page 18

3.2K 278 26
                                    

   *🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

Wattpad @ 68billygaladanchi.

         18
Talented zaune saman kujerar office d'inta yayinda yousouf ke zaune saman kujerar da aka tanada sabida bak'i, ya mata k'uri da ido cikeda shak'iyanci, ita d'inma shi take kallo dukkaninsu da abinda suke sak'awa aransu game da juna, murmushi suke sakarwa juna wanda suka d'ai suka san ma'anar sa....
"Ki bari kawai gayen nan shimafa akwai wayau,duk wata hanya dazamubi seya b'ata b'ata mana ita akan me"  shafar idanta tai dake mata d'an k'aik'ayi kan tace

"Bazaka gane nafishi wayau ba se sanda na gama da wannan Meenal d'in, nifa inaga aduk duniya babu wanda yakaini k'inta, ina murna Allah ya rabani da salma batare danasha wahalar komai ba, ita kuma kaman daga sama tazo da wani rainin hankalin ta harta aure mijin, tunanina fa d'ayane ada Hidar kinsan Hidar shine kurun abinda nake tunanin, inga na kasheshi na kashe banza, sabida salma ta tafi dole magajin takawa ya bita, dankuwa nice nan zan haifi sarkin Hankaka na gaba, dan idan ina numfashi babu me haihuwar magaji seni, Hidar kuma sena kasheshi" Murmushi yusuf yae

"Idan kuma ya kasance tayo cikin 'yan biyu tun acen india fa?" Murmushi tayi

"Yusuf kenan, ai kuyangar dasuka d'auka itace matsalarsu, acikin kuyangin nan akwai wacce take guruwa a fannin aikina, duk wani motsinsu daka sani ina kallon su, Akwai camera's d'ina har cikin toilet na d'akin asibitin dasuke, kasan fa ni nawa k'anana ne, rannan ma nazo nantarar hadda wani mata wanka, kullum ma shiyake mata, ai bakasan Takawa bane ba baze tab'a kusantarta ba se idan ita ta kawo kanta, itan ma se yaga dama intazo, jiyama atare suka kwana amma shi ya shinfid'e kansa k'asane warwas...." Girgiza kansa yae

"Talented nifa kin soma bani tsoro wlhy, shisa ake cewa ka rok'i Allah ilimi me amfani, gashi naki yana amfanarki, anya kuwa nima baki d'ana mun camera's ajikina ba?" Dariya tayi tacigaba da jujjuya kujerar datake kai

"Bazan baka tsoro ba sena gaya maka sanda nace cire camera's a gidan Takawa akwai wanda na saka a takalmina qana nan, duna nan sunbi tiles, sedai basa d'akko rahoto yanda nakeso sabida samasuke kallo su, amma inajin maganar da akeyi, wannan remote dana nuna masa, tracke ne amma dashi na d'ana camera's d'in, duk inda naje inda nakeso na dasa senayi pressing nasi se camera tafita tawa mazauni agun, shifa gani yake kamar yafini wayau amma ni wlhy har hanjin sa nake gani"  Dariya suka saka ya mik'o mata hannu suka tafa

"Kindaiji likita ya kawo 1.5 bako gaddama ko, cikin rufin asirin Allah" Tana murmushi tace

"To ai ya kyauta d'an kasuwa ni karma kayi cinikin kaina ban saniba"  yana dariyar sa ya mik'e tsaye

"Zan tafi, zakiga na tura miki 200k acikin acc naki, ki siyamun wannan turaren dakike shafawa me k'amshi kinji" Mik'ewa tayi tana murmushi

"Ayi haka Na talented, kaida nacewa ka kashe abunka kurun kaji dad'i" Fara'arsa ya fad'ad'a... "Karki damu talented, gudummawarki me yawace awurina nifa wlhy harna fara sanki, sannu sannu nasoma jin haushin Takawa ina kishinsa sosai" Dariya tayi

"Nagode da soyayyar nima haka" ya juya kurin yabar office d'in.

**********
    Asuba shine ya soma farkawa seda ya tasheta sannan ya bar d'akin gaba d'aya yaje guest toilet ya kimtsa kansa,yae alwala ya nufi masallacin dake bayan layin dayake akwai musulmai sosai a area dasuke.
    Tana ganin pillow ta gane anan ya kwana, bata damuba tunda yake anan india sun saba kwana d'aki d'aya da Muhammad bayan da aka sallameshi, memories nashi se yawo suke mata akai, wanka tae tare da d'auro alwala ta kimtsa tsaf abinta cikin doguwar rigar silk material me asalin kyau kalar ruwan toka tayi kyau ba laifi sabida jinya ya sanya tayi k'iba ta cicciko abinta sambarka, bayan ta idarda sallah tajima tanawa kanta da yaa muhammad adu'a samun rahamar Allah, sannan ta koma ta kwanta, se lumshe idanta takeyi, tanaso ta saka wani abu a bakinta yunwa takeji amma menene zata saka d'in, bataga alamun komai a d'akin ba sam.
Da sallamar sa ya shigo  d'akin ta ansa cikin murya cen maqale batare datayi yunk'urin tashiba, zama yae ata gefen gadon yace

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now