun yae ta juya zuwa toilet...

*Amun afuwa inata hidimar biki, kuyi manage da wannan, daganan zuwa talata zaku iya jina shiru, idan kuma Allah yabani damar yi zanyi, amma banyi alqawari ba*

Mom Nu'aiym.
    

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now