page 48

3.3K 339 16
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

   Wattpad @ 68Billygaladanchi.

*Wannan shafin Nakine Ummu Ramlat, inajin dad'in comment d'inki Allah yabar k'auna*

*my wattpad pipu vote naku sunayin k'asa, mutum sama da 1k su karanta page befi 200vote ba zan muku yaji fa tam*

                   48

Masarauta ta d'auki hargitsi acikin kwana bakwai da aka d'auka na mik'a su waziri hannun hukuma, mutane da dama sunga rashin dacewar mik'a sarauniya hassy acikinsu kodan zamtowarta mace, amma sarki yayi biris dasu danshi yasan inhar muddin bacen take ba bazasu samu sassauci ba, bazata gushe ba harseta cimma mugun nufin ta akansu. Gaisuwa irin ta girmamawa yayiwa mahaifiyar sa Hajiyar Kilisa bayan nan se sukayi shiru dukkansu na wasu 'yan dak'ik'u sedaga bisani hajiyar tace

"Na fari dama cewa zan maka ka mayar da Hansatou gida, ta cancanci dukkan girmamawa tunda yake tayi zama sarauniya ta garin nan, bayaga haka kuma k'anwace awurin me d'akinka koda ta kawar da kanta tokuwa badan hakan yana mata dad'i ba" Murmushin Takaici yae

"Hakan idan kina ganin shine daidai sena sanar a mayar da ita d'in, amma  kinsan halinsu sarai, zata iya b'ullowa da wata muguwar hali kuma" Gyaran zamanta tae

"Nasan halinta kuwa sosai, ka mayar da itan idan yaso seka karya lagonta itada Daurama a baynar dasi a fada kowa ya huta, daga zaran komai ya gama tonuwa zakaga ta saduda" Godiya yayi tare da alqawarin cika mata sharad'in ta na dawo da hassyn badan ranshi yaso hakan ba sedan biyayya kawai.

************
   "Tokuma  ni sabida Allah dan kawai sun fad'i k'aryarsu se ace bazanyi tafiya ba, kalli k'afana yanda ya kumbura, dan Allah ni kace su bari mu koma gida kaji"  dafe kanshi yayi,rigimar da meenaly ta tsira a 'yan kwanakin nan yawane da ita, gabatada lapia se shegen fitinan tsiya

"Naji zance su sallameki k'afan kuma zan matsa miki seya sauka kinji" kwantar da kanta tayi ajikinsa

"Yama daifi gaskia" rik'ota sosai shima yae

"Meenaly i missed u, yaranki ma sunata tambayar ki" murmushi tayi

"Same here hubby, amma ni ka sanya akawomun su Meenal kaji" Kwanciya yae harshi akan qaramun gado ya kwantar da ita akan k'irjinsa

"Zasu zo suyita k'iriniya ga ba'aso kina motsin nan, zama su iya sakaki yin wasan ball, gwara su zauna gun ummie" Turo baki tayi
."nima idan muka koma gun ummie zam tafi kai baka sona naga alama" murmushi kurun yae be kula zancen taba

"Me kikeso ayiwa taurari?" Murmushin takaci tayi

"Wannan wai? Hmm kasheta nakeso ayi sabida itama kasheni tasoyi kuma ta kashemun yaro"

"Wannan shari'ar musulunci ce ko shari'ar kice" ya furta yana kallonta cikin ido

"Ka barmun ita da ranta ka mayar da ita baiwata, sena ghana mata azabar bayin datakejin tarihinsu a duniyar data gabaci tamu duniyar, sena nuna mata ba'a tab'ani a zauna lapiya, zan shayar da ita mamaki ta hanyar dazatayi data sanin zuwan duniya da wayar gari ta ganta acikin masarautar hankaka zan dawo Ameenatou na, zan ari wani hali nawa dana rataye dacen baya na dena amfani dashi, zan nuna mata acikin mugwayen dake duniyar nan nima ina cikin sahun farko imani ne ya b'oye nawa da hasken musulunci" sajensa ya shafa daga samansa har zuwa k'asansa yaja sauran gemun nasa

"Wannan hukuncin dakika yanke akanta yafi komai yimun dad'i na dad'e ina tunanin kalar azabar dazan bata dan nasan laifin ta be cancanci kisa ba dasena kasheta kuma in binne ta da sauran ranta agaban ubanta da uwarta amma yanda duk kika mata kinyi daidai" Shiru ya d'an ratsa wurin na wani lokaci kafin ya kuma cewa

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now