27

3.2K 292 26
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad @ 68billygaladanchi
     
     27

Tsaye ya mik'ar da ita ya sake zabga mata marin daya haifar mata da soma yin hab'o kai tsaye jinin hancinta ya soma zubowa, kuka takeyi tana magiya amma ina basu saurareta ba

"Oga mu yanke harshen mana da yatsun muyi mubar nannpart d'in kar wani farka" tsaki yaja

"Wanda duk ya farka sena kasheshi, kumama maganin baze baiwa kowa damar tashiba se nan da awa sha biyar, ko yanzu kuma sunada awowi 11" D'an kwab'e fuska d'ayan yae 

"Oga to yanzu me zakayi?" Hararar sa yae

"Bakinta zaka d'auremun biyu suja kaf'a biyu suja hannayenta banson gaddamaa zan hau tane" Kallon sa

"Kana ganin oga wannan baze mata lokaci ba?" Cikin hargagi yae ihun daya farkar da Hidar Dake sama ya tashi ya lek'o, Tsoro ne ya kamashi dukda zamansa yaro ya koma sama ya lafe kurun....

**********
   Ihun da ogan yae ne ya mayar da hankalin sojan da Takawa yasaka zagayar part d'in na meenal cikin dare, dukda banan yake kwana ba amma yana zagayawa duk bayan d'aya seya koma part d'in takawa dase yayi tafiyar mns ma ze isa da k'afa dai, yazo zagaye an our ago yaga sunada barci amma seya koma ganin babu suspicious abu, yanzu time na dawowa ne yae.

  Baya yaja kad'an ya zaro wayarsa yakira ogansa

"Akwai matsala apart na Madam, kuzo da yawa", da sand'a shi kuma yashiga gidan bayan ya sanar dasu insunzo sushigo yana ciki, sojoji bakwai ne suka taso gaba d'ayansu zuwa wurin part d'in da gudun su, Kai tsaye ciki suka afka adaidai lokacin da suke rirriqeta suna shirin zare kayan jikinta, babu ruwan soja kai tsaye suka harbe hud'u daga cikinsu, dama kuma su basuda bundiga se makamai kurun, Suka daddam k'e sauran suka doma dukansu suna shurinsu da takalmin su masu shegen nauyin nan, duniya ba imani mazaje sunkai goma dukdan a cutar da mace d'aya! Daganan suka soma musu bayani, Meenal se hak'i takeyi tana mayar da numfarfashi, da hannu ta nuna musu sama, takasa magaba k'wak'wara, sojan ne yaje yasoma duddubawa bega komai ba, ana haka Hidar ya leqo daga sama, aikam ya sakko dashi ya soma rarrashinsa danyaga yana kuka, d'aure sauran b'arayin sukayi sannan suka nemi taimakon Madam, ita da kanta ta ciro Small meenal dukda sarawan da kanta keyi, sunso zuwa dasu part d'in oga amma akwai tafiya gashi darene, sun sani tabbas Meenal bazata iya tafiya ba kuma su bada mota suke ba, dole aka barta da sojoji guda biyu sauran suka juya donsu tado ogansu yazo yaga 'yan ta'addan da aka kama.
 
   Takawa yana bacci yajiyo knocking nasu yasha mamakin knocking cikin dare haka, haka yaje toilet yadan yi freshin up cikin wannan izzar yafito da singlet da gajeran wandonsa, Michael ne yace muryan sa yana rawa

"Oga ansmu wasu b'arayi sunje part d'in Madam har suna qoqarin suyi rape nta sanda mukaje..." Kanya k'arasama ya bankeshi aguje zuwa part d'in nata da k'afarsa...

Cikin gidan ya afka tare dasu dasuka rufa masa baya da gudu cikin daren, kutsawa yae har cikin d'akin nata, acen yaganta itada yara ta ruqumqumesu tana kuka mara sauti, jini harya kwanta mata a idan nan, fuskar ta kumbura tayi wani iri, ga jinin hancinta har yanzu be tsaya ba se zuba yakeyi, dama yaran duk qaran bundiga ya tashesu basu bama har sauran part sunji wannan k'arar bundigar kowa dai ya lafe ne sabida tsaro.... Kansu yae ganin yaransa lapia lau ya lalubo wayarsa yake sanarwa amo had'e cewa zasu rako yaran yanzu, taso ya turo mata har Meenal amma yace noo ta barta ze kula da ita.

   Seda yaje yawa sojojin warning akan suje su binne wanda suka harba kuma su b'oye masa wanda suka kama batare da kowa ya saniba acikin masarautar ba, seya gama bincike tukunna" sannan ya dawo wurinta se kuka takeyi, har lokacin kuma k'walla be dena ambaliya daga idanta ba, ga jini duk ya b'ata mata jikinta wanda ya zubo daga hancinta, Toilet yaje ya tara ruwan d'umi sannan yazo ya zare rigar jikinta a hankali ya d'aura mata towel, itadai yaukam jitake bazata iya k'ara kwana d'aya a wannan masarautar ba, ta zubar da makaman yaqinta gun mommy da daddy zataje,  a tsorace take dankuwa wannan mugun anufinsa wannan k'atuwar abar ze tura mata, to ina? Kuma wai da gaske da cire 'yan yatsun nata zasuyi? Sautin kukan ta ta k'ara tunawa da masifar data  jefa kanta aciki, shikuma gogan komai bece da itaba har suka je ban d'akin, a ruwan ya zuba ta ta runtse idanta, haka seda ya mata, wanka sosai ya gaggasa mata fuskar nan,,D'aki ya kawo ta yaje ya d'akko wasu ruwan zafi da small towel ya gaggasa mata fuskar nan data kumbura, da k'ank'ara ya gasa mata idanta sannan ya gyara komai bayan yabar security a wajen har lokcin kuyangin suna bacci da bayi, sannan ya dawo ya rufe gidan da k'ofar d'akin zuciyar sa babu dad'i, zare singlet d'inshi yae yadawo iya boxers ne ajikin sa, batare daya sanya mata wasu kayan ba kota saka ya shige acikin duvet shida ita kansu ne kurun  waje, sumar kanta ya soma shafa a hankali bayan ya turata gaba d'aya ajikinsa hannunsa ya mik'ar ya d'aura mata kanta akai, cikin taushin murya yace

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now