page 13

2.7K 267 7
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                       13
Juyawa yae da sauri batare daya tsaya baiwa message d'in wani muhimmanci ba,  idan yace ya tsaya tunani yanzu abubuwa da yawa kwab'e masa zasuyi....Asibitin dasu Small meenal suke aka zarce, kai tsaye suka bata taimakon gaggawa, Talented ta rud'e se kiransa a waya takeyi, idan ya nemi sanin infor na inda tasan tarihin meze faru a asibitin me zata gaya masa? Ga alama yau ko kadan be yadda da zancen taba, idan hakane akwai damuwa sosai dan TAKAWA babu abinda baze iyaba idan ka tab'a shi, ko banza yaya suka iya da soja!!!!..

    Jini ake buk'ata bashida alak'a da kowa na gidansu, ta zubar da jini sosai, bemasan tukunna meze fad'awa iyayen taba, cikin nauyin jiki ya had'e kan Excort nashi da fadawansa suka dunguma gidan daya ajiye yarinyar rannan.....

   Sosai akai musu da tarba taban mamaki, tabbas Abba yasan wannan fuskar a duk inda ya santa sedai ya manta ko inane....karamci dai ya karramasu dukda akan hanyar tafiyar sa yake zuwa sokoto wani aiki, kuma flight zebi amma ya gagara sanar musu, shi kuma TAKAWA se wani shan k'amshi yakeyi, parlor yayi tsit sedaga bisani yai gyaran muryarsa yace

"Amm sedai hakuri, kasan mutane mazaka rasa mahassada ba, damasu so suga bayanka, yarinyar nan gidanne taje gidana ta duba yaronta Hidar, so bayan nafita sekuma wasu b'arayi sukaje gidan da zummar hallaka yarona, to dabasu sameshiba ban saniba ko gaddama ta musu, se suka yanketa a hannu yankan kuma yayi muni gaskiya, ta zubar dajini me d'inbin yawa, yanzu haka jini ake buk'ata, tanacen asibiti, shine naga dacewat zuwa in sanar daku dan yin shirun kuma ba alkhairi bane ba" zabura dad yae

"Wai wace yarinyar nan gidanne takeda wani yaro? Yallab'ai ni 'yata ai mijinta daya rasu basuda yaro a tsakanin su, kuma bata taba haihuwa ba, kodai kuskuren gidan kukayi?" Kishin gid'a yae...TAKAWA akwai iko, mulki da jin sarauta, yana san sarauta yana muradin yaga zama sarkin a masarautar hankaka ya mulki birnin su....

"Sunan ta Ameena Meenal, nasanta bance ta haihuba, yaron wurina nake magana, kuyi hakuri kuzo muje ku ganta, tana buk'atar ku a wurin" Zuface ta soma tsatsafowa dad ya mik'e ya juya ciki, mahaifiyarta ya sanarwa suka d'unguma asibitin cikin tashin hankali mara misaltuwa!!!.

***********
    Bacci takeyi sabida allurar baccin da aka bata, jikinta duk a mace kana kallonta kasan har a cikin baccin azaba takesha sosai!!, dad hannunta ya rik'o

"Lelena kuma abinda kika janyowa kanki kenan, bakisan mutane ba kin zure musu? Bakida wasu dangine a rayuwa dazaki kafe akan wancen? Ina ke ina Ahalin gidan sarauta? Inake ina huld'a da Soja!  Yana maganar tamkar tana jiyo sa, duk a rud'e yake....mom dai se kuka takeyi, jinin dad aka gwada yanayi aka deba aka jona mata.

**************
   Talented mesa kike so ki mayar dani yaro k'aramine wai? Ina kika san da zancen zuwa kisan meenal?" Sadda kanta tae a k'asa cikeda fad'uwar gaba

"Ranka ya dad'e ka fahimceni, ni nagani ne a message d'in yarinyar tawa wani lamba, akan zataje gun meenal, idan kafita zata sanar musu ka fita se suzo, kaga message d'innan" ta mik'a masa wasu takardu datayi printing ya duba sosai haka d'inne kuwa, murmushi yae da gefen baki

"Yaya akayi kuma kikasan sun juya zuwa gun HIDAR" ai ban saniba, ina kaine ka kira a waya kake sanar dani akan hakan, kuma kace ka barta agidan, hasashene kurun yarinyar tanada hurd'a da mutanen damuke zargi na kusa ma, dole ne mu yakice ta cikin sauri, kurun a rabata dasu HIDAR ace karta kuma zuwa inda suke bashi kenan ba?" Gyaran zaman hularsa yae, yaune rana ta farko da talented ta gaya masa maganar dayaji be yadda da itaba, bawai zarginta yake ba amma yaya zata d'aura laifi kacokam akan yarinyar, Hidar ya sanr masa mom ce ta b'oyesa, tace masu kashe mutane a film ne sukazo karya fito, idan hakane kenan taimako tae. Barin gidan talented yae zuwa gidansa kai tsaye.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang