page 7

3.4K 269 3
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

              07

Mahaifin Meenal dana marigayi ne zaune a babban hall dasuke meeting na company susu biyu suna tattauna matsalolin da yusuf ke shirin kawowa wannan tafiyar, sabida ya tubure har yana cewa zebar garin

"Ka rabu dashi kawai Alhaj muhammad, ni inaga tunda ya nuna bayaso kar a masa dole, kasanfa mace tana lank'wasuwa amma banda namiji" Nisawa yae

"Kasan ai bana sauya hukunci, idan dai har Ameena ce tace bata sansa to wannan zan janye amma intace dani tana sansa tabbas se idan Allah ne ya hana"

"To tunda hakane muja lokacin da tsayi, kamar nanda shekara d'aya haka koma d'aya da rabi" Murmushi Alhaj muhammad yae

"Baza muwa yarinya haka ba, tasan dad'in miji fa, ka gane mana idan aka ja mata lokacin da tsayi baka ganin za'a samu matsala?"  Murmushi yae

"To yaya kakeso ayi?"

"Shekara d'aya ta isa, kan nan kaga sun isa sabawa da juna ko?" Haka suka tashi a kan senan da shekara d'aya auren...

**********
     Tunda usuf yabar gidan su meenal har akayi 2 weeks bata k'ara ji daga gare saba, tana mamakin sa tunda ankai k'arshen magana meye hakan kuma? Tanaso tamasa waya amma tanajin tsoron kiransa a waya sabida gargad'in daya mata....tanaso ta koyar dashi yanda ze sota ya saba da ita, duk da ita sam ba sansa take ba, amma  ba hali tunda ba damuwa yae da itaba, shawarar kiransa ta yanke wannan ne ya bata daman kiran nasa...

"Wake kan layin ne?" Ya ambata da muryarsa datake a bud'e kullum maganar kaman fad'a sab'anin moh dayake da sanyi sosai

"Ameena ce ya yusuf ina wuni, ya kwana biyu"  gyaran muryarshi yae ta k'ara bud'ewa

"Wace Ameenan?" Ya buk'aci sani

"'Yar gidan Abba mustapha" tsoki yaja

"Ke banza meye na kira na? Ban gargad'eki akan kirana ba?" Nisawa tae

"Kayi hakuri yaa yusuf, dama naga kwana biyu baka leqo gunaba kuma ba waya shine nace barinji ko lapia?"  Tsaki yaja

"Dacen ina zuwar miki ne? Eh nace ina zuwar miki ne munafukar Allah? Mezanzo nayi a wurinki? Me kike dashi na burgewa daze burgeni ko yaja ra'ayina nazo wurinki, waike kam sam bakya gane zance ne, inaga kanki kwata kwata baya ja, k'walwar kifaye ne dake, na gaya miki na tsaneki tsana mafi muni, wlhy danai tozali da wannan jemammiyar fuskar taki gwara nayi mummunan mafarki, dan nasan idan nayi adu'a ze kau,ke kuma ganin ki kurun yana haifar mun da tashin zuciya,k'azama kawai" Kalmominsa sun sakata a wani k'unci da bata tunanin akwai kalaman dasuka tab'a tunzurar da ita duk rayuwarta kamar nasa...runtse idanta tai tana me k'ok'arin mayar da k'wallan dayake shirin zubo mata.....lokaci d'aya  tunaninta ya kaita wani lokaci cen baya dasuke india.....

"My Meenal bana fatan wannan ciwon ya kaini lahira, ina matuk'ar farin cikin kasancewa tare dake, inaso inyi rayuwa me tsayi in bautawa mahaliccina kuma in rayu ina kallon kyakyawar fuskar nan taki bazan gajiya da kallonki ba har abada, koda wane lokaci ina k'ara yiwa Allah godiya da ni'imominsa akaina sabida banike a matsayin mata ma Ni'ima ne my meenal" A wancen lokacin kallonsa tae sheqeqe

"Kaifa ka iya b'atawa mutum rai, kurin muna zaman zaman mu seka soma rattafe mara ma'ana" bece komai ba se murmushi....

Harya kashe wayarsa tana nan runtse da idanta bata kuma dire wayar daga kunnen taba, tana matuk'ar san tacikawa muhammad burinsa na auren yusuf amma tayaya? Yana mata wannan mummunar tsanar ina zasu daidaita, ashe zuwan muhammad a wurin ta kafin auren sa zallar so ne? Ashe k'iyayyar mutum a wurinka kan kai haka? Dukda take k'in muhammad  bata k'in fitowa idan yazo mata, har kwalliya takeyi,kuma idan ya kwana biyu bezo mata bama har fad'a takeyi taji duk ta damu akan rashin zuwan sa, kenan k'aryar tsana take masa? Ashe k'aunace bata gane ba se yanzu dabatada amfani?.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now