page 51

4K 295 47
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

51

Kai tsaye asibitin ya nufa, acen ya tarar su Gimbiya sailuba sunata rusa uban kuka da sauran yaranta, kai tsaye wurin da akace gawar tana nan yaje, cikin sanyin jiki ya yaye farin k'yallen da aka rufe fuskarta dashi, cikin tashin hankali yaja ya rufe tare kawar da kansa, besan sanda ya soma zubar da hawaye ba tsananin tausayin tsohuwar yana kwatanto kalan azabar datasha a wannan mugun yankan kafin mutuwar ta wannan wane irin rashin imani ne haka? Meta musu yaji ita me laifi ce amma komai lalacewarta uwar ubansa ce ko sunaso ko basaso, baro d'akin yae a daidai sanda me martaba ya k'araso shime cikeda tashin hankali, gayar dashi yae yana me share k'wallan daya zubo masa bega amfanin irin wannan mugun abunba, dafa kafad'arsa me martaba yae yace

"Kayi hak'uri takawa, Me mulki baya haka sam, kazama jajirtacce lallai wannan aikin wasu mugwayen mak'iyan mune sukayishi" Rausayar da kanshi yae gefe d'aya batare dayace k'ala ba, ya wuce waje kawai inda ya bar su sailuba haka yazo ya tarar dasu tsaye sunata kuka, matsawa yae kusa da ita yace

"Haba Aunty idan kina haka sauran k'annenki su suce me, yanzu adu'arku kurun take so banda wannan ba komai" kallon tsana ta wurgo masa

"Koda fansa kakeso ka d'auka Mu'az bata wannan hanyan ya dace ka d'auka ba, kaduba kagani fa azabar yanka koda yatsanka aka yanka bare a raba gangar jikinka da kanka sukutum, menene laifin ta dazata cancanci kisa na wulak'anci irin haka, ai munada kotun shari'a anan, be dace ace ka d'auki hukuncin yin ramuwar gayya irin hakaba, bazan tab'a yafe maka ba har abada" kallon mamaki ya bita dashi

"Me kenan kikeso kice Anty sailuba? Kenan nine na kashe kakata, to angaya muku kowama zuciyar sa irin takuce? Kokuma so kike a baynar jama'a ki fad'i mugun aikin data aikata, kinfi kowa sanin ni banida zuciyar kisa amma da sannu zan lalubo wanda ya kasheta ke kuma in makaki kotu na zargina da kikai ba bisa hujja ba" kallon takaici tamasa amma ta gagara furta wata kalmar haka sukai jugum jugum har sanda aka kammala bincike aka nemi yi mata wanka a mata sutura akaita gidanta na gaskia....

********
Jikinsa a sanyaye yashigo gidan sam be kawo aranshi ace shi bane yae kisan, lallai babu yadda kenan azukatan junansu akan su, kowa gani yake kamar dan uwansa ze iya hallakar dashi akan mulkin banza, tana zaune kanta yana juya mata yazo ya kwanta ya d'aura kansa a saman cinyarta ya juyo yana fuskantar ta

"Meenaly ina cikin damuwa na rud'e na rasa tunanina da nutsuwa ta, ki taimakamun da mafita kinji" kallon sabtae cikin tausayawa kafin takai hannunta saman kanshi

"Kayi hakuri ka sanar dani menene komai a dunk'ule yake aguna" murmushin takaici yae

"Su Anty sailuba gani suke kamar nine na kashe daurama" kallon mamaki ta masa

"To akan me su rasa wanda zasu zarga se kai kad'ai,meye hujjar su ta fad'an wannan maganar?" D'ayan hannuntabya kamo sannan ya mata bayanin meya faru shida antyn dakuma yanda yae da Sarki Ra'uf jiya" nisawa tae sannan tad'anyi shiru na kusan mintuna uku tana nazarin abinda ya sanar mata, harya cire ran zatace wani abin ya tsinkayi muryar ta tana magana

"Wannan banaji yana daga cikin abubuwan dakai yakamata su dameka, damuwa d'aya ce anan yanda zamu b'ullowa al'amarin amma inaga ai wannan ma yanada sauqi fassarawa a guna, kwanakin baya akwai wani audio danayita so na baka se hankalina ya d'auku bansan dalilin dayasa na manta ba sam, zan duba maka a phone d'ina dana dena amfani dashi amma bari in maka fashin baqi akan wannan al'amarin based on d audio dana saurara

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now