page 31

3.2K 306 18
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*
 
Wattapad 68billygaladanchi.

    31

Adama ce ta jiyo sautin k'arar abubuwa da kuma gunjin kuka, bisa ga dukkan alamu kuma daga b'angaren sawun takawa ne, dan haka da azama ta d'auki hanyar part d'in nasu, kai tsaye d'akin ta shiga da sallamar ta, Mamakin yanda jini ke fita hannun meenal tayi lokaci d'aya ta d'are kan gadon

"Subhanallah dawun takawa meya samu hannunki haka, ya naga d'akin duk kaya a warwaste?" Batace da ita komai ba dai, haka taje ta tattaro jama'ar gidan takawan baya nan ya fice yanzu, dan haka duka nemi taci akaje da ita asibiti, hannun aka duba aka mata dressing nashi, deep cut ne ta samu gashi hannun nan ne me karaya, kai Meenal dai taga rayuwa itakam, koda sukaje gidan bata dena kuka ba, su a zatonsu kukan zafin da hannunta ke mata take se sannu suke mata dukansu, an gyara d'akin tsaf aka kawo mata abinci amma ko kallon sa batayiba, ita gidan ma gaba d'aya duhu yake mata, Niger take so ta koma abunta.

**************
    Nusy yau abun duniya ya dameta gata an kawota wannan masarautar ga Baraya, an ajiyeta batare da ance mata komai ba, ga sarauniya daurama ta mata alk'awarin kisa, hankalinta atashe yake acikin kwana d'aya dukta rame, batada masaniya akan sak'on da akace ita tayi wlhy itakam, batawa kowa message ba, yama za'ayi ta tonawa sarauniya asiri?, Bakin ciki kam ya isheta matuk'a se kuka takeyi.

   Takawa be waiwayi gidan ba se after 9 na daren ranar, be nemi kowa ba ciki kuwa hadda Meenalyn mu'az, zuciyar sa ce ke masa wasu alamu na damuwa da ita yakeso ya k'aryata zuciyar tasa da wannan yae alk'awarin baze k'ara matse mata ba, baya baya ze rik'ayi sabida bayaso yanda jikinsa ke k'aryatasa idan suna tare, ba gangar jikinsa ba xuciyar ma k'aryatasa takeyi,idanshi sesun k'aryata tunaninsa daidai kunnayensa so suke su zauna su saurari muryar Meenal, meyasa ze cuci salma akan hakan? Shi arayuwa ko Salman sa bewa haka ba, yasani wannan sabone kurin ke k'ok'arin shiga tsakanin sa da Meenal badai soba, salma kad'ai yake so baze tab'a had'a son wata dana salman saba, baze cutar da ita a bayan taba, dolene ya nesanci zama kusa da Meenal, Burgesa takeyi, magana idan Meenal nayi seta shagaltar dasu wurin kallon bakinta, Tafiyarta me sanyi tana kashesa, yin tafiyar takeyi tamkar arayuwa sarauta ajininta yake haka yakeso shi dama ce, Besan meke damunsa ba idan idanshi ya tsunduma a nata, seyaji lokaci d'aya jikinsa ya mutu babu abinda yake masa dad'i sama da kwana ajikin meenalyn sa, shifa yana cikin masifa fa, baze tab'a cutar salman saba danma Allah yasa basonta yakeyiba, yaudai juyi kurin 'yan mazan keyi amma bacci ya gagaresu, yau kuma k'aunar kwanciya ajikin Sawun sa yakeyi ita kad'ai zata haifar masa da dukkanin farin cikin dayake buk'atar samu a saman shinfid'ar sa, Lumshe idansa yae, be tab'aji ya kasa bacci ba dan salman sa bata kusa dashi, hasalima sabon sane hakan amma to yu meke damunshi, kenan tsakani daida Allah har k'arfe biyun dare ya gagara bacci akan lallai seya rab'i jikin waccen Meenal d'in? To kodai sabida yawan sha'awar dayakeji ne yanzu yakeso yaje gun mace badai sabida yana meenal bane ba yanaga, Tokuma idan itama ya saba da ita yazo kuma suka rabu yakenan, gwara kurin ya zauna warsa anan d'in, bacci fa ya gagari Malam mu'az har k'arfe Ukun dare, da wannan ya tashi yaje hanyar d'akin Sawun Takawar...!!!!

   Da sallamar sa ya shiga dukda baya tsammanin ganin ta ido biyu kota amsa masa, amma ga mamakin sa zaune take ba komai ajikinta se under skirt dataja har zuwa saman k'irjinta, fitila a kunne tana dafe dakai, dasauri ya taka zuwa inda take ya d'are tsakiyar gadon inda take zaune, hannunta ya sauke daga saman kanta data dafe, yabi idanta data sauke masa a wahalce da kallo, sun kumbura sunyi jajir fuskarnan dake fara k'al tayi pink sosai sekace wacce tasha naushi, kallonta yake ido cikin ido amma ya gagara furta wata kalma, hannunta dake d'aure da bandage yabi da kallo, rik'o hannun yae

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now