page 23

2.7K 285 20
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad @ 68billygaladanchi.

23

Lafiyayyen mari Sarauniya hassy ta dire akan kuncen malmo

"Dana baku abincin kukai shine kukaje kuka sanya guba aciki, wato meenal d'ince ta gaya muku hakan zakuyi ko? Tun yaushe kuke a masarautar nan da har zaku zab'i bare 'yar talakawa ku cutar da Takawa" Jikin Malmo na rawa itada Me sulhu suka hau rantse dan kuwa sune manya acikin kuyangin

"Wlhy Tallahi Ranki ya dad'e babu wani abunda Sawun Takawa ta bamu muka zuba a abincin, hasalima ita batasan da zancen abincin ba" k'afarta ta sanya ta shure Malmo

"Karki mayar dani k'ank'anuwar yarinya mana?, to idan ba Sawun Takawar ba waye ya baku izzinin saka gubar?" Me Sulhu ce ta karb'e zancen dace wa

"Allah ya taimaki sarauniya Wlhy nidai bansan komai ba, tun safe yau dai suketa k'usk'us itada malmo mu dama ba'a bari muke isa d'akin Sawun Takawa gyaranshi ma malmo ce keyi, sabida haka sedai ko ita aka saka, dan kuwa jiyama munje B'angaren Takawar akace damu wai Sawun sa ta masa girki ya bayar kyauta, ranki ya dad'e kuma wa 'yanda ya baiwa se suka baiwa kuliya, tanaci anan ta shure basu dai fad'a bane ba sabida gudun abinda kaje kazo, watak'in ganin batayi masara ba jiya shine yau ta b'ullo ta wannan hanyar" Wani murmushi Sarauniya tayi

"Lallai asirin Sawun takawa ya tonu, haba mana take ta cemun wai itafa bazataci abinci ba idan ankai ashe da biyu tayi" Raliya dake tsaye tana yatsina fuska itaga 'yar sarki tace cikeda izza

"Naji ance taci abincin sabida yaga asirinta ze tonu she's acting smart to prove her innocence, kuma ni na tabbtar itne tayi abun, ke malmo ki gayamun Gaskiya in sparing life d'inki, itace ta baki ki zuba?" Jikin Malmo se rawa yakeyi cikinta ya d'uri ruwa muryar ta na had'ewa da yawu da majina ta furta

"Inaga sedai bayan da aka kai aka ajie kanya shiga ta zuba amma wlhy tallahi nidai bata bani ba komai in zuba a abincin ba" Dama mafita suke nema dan haka sukace

"Tabbas da hannunta ta zuba d'in kuwa sabida nina tabbatr dan taga ya kamata ne take acting banza 'yar talakawa, shi kuma tunda yafita da gawarta tun daren jiya be dawoba, soko Allah yasa y gane gaskiya" Juyawa sarauniya tayi tana sanya murmushi akan face d'inta, koda takawa be mutuba aidai zasuyi Nasarar rabashi da Meenal na har abada.

*************
Dafe da kanshi yake yama rasa wane tunani zeyi, duniyar sa abar tausayi ce, rayuwarsa duhu yake gani tuni, waze yarda dashi? Mecece mafita agareshi? Yazamana rayuwar sa kenan ba komai aciki se fitina? Ya kasance kenan bashida wurin b'uya se lallai an kashe shi? Meyayiwa mutane ne arayuwa? Ina yaga hanyar bi yaga haske? Akan sarauta zasu tsaneshi? Akan abinda gadon abunsa yae zasu nuna mai iya karsa? Akan hakane shida iyalansa basu da zaman lafiya? Meyawa mutane ne? Tunaninsa ya tsaya cak, kwata kwata jijiyar dake harba saqonni zuwa kwalwar sa ta dena aiki ta tsaya cak!!! Hankalinsa ya tashi ainun, yanzu kwanansa d'aya da ita a sibitin amma har yanzu likitoci basu ce dashi komai ba, yayi tambayar yayi tambayar amma a banza, ya rasa sukuni gashi yau ko d'an kukan dayake lab'ewa yae ya gagara zuwar masa Banda Umminsa babu wanda ya kula y kirasa yaji ya ake ciki, gashi shi kuma y gagara kiran iyayen Meenal, yana nan zaune har wani Dr. Yazo kusa dashi

"Yallab'ai muna buk'atar yin magana dakai" D'agowa yae daga duk'en dayake ya k'ura masa ido kurun batare daya ce komai ba, seda likitn ya k'ara cewa

"Yalla6ai kai muke saurare" mik'ewa yae cikin mutuwar jiki yabi bayan sa har zuwa ofishing babban consultant nasu, kujera suka nuna masa ya zauna akai sannan ya kallesa ya bashi hannu sukai musabiha Dr. Dayake ba indiye ne ya tattare nutsuwarsa ya had'e hannayensa duka biyu gu d'aya ya d'aurasu asaman hab'arsa yace

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Kde žijí příběhy. Začni objevovat