page 50

3K 301 16
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

*Muna barar adu'arku, Allah yayiwa member ta group d'inmu kuma 'yar uwarmu me suna Mama A'i  rasuwa, Allah yajik'anta da rahamar sa Ameen.*

      50

Jikinsa se rawa yakeyi tunda akace masa Takawa na nemansa, gabaki d'aya ya nemi nutsuwar sa ya rasa, yasani daganin yanda ya aiko kiransa shibe zoba akwai wata a k'asa, ada yana zuwa ya gaggasa masa maganganu amma  dukda shike zuwa kuma indai yana masarautar toyana bashi girmansa na zuwa ya gayar dashi kowace safiya, besani ba ko wani daga cikin mutanen da aka damk'e suke a hannun hukuma ya ambaci sunan sa acikin wa 'yanda sukeda hannu a cab'ewar al'amuran masarautar, gashi kuma labari ya riskeshi akan fitowar Takawa b'angaren daurama ba jimawa ta fad'i cikin ciwo, idan hakane akwai abinda ya sani game dasu tabbas, baze tab'a bari sunan mahaifiyar sa ya lalace ba da tsufanta da komai dole ne ya d'auki wani k'wak'waran mataki akan hakan, da yana da iko da wannan hatsibibiyar me shegen wayon matar ta Takawa ze hallaka har lahira sabida itace matsalar su kafin zuwanta Takawa a duk dabarun sa be aikatawa kansa komai ba seda tazo ta zama hankaka mayarda d'an wani naka, butulu me manta alkhairi ai shine yajago tanci d'aurin auren ta dukda yaso Takawan ya auri RALIYA,  a sukwane yake tafiya yana narka uban zufa hankalinsa duk a tashe bazaka tab'a cewa wannan ya tab'a zama saraki ba harya iso b'angaren na Takawa, shima dukda yake tare da fadawan sa da hadimai hakan be hanashi neman iso da kanshi ba, izinin shiga aka mai ya kutsa k'ai ciki da sallamar sa, a babban parlor na takawa ya sameshi yana zaune yanacin sabino d'an kampani da abinda ake cin dabinon tsinken roba, Gaisawa sukayi sosai kaman ya saba gayar da sarki Ra'uf matsayinsa na ubansa sannan ya kawar da kansa gefe d'aya cikin zullumi

"Ranka ya dad'e kadaiga yanda jikin Sarauniya daurama ya dawo yanda nakejima ta samu shanyewar b'arin jiki kuma ni hakan bemun ba ada so samune tamun bayani cikakke akan wanda sukeda hannu akan sacewar da akawa mahaifina dannifa bazan tab'a gafartawa wanda suka sanyashi acikin k'unciba na kusan shekaru 33, sekace a tatsuniyoyin da ace asace mutum baya ganin rana tsawon shekaru, ni'a ganina  yadace kaima kayi wani abin a k'alla d'an uwanka ne amma ka lafe kaman ba'ayi ba, yanda za'ayi da daurama nakeso ka gayamun, dankuwa ni harta soma bani labarin komai tiryan tiryan, sekuma tacemun jiri take gani shine fa nabata hutu har da washe gari to ashe ciwon kenan dan gatacen rai a hannun Allah, amma ko yanzu ni a nawa tsarin gobe da azahar zan koma wurinta tunda naga bakinta be samu matsalar komai ba" Cikin tashin ya kalleshi

"Kace harta soma yima zancen mutanen dake da saka hannu aciki da wanda suka sani, wa da wa tace maka"  kallon zargi ya masa yanaso ya k'ara tabbatar zarginsa a kansa kanyace

"Nifa harna soma mantawa amma wannan daine daka ga an kama, sedai tace dani akwai mutane uku dabata fad'a ba sune nakesan sanin kosuwaye kuma da ikon Allah gobe da azahar zanje da yardar Allah" zufa ce ta keto masa ya sanya hannunsa ya sharce cikin tashin hankali yace

"Ai Takawa wannan tafiyar dani za'ayita idan muka idar da sallan azahar semu wuce kai tsaye dan gwara muji bamuda gabbas akan rayuwarta" Murmushi takawa yae

"Kowama bashida tabbas akan tasa rayuwar, ko yanzu ko anjima ko gobe ko wane lokaci zamu iya mutuwa, fatan dai mu cika da kyau da imani amma ba wannan tunaninba, zaka iya komawa dma abinda yasa banzoba sabida naga maganace me buk'atar sirri aikasan danazo"

"Hakane Takawa shisa hankalina ma ya tashi na wanzo da gudun fanfalk'i" Murmushi yae kurun aranshi yace "Da sannu sannu dai" haka yamai sallama yfita cikin tashin hankali mara misaltuwa.

**********
    "Ni narasa yanda akayi Baby yanzu bakya d'aukin jin k'amshin jikina" murmushi tae me sanyi

"Ban isa na dena d'oki da begen k'amshin dake tashi daga jikin kaba Takawa, kaime sanyine, k'amshin kama haka, komai naka ina sanshi, yanayine na laulayi cikin yana girma abubuwan suna raguwa amma in fad'ama gaskia tun kafin zuwan wannan cikin k'amshinka abinda nake matuk'ar sone sama da komai, tun farkon ganina dakai nafi tsawon sati ina fama da begen yanayin k'amshin jikinka har akayi tsawon inajin k'amshin naka a hancina, in gayama gaskia a wannan lokacin ina cikin tsananin damuwar rashin muh'd amma wayana dana baka rik'o rannan ita ta zama abun d'ebemun kewar k'amshinka har zuwa sanda iska ta gama kwasar sa tai gaba dashi, nayita zuwa yawon nemanshi a gun siyarda turaruka amma bana samu sam, so tari kuma dana aureka nikan saci naka in saka ajikina amma daga bisani sena fahimci ba turaren bane yake sanya ka k'amshi kaine da kanka kake da k'amshin dake k'amsashen turaren, kadena wata tantama dan harna komawa mahaliccina k'mashin ka da komai naka dakai kanka kune abun sona" K'ura mata ido yae har sanda takai k'arshen zancenta, wani narkewa yakeji zuciyar sa tanayi akan meenaly, besan yanda akayiba yafison kalamanta fiye da sauraran komai aduniya banda alk'ur ani me girma, wata duniyar yake tsintar kansa aduk sanda take gayamai ire iren wa d'an nan kalaman, seda ya mayar da nauyin kansa a gefen wuyansa ta hagu sannan yace

"Meenly ina sanki kinji, inason komai daze fito daga gareki, tafiyarki, maganarki, amon sautin zancenki, nutsuwar zancenki, hankalin zancenki, kyawun fuskar ki,kyawun surarki d'abi'unki, mu'amalarki k'amshin ki,murmushin ki komai ma idan dai nakine ina sonshi fiye da yanda nakeson kaina" Kwantar da kanta tae asaman kafad'arsa ta dama

"Banida Buri a duniya daya wuce na sanyaka a farin ciki me d'orewa, bana fatan dena numfashi harse na sanyaka farin ciki na har abada, kaine kurun abinda nake gani na ganu, nake ji na ganu, nakejin maganar ka na tabbatar naji, nake jin k'amshin ya dulmiyar dani, nake rab'ar jikinsa na tsumu, kaine kake bayyanar da hasken walk'iya acikin duhun daya mamaye ruhina, kaine kake wanzar da farin ciki a ruhina aduk sanda wani abu akasinsa yae k'awanya da rayuwata, kai kad'aine nake gani inji sanyi kai kad'aine Takawa na nake gani inji banason kamun nisa, kaine kawai ba wani sekai nakeji kaman in d'aura hannu aka in xunduma ihu idan kamun nisa koda na wuccin gadi ne, ban saniba ko dama cen kaine, ban saniba ko dama cen ajiyar takace abu d'aya zan gaya maka shine ina k'aunar ka fiye da yanda uwa ke k'aunar jinjirin yaro sabon haihuwa, ina maka so fiyeda yanda kake tunani ina maka so adadin taurarin dake haske sararin samaniya idan zasu irgu" k'ank'ameta yae yana jin wasu k'walla suna tarar masa tsabar tsumashin da kalamanta keyi, wani irin k'aunar ta ke ratsashi aduk sanda  take zuzutamai kalamanta masu mantar dashi waye shi, ba abinda yskeso sama daya kasance tare da ita

"Ni masan nafi sanki akan san dakike mun, sabida baki tab'a cewa kina mafarki naba" d'ago kanta tae dukda ta fuskanci zolayar ta ykeyi

"Mafarkinka har ido a bud'e nakeyi, kaine kake mafarki na a yayin dakake bacci niko girki nake mafarkinka nake" Girgiza kanshi yae yana dariya

"Idan gaske ne ki sunbaceni a nan" ya nuna lips d'insa da d'an yatsan sa.. Kawar da kanta tae gefe d'aya tana murmushi cikeda kunya

"Idan zaki fad'i magana kin iya fad'a kanki tsaye amma idan zaki aikata seki wani noqe, acikin duhu kin iya kamawa ki kusa ciren lips d'ina a haske rana sekuma ki waske nifa banason wayon nan" Mik'ewa tayi tana murmushi

"Nidai bazakayi wannan daniba" Kishingid'a yae yace

"Hajiya wai kinga qaton tunbinki, anya kuwa basui kuskure ba, da alama yaran cikin nan biyune" murmushi tae

"Kanka akeji alaji, katashi kayi wanka dai" be kulataba wayanshi ya k'ara, d'agawa yae tare da sallama

"Kazo asibiti yanzu, anzo anwa Sarauniya Daurama yankan rago acikin asibiti cikin daren jiya yanzu aka wayi gari da wannan" zabura yae yana ambatar sunan Allah abakinsa, kallon agogo yae k'arfe shida da rabi na safe dama idar da sallan su kenan suka hau surutu shida madam, kallon shi tae ta matso da sauri

"Lapia dai Abu Haidar wani abinne ya faru?" Cikin sanyin jiki ya zare wayar daga kunnen sa

"Zuwa sukayi suka kashe daurama, kisan wulak'anci wai yankan rago suka mata, sabida akwai abinda na fahimta nayi magana shine abun yazo da kisa haka, sabon salo kenan fa Meenaly" Cikintane ya juya mata, bata zata cutar dason duniyar yakai musu haka ba, dafe cikin tae takai zaune tana ambatar sunan Allah cikin rud'u, rik'eta

"Lapia dai?" Murmushi tae

"Shock ne kawai fa, amma garau nake ai kanamun adu'a kuma inayi so karka damu kaji nawan" ta k'arashe maganar tana kallonsa tare da d'age mai gira d'aya, dukda yana cikin damuwa seda ya murmusa kanya juya zuwa waje yana fad'ar

"Ina zuwa"

Mom Nu'aiym.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now