page 4

3.1K 267 7
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                        04
Muhammad yana cikin tsananin tashin hankalin jin cewan Athsma dayakeda  ita tanaso ta masa illa a huhunsa koma tayi, acewar likitan wani sashe daga cikin huhunsa na dama ya soma lalacewa, wanda wannan case ne dabe cika yawaba, sedai ko su bashi magani idan anyi sa'a ze warke, besan waze gayawa ba yanaso ya gayawa meenal amma ina fuska, zance ma idan zezo gunta seya daddage ya cire tsoro da had'iyar hak'uri......

    Shiru suke acikin motan tamkar wasu kurame, bamewa wani magana acikinsu, shi muhammad damuwar ciwonsa ya isheshi beso ya sanar da iyayen sa su tashi hankulansu, yakuma rasa waze sanar wa, likitan sa ya sanar masa maganin beyiba seyaje india, dukda yake abinda yakeji ajikinsa yafi qarfin tunanin sa yana gani tamkar bashida rabon yin rayuwa me tsayi amma haka yake shirya musu yin tafiyar shida Meenal sati biyu bayan an kaita gidansa tubda yake auren saura sati uku, kuma sun kammala jarabawar hutun zango na biyu a wannan lokacin, yana so ya sanar mata akan ciwon sa amma besan ta ina ze soma bama....

"My meenah, bayan sati biyu da tariyarki zamuje india fa, daddy yasan da maganar ma so komai na tafiyar mu yana kusan kammala inshaa Allah" kallon sa tayi ta yamutsa fuska

"Ina zamuje? Kace india haba mana yaa moh mesa kakemun haka ne wai, yo indiyawa dake shegun talakawa ba gwara munje wata qasar ba ko Uk haka ko America ko china amma tsabaragen tsiya murasa inda zamuje yawo se india haba mana" kallo ya callarowa fuskar ta

"Idan na fahimceki nufi kike ban gwanince ba ban kuma burge duniya ba idan naje india hutu, kokuma ke ban burgeki ba, zuwa yanzu ya kamata ki gane wani abu guda d'aya nifa komai nawa a cikin tsanaki nake yinsa bakuma na garwaya tsaftattacen tunani na da gurb'ataccen tunanin wanina danake yaqinin akwai tabon rashin jaraba imani a lamuransu, ki kula nifa tsarina dabanne da tsarin masu tirsasa rayuwar waninsu koda basu kai wannan k'arfin ba....kalmar tsiya kalma ce dake cure da tarin ma'anoni marasa dad'i ciki kuwa hadda girman kai dake hanaka shigewa Aljannar firdausi, yazama sabonki na barin furta wannan kalmar wa koda mak'iyinki ne" Cingom dake bakinta tad'an tauna

"Dazaka tanadarwa gabanin yanzu wa 'yannan kalaman naka, zuwa gaba ko nan da anjima zaka amfana dasu, na tabbatar zakayi tozali da mutane kamar kai, seka rarraba musu murd'add'un kalamanka danni kam bana gane kaso goma acikin kaso d'ari na murd'add'un kalamanka sekace wani bafaden sarakunan wani lokaci cen baya me yawa daya shud'e" Wani murmushi yai mata daya tsaya iya lab'b'an sa yace

"Zamana tare dake a 'yan tsakanin nan na fahimci zama da me d'aukan kanwa ya sanya kanki kema yayi fari, kalamanki sun soma kaman ceceniya dana matar da mijinta yake bafade acikin fadan daya shallake tafiyan lokaci acikin lokutan dasuka gabaci kakannin dasuka haife iyayen iyayen rai biyu dake acikin motar nan, wannan kad'ai ya isa ya nunan tabbas murd'add'un kalamai na sun soma tasiri akanki danake kyautata zaton munkusa raba daidai akan su" k'ura masa idon ta tai, muhammad yana sha'anin sane kurun sabida yaganta haka, yadinga zaginta kenan acikin baud'add'iyar hausar sa dabata ganewa yake zaginta akan banza da wofi............

"Amma dai kasan duk wanda yai zagi a kasuwa ai yasan da wanda yake ko?" Murmushi yae

"Yanzu me kike so ayi akan sha'anin bikin nan" K'wafa tai

"Meko nakeso ai kud'i zaka bani akan kamun dazanyi se dinner kuma harnayi magana dame decor 2.5m zata mana, amma acikin nan gidan zamuyi ta filin baya....idon sa ya k'ura mata na 'yan mintuna

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now