page 30

3.5K 300 20
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattoad 68billygaladanchi.

*Assalamu Alaikum, Fan's please kuyi hakuri, bazan iya baku book d'innan daga farko ba gaskia, idan nace zan rik'a bayarwa wlhy abubuwan zasu mun yawa, karkuga kamar ina muku wulak'ancine wlhy ba haka bane, idan babu ku wanakewa rubutun, amma dukda haka abubuwan sunmun yawa dama kuma nayi alqawarin ana kaiwa 30 nadena baiwa kowa daga page 1 gaskia, sabida haka kuje wattpad zaku samu complete acen, nagode.*

     30

Zaune take acikin parlor tana tunanin yanda za'ayi taje yawo, itafa harga Allah bata wani zo da kayan taba, kuma ta iya dubai kamar me basuda wurin zuwa hutu se nan, beside ta kwana biyu bata sauya waya, Allah sarki yaa Muhammad Allah yajik'ansa sanda yake raye kulum cikin rik'e manya manyan sababbin phones take bama d'aya ba amma wannan shakurundun banda shegen girman kai ba abinda ta iya, tunanintane ya d'auketa wani lokaci daya shude cen baya

"Mesa bakyasan wannan lace d'in my meena? Kokinsan customize one ne nida kaina na zana abuna na sanya aka miki irinshi ke kedai bakiga ba ko ina anzana Meenal wa Muh'd" Tsaki taja masa a wancen lokacin

"Dama bakamun kaud'i da mugun iyayi bane, kace a saka Meenal kawai banda shirmen sunan ka, amma ni ya xan sanya abu me sunana da naka" murmushi ya sakar mata

"Bana fatar ranar da zakiyi danasanin k'iyayyar dakike nunamun a sarari meenal, shiysa bana kai abun a raina amma kisani inajin ciwo, kusan 350 lace d'innan yaci awurina amma shine ke kike kushewa dan kawai sunana ya fito ajiki" wurga masa lace d'in tayi a jikinsa

"Kaine matsiyaci Alhamdulillah dai ubana yamun wanda ya fishi lace d'inka kuma ka rik'e banaso" tae shigewarta cikin gida, abinda tafi tunawa ya bata haushi shine yanda ya bata hakuri yakuma ci gaba da adanar lace d'in hartaxo gidansa ya bata, haka tak'i d'inkawa, yasha cewa da ita

"My meena dan Allah ki d'inka lace d'innan inason inganki sanye dashi" haka harya komawa Allah bata d'inka ba  yanzu kam tayi alk'arin d'inkawa takuma saka idan har ta koma Niger. Gganin tunanin baze k'areta da komai ba se b'acin rai ya saka ta mik'ewa shigarta tae tsaf cikin riga dakuma wando rigar ta wuce cinya zuwa gwiwar ta irin kaftan top d'inna, kan nan yasha gyara aka tufkeshi a tsakiya sannan ta sanya mayafi qarami aka zagayeshi, toms ta saka a k'afarta ta kimtsa sosai sannan ta fice daga gidan zuwa yawonta, kwanan su biyu kenn amma bataga alamar yana shirin kaita yawo ba ita kuwa ta saba da yawon ta a dubai tasan gari.

Kai tsaye wani shope dasuke siyan dogwayen riguna ta wuce, acen ta bada a d'inka mata wasu k'waya biyar sannan ta wuce jewelry shop cenm ba laifi ta tsinta sabida duk tana buk'atarsu, siyayy dai tayi sosai sannan lastly ta siya zube me sunnan muhammad ta saka abunta ta kar6i jallabiyunta ta wuce, har inners seda ta siya, tun a k'ofar gidan k'irjinta ya doka bata tab'a zaton zataga fuskar Takawa haka ba, kai kodacen bata tab'a ganin fuskar sa a irin yanayin data gansa ba yanzu, tamkar wacce k'wai ya fashewa aciki haka ta tako da iyayen kaya se nishi take zuwa k'ofar gidan, ko k'ala bece mata ba, sauke kayan tayi wata kuyanga ta karb'a ta wuce zuwa d'akinta dashi...

"Sannu Takawa ina wuni" wani mugun kallo ya wurga mata daya sanyata had'iyar wasu yawu masu kaifin gaske, dan kuwa zasu yanka mak'oshi, wucewarta tayi ciki taje ta kwanta kurun tana mayar da numfarfashi sabida indai be mata masifa yanxu ba to bazeyiba din, kokuma dai yayi kad'an anjima, tana kwance ta lumshe idanta yashigo d'akin, jin motsinsa da k'amshin turaren sa sune suja tabbatar mata ya iso, mik'ewa tayi tsaye gaba d'aya ta d'an ja baya, itafa yau tsoro ma yake bata wlhy, bece komai ba ya soma zazzage kayan data sissiyo, haka yaeta tonesu haryakai ga sabuwar wayar data siya acikin kwalinta, watace me tsadar gaske, ranshine ya b'aci idan tanason waya base ta masa magana ba meye na zuwa ta siyo kaya hadda waya, kodan be siya mata kayan lefe ba take masa haka? Wai akan me ma zata fita bata gaya masa ba? Wai ita tasan gari, ball yae da kwallin wayar, ita kuwa taja baya zuwa jikin bango, bata tab'a ganin Takawa acikin b'acin rai makamancin na yau ba, dama haka yake zuciya?, jikinta har rawa yakeyi dama kuma Meenal duk iyashegenta akwai tsoron duka, cika baki kam sune agaba amma duka bata had'a komai dashi ba, kowa ya sani ko secondry scool nasu ansanta da tsokana amma bata bari a tab'a lafiyar jikinta, batasan mesa yake mata haka ba, kullum idan yae fushi seya yae kaman ze daketa harga Allah tana tsoron yanayin mutumin nan wasu lokutan, seya murd'e tamkar bashiba idan kuma yaso wasar sekiga yana abu tamkar wanda be tab'a shiga rigar mulki ba, takowa yae har inda take ya sanya hannayensa duka biyu ya dafe ginin datake jiki, yace cikin murya k'asa k'asa amma da magana me kaushi

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now