page 24

2.8K 282 16
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

    Wattpad 68billygaladanchi

              24
Wata irin fusatace ta tasowa Sarauniya Hassy, lallai zata wulak'antar da wannan yarinyar ina ta samo wannan bayanan?, tayaya tasoma maganar sirrin daya shiga tsakaninta da waziri, wannan sirrine wanda babu wanda yasanshi daga ita se wasiri se kuma hajiyar Rusau se Allah, se sharce gumi takeyi a wannan daren bata runtsa ba, kanta ya dena ja kwata kwata, kodai da bak'ak'en aljanai take yawo ne? Da wannan ta yanke shawarar zuwa gun waziri domin su tattuna barin masarutar ya kamata, no where is safe yanzu acikin masarautar, shirinta tsaf tayi ta kama hanyar waje wuraren k'arfe 8 na dare, malmo ce ta walwalo da gudun ta ta zube a k'asa tana me baiwa Meenal girma tace

"Ranki ya dad'e Sawun Takawa Iska ta kad'a shanyar da kikayi zuwa wajen masarautar nan yanzu yanzun nan" Murmushi Meenal tae  Malmo akwai kaifin basira da saurin hadda akan nan, kallon sauran kuyangin ta tae  dake wurin sannan ta mayarda dubanta zuwaga Malmo

"Ba wani abu bane me muhimmanci tunda akwai ire irensu da dama anan, jeki kawai sabida binshi wajen msarautar ma rashin tsaro ne" K'ara duk'ewa Malmo tayi

"Zanje inci gaba da kulawa da sauran, gudun kada iskar ta k'ara watse mana su" jinjina kai kurun tae ita kuwa ta koma waje, kai tsaye Meenal Bed room d'inta ta shige ta masa key, sannan ta bazama danna Audio d'inda ke zuwa mata direct, shiru babu komai sabida bata isa wurinba, tafi one hour tana saurarenta harm ta sare sannan ta soma jiyo maganar su

*
"Waziri akan zancen damukayi daka kwana biyar data wuce, dawa kayi magnar ne? Kallonta yae cikin mamaki

"Haba mana hassy? Dawa to zanyi maganar ne e?  Ko tun shekaru sama da 30 da suk wuce mun tab'a yin maganar dakikajita a wani wurin?" Nisawa tayi

"Karkaji haushina waziri wannan sawun ce ta takawa take k'ok'arin wulak'antamu indai bakayi maganar nan da wani ba inaga to wlhy da bak'ak'en aljanu take aiki, Audio fa ta kawomun na maganar dukda muka tattauna dakai acikin sirri, kuma ciki hadda sharrin dana kulla mata nabaiwa wata guba ta zubawa takawa, dukkanin wasu sirruknmu da basu wuce wata d'aya ba wlhy tana sane dasu" da sauri ya kalleta

"Toko dai tana amfani da wasu abubuwan computer nan ne na zamani" girgiza kanta tayi

"Anan dajin kuma Waziri?, tayaya wata computer zata zo nan, aljanine dai tasaka yake bibiyata, kuma shiri zanyi inje Niger gobe, gun Mark'azuzu d'an tala, Zansa kai tsaye ya dakatar da aikinsu ya haukatar mun da ita kowa ya huta, batada labarin wuta ta tab'o, sabida ni wlhy ba'a wasa dani batada labarin gidan zaki ta kawo kanta da kanta, ni zakanya ce kuma bana wasa"  dariya suka kwashe dashi kanta kuma cewa

"Idan kuma mukayi wasa seta tona asirinmu akan Sarki Abduljalal, yin hakan kuma barazana ce agaremu babba"  HAKA suka gama tattaunawa sannan ta nufo masarautar.....

   Meenal kai tsaye ta mik'e ta shirya sosai shiga me tsadar gaske sannan ta shirya zuwa B'angaren sarauniya, lokcin k'arfe sha d'ayan dare yakusa yi, acen sarauniya ta sameta, kuma kowa ya kula da tsoratar da tayi sanda ta ganta, zubewa meenal tae ta gayar da  ita agaban kuyangin ta, amaimakon ta ansa seta kore duka kuyangin ta  ta mayar da dubanta zuwaga reta, mik'ewa tae ta tako har suna jiyo bugun zuciyar juna ta fuskanceta tace.

"Ina da ido k'waya dubu, kunnen k'waya dubu, k'afafu k'waya dubu, mjiya k'waya dubu, magana k'waya dubu, dukkanin jikina dakike ganinsa ido ne sunkai k'waya dubu, asaman idanuwa na dubu inada kunnaye guda biyu, kiyi kuskuren zuwa  Nigar jibi in kasheki tun a hanyar ki ta zuwa base kin isa ba, ki kira bokanki a waya kuma kiji labarin mutuwar shi zuwa gobe da safe, kiyi kuskuren sakawa a haukatani zan sanyaki mutane dubu su soma miki kallon mahaukaciya cikin second dubu, kina zata ke kad'ai Allah zeta baiwa sa'a a duniya? Ki kiyayeni wlhy, inji maganar zuwa Niger in sanar da inda tsohon sarki yake kuma in kashe mutum in kashe banza.....Abu na gaba kuma ki sani wlhy nasan cewar acikin yaranki akwki wanda ubansu ba sarki bane ciki kuwa hadda d'an fari...hahhhhh ta juya kawai ta barta a tsaye cikin tsananin fad'uwar gaba  da tashin hankali, seda ma taje tagaga zata fad'i ta rik'e kujerar dake kusa da ita, zufa se tsatsafo mata yakeyi tako ina.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now