page 5

2.9K 293 14
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                  05
Haka ta zauna wurin jugum jugum se kiran 'yan gidansu takeyi da kuma maman shi tana cewa su masa adu'a...mahaifiyarsa makam se a sannan tasan cewan baida lafiya, koda yake tasani amma bata zata abin yakai cenba dukda yake ta kula sosai baya cikin walwalar sa kuma yana rama a tsaitsaye, adu'a suka duk'ufa yi har Meenal d'in wacce duk tagama firgicewa....sa'o'i kusan goma sha biyu akayi ana gudanar da aikin kasancewar case ne wanda basu saba gani ko sanin irin saba, Sanyine ya tab'a masa huhunsa abin mamaki kuma yaketa dagargajewa, yana matuk'ar ban tausayi, sunsha mamakin ganin yanda yaketa kumbura ma, da k'yar da yardar Allah suka daidaita inda zasu iya d'in kannan aka sallame wannan aikin....

    Tunda aka fito dashi daga aikin be farfad'o ba har kusan sa'o'i sha biyar, hakan ce ta sanya suka mik'ashi ICU inda ze samu wadatacciyar kulawa me ma'ana....Meenal hankalinta yakai k'ololuwa wurin tashi tashiga diririta ainun, haka ya kwana biyar acen batare daya farfad'o ba, dukta fice a hayyacinta  tashiga walahaula...se a kwana na biyar ne ya farfad'o Alhamdulillah kuma ya samu sauq'i sosai, danma lokaci d'aya ya soma magana tasha murna ba kadan ba, haka sukayi satuka hud'u da kwana uku kan suka baro garin yana cike da jin dad'in samun lafiyar sa.

Wannan kenan.

     ***********
Samuwar lafiyan muhammad da dawowarsu gida shine ya baiwa meenal daman komawa halayyar ta nada, a india sukan kwana a d'aki d'aya harma kusa dashi amma suna dawowa ranar farko shishi kad'ai ya kwana a d'akin sa, be damu da hakan ba sabida shi tunda ta damuwarta akan ciwon sa ta kula dashi ta gama masa komai, yasani ko baso aranta nasa to kuwa akwai Tausayi wanda yake fatan yakoma k'auna me tarin yawa.....

   Zaune yake a main parlor na gidan wanda acikinsa ne d'akunan gidan k'ofofinsu yake, yana jan carbi dake hannunsa idansa a lumshe yana tunanin yanayin dayakeji ajikinsa, harga Allah a 'yan kwanakin nan ya tsorata da abinda yake fitar wa a hancinsa, seyake fito da tsoka ja jajir a hancinsa kota mak'oshinsa, kwanajinsa 32 kenan da dawowa k'asar amma acikin kwana goman data wuce yana cikin tsoro me tsanani ya gama fitarda yin wata rayuwa me tsayi aransa ya sani yanayin dayakeji akwai illa kam, zuwa tai ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa tana taunar cingom dake bakinta a hankali, k'amshin turaren ta ne ya sanar masa zuwanta  wannan ne ya sanya ya bud'e idanshi sosai ya diresu a kanta, hango tai yanda sukayi jajir wannan ne ya sanya da sauri ta taso ta zauna kusa dashi, hannunsa ta rik'o taji zafi rau ta kai d'ayan hannunta saman wuyansa nanma zafi sosai cike da damuwa ta furta 

"Yaa moh kaddai jikinne? Kaga idanka kuwa, menene yake damunka kuma?" K'ura mata ido yae na kusan 20 seconds kanya dire numfashi yace

"My meena so nakeyi ma in kwanta, amma kwata kwata na kasa motsa koda d'an yatsa nane, zazzab'in jikina har mamaki yake bani, ga ciwon kai sosai  dayake damuna" cikeda tausayi tace masa

"Sannu yaa muhammad, Inshaa Allahu zaka samu lafiya, dama akan fitar danace ma zanyi ne gidansu zulaiha shine na shirya da zanje amma bari kawai namata waya akan bakada lafiya se wani lokacin" Gyaran zamansa yae

"Jeki abinki my Meenal, ai sauki a wurin Allah yake, ki tayani naje na kwanta a d'akina amma dan Allah karki dad'e kinji" murmushi tae sannan ta mik'e tsaye ta tayashi ta rakashi har d'akin sa, tafita tabar gidan jikinta a sanyaye haka bata wuce awa d'aya ba ta dawo masa gidan, tasha mamakin rikicewar jikinsa lokaci d'aya, tayi masa kuka sosai yanda bemasan inda yake ba, Dr. Sa dayazo ma yayita complain daganan akaje dashi hoton huhunsa emergency, A gaskia babu wani ceto daza'a iya yiwa muhammad a wannan lokacin, hoton ya nuna duka huhunsa na b'angare biyu ya gama nunnugewa, shine ma yake fitarwa a hanci da mak'ogwaron sa, ya gama tashi aiki, wano zubin abubuwan se ajali ciwon nan daba'a tunanin hakan, likitan ya shiga rud'u kasancewar sa amininsa, zamansa asibiti ma b'ata lokacine da wannan ya mayar dasu gida yake bashi pain reliver  sabida babu wani abunyi ba'a dashen huhu bare a dasa masa, sosai muhammad yake da ban tausayi....

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now