page 44

4.5K 346 65
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

  Wattpad @ 68billygaladanchi.

                 44

Har suka isa masauki be k'arayin mata magana ba itama kuma haka, seda suka isa d'akin suka zauna sannan ta kallleshi

"Abu Hidar kace zaka kaini gunsu mom sekuma na ganmu anan?" Hancinta yaja

"Kisa rantsuwa kema bakifi son nan akan cen ba?" Rufe fuskar ta tae da tafukan hannayenta

"Allah ni inaso inga mom" Janyota yae jikin k'irjinsa

"To maza sanya hijab d'inki kizo muje na miyar dake gun mom" Kallon agogon hannunta tae

"Noo yanzu after 11 gobe da safe dai semuje ko" d'agata yae gabad'aya ya shiga zagayar d'akin da ita, dariya tashigayi ba k'akk'autawa, ita mamakin sa sosai takeyi wasu lokutan, yanzu yanzu zakagan shi fuska ba annuri yanzu yanzu kuma zakaga ya washe kaman ba shiba, seda ya gaji ya direta akan gadon yana shima ya kwanta yana mayar da numfarfashi

"Yarinya karki zama k'atuwa fa wannan nauyin haka, idan har kika k'ara bazan miki doki ba" Murmushi kurun tayi, Daganan kuma zance ya sauya suka shiga yin hidimar d'ebewa juna kewa, mu'az be gushe ba sedabya tabbatar ya saukarwa matarshi gajiyar daya tara mata, yau taji sauk'i kam ba laifi tayi garau da ita, seda ya tabbatar ya kimtsa ta da kanshi, taci ta k'oshi sannan suka kwanta b'acci, yau sun kasance cikin farin ciki dukkansu, meenal Anci kaza da me siyan kazar kuma anyi baccin dad'i.

**********
    Yauma kamar kullum toshe da hanci takecin chips d'in da plantain dukda bawani k'amshin dabanne dasu ba amma dazaran ta bari k'amshin ya haye mata kai toko tabbas setaga haza dan duk seta harar da abinda taci, kallonta yakeyi cikeda tausayi shidai ciki ba abinda baya zuwa dashi, ita kuma kalar nata laulayin kenan salma ba haka tayi ba sam duka haihuwar ta uku, ko wanne da salon sa amma bame wahala kamar Meenal, yakula cikin ma zallar sha'awa yake sanya mata, baiwar Allah gashi bata ma gama sanin kan abinba, sedabta gama cin abinci sannan ta kalleshi tana janye Pack d'in, murmushi ya sakar mata tace

"Kallon na miye?" Hannunta ya kamo

"Na kwad'ayi ne" batace masa komai ba se murmushin dai, seda ta wanke hannunta da bakinta sannan ta dawo ta nutsu yanayin sa ya nuna mata tsaf magana yake so suyi

"Meenaly zanje masarauta tare da Abbana da ummiena da yaranki, zamuje ne muyi gabatar da Abba amatsayin wanda ya b'ata kuma muka ganshi daga baya koda yake bazamu wa kowa wannan maganar ba ta yanda aka sameshi kamar dai yanda na gaya miki jiya, yin baya baya ko b'oyo akan abubuwa baze tab'a bamu nasara akan mak'iyan mu ba, harga Allah naso naje dake kema masarauta amma kuma ina tsoron kar wani abun cutarwa yazo miki, sabida haka na yanke shawarar ki zauna abinki agida gunsu mom,zan baki tsaro me yawa inshaa Allah kafin na tafi" kallon sa takeyi tunda ya fara magana seda taji yayi shiru alamar ya gama sannan tace

"Su Hidar, fa baka tsoron wani abu ya same su?" Murmushi yae

"To ai suma dan dole sesun je ne meenal, yanada kyau kowa nawa ya hallara"

"Niba koman ka bace kenan Takawa, rashin son da kakemun haryakai ace kana wareni acikin kowa naka? Kokana manta cewar nid'in nan matar ka ce ta sunna inada dukkan hakk'in daya dace akanka, awurina nidakai ya dace ace mu gudu tare mu kuma tsira tare" Nisawa yae

"Karkice haka meenaly meyakawo zancen rashin so, nida bakina nace dake bana sonki, kinga ke kinada juna biyu ga cikin yanzu ne ma ya shiga satinsa na farko acikin watanni uku ko fad'uwar gaba ma wani abinne bamusan mezeje yazo ba koda bama fatan komai se Alheri" Turo bakinta tae cikin takaici

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now