43

3.4K 329 34
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad 68billygaladanchi

       43

Bekosan wainar da akae tonawa ba, abokin tafiya ne ya kirashi a waya bayan yaga tafita da k'afa, dama yae wlcm back da wannan ma ya samu daman kiran Abokin tafiya dayike duka contact nashi suna nan acikin gmail nashi, Ringing wayar tayi harta yanke bejiba, se karo na biyu ya d'agota cikeda baccin daya masa nauyi, tsaki yaja ganin Abokin tafiya ne, ya k'ara kifar da wayar kurin batare daya d'aga ba, ganin hakan baze yiyu ba ya sanyashi bin bayanta, yana kallo tahau adaidaita da wannan yabi bayanta. Yana cikin tashan sanda tahau motar abuja kuma lokacin saura mutum biyu yana zaune a motarsa har suka cika suka tashi har lokacin yana k'ok'arin kiran Takawa amma baya d'agawa, dafe kanshi yae tunda yake yaga layin abuja tahau mota kuma motar abuja ce watak'il Takawan yasan da tafiyar amma kuma ze bari tahau motar kasuwa ne? Ya tambayi kanshi, watak'il kuma b'adda kama yakeso tayi shisa, da wannan tunanin shima ya koma masauki yaci gaba da sabgogin sa, Takawa be farka ba se 11, sannan kuma wankansa kurun yayi 40 mns, yasha  mamakin rashin ganin ta, amma tunawa da yae jiya ma ta fita ya sanya yae tunanin tafita ne ta siyo wani abun, order abincin yae yaci, bashi yabar d'akin ba se wuraren 1 bayan yayi alwala yafita domin gabatar da salla yakuma fita, a reception yabar key akan idan tashigo abata, haka yashiga sabgoginsa bayan idar da salla,abokin tafiya yanaso ya masa maganar ta amma seyaga tunda har aka d'auki wannan lokacin be tambayeta ba tokuwa tabbas yasan da zancen tafiyar da wannan ya gimtse bakinsa kurun sabida ko maganar msd col d'inma takawa be masa ba.

***********
   Tunda taje gidan Al-Ameen tak'i tayi magana, banda kuka babu abinda takewa matar sa, gashi baya gari kwata kwata,  maman humaira (matar Al-ameen) tashiga tashin hankali matuk'a, ga wayar gogan akashe, da k'yar ta lallab'a Meenal d'in take d'an tsakura mata dangane da alk'awarin dashi Takawan ya mata na saki sannan kuma ita bazata zauna dashiba danba sonta yake ba" Nisawa Maman humaira tai

"Waike meenal mesa bakyaji ne? Har se yaushe zaki san ciwon kanki, ke yanzu tsabar bakida hankali seki zubar da cikin ki akan wani shirmen mijinki baya sonki, ina ke kina sonsa?" Kallon ta tayi ta k'ara turo baki

"Yo anty dan ina sansa seya rik'amun wulak'anci?, yoko ina sansa ai zan iya hak'ura da shi tunda na hakura da yaa muh'd niba namijin daya kaimun dole" Murmushin takaici tayi

"Yanzu gayamun fushin menene ya kawoki nan gidan batare da izinin mijinki ba?" Share k'wallan daya zubo mata  tayi sannan cikin kunya tace

"Anty fa kullum dan yaga k'amshin jikinsa nakeso seya rik'a guduna, kuma seya zo ya dinga mun abubuwan iskanci seyaga nazo inaso, bazan iya hak'ura ba seya tashi ya k'yaleni kuma marana ya murd'emun bana ma iya tsayuwa yae fuska kaman be gani ba tsabar mugunta, jiya ma cemun yae wai idan bazan dena zancen zubda cikin ba haka zeyita horani, jiya shine naga zan mutu abanza sena tahowata inda baze ganni ba sam" Murmushi maman humaira tayi

"Gaskia nan kam yanada laifi anan, sam shikuwa ba'a yiwa mace haka musamman me ciki, wannan kawai aiseya b'arar da cikin kiyi hak'uri wasu mazan suna sani suke maka abu dan kawai suga k'arshen ka, kema kinyi kuskure mune muke d'aukar ciki musha wahalar shi irin wannan wahalar dakikesha yanzu komafi amma zakiga mazan wani zubin harse su fimu son 'ya'yan gani yake kamar k'arshen k'iyayya kenan ki nuna masa bakya buk'atar wani jini a tsakanin ku yazo duniya shiyasa nake ga yake miki horo irin wannan"  Sadda kanta tayi a k'asa zuciyar ta tana mata suya

"Nito bazan bari ma yasan ina nan d'in ba, kosu mom bazasu san inda nake ba, seya musu bayanin cewar latsani yakeyi na gudu dan kar ya kasheni" Dariya Maman humaira tae

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now