page 21

2.6K 263 13
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

  Wattpad @ 68billygaladanchi.

        21

Zaune talented take tana k'ok'arin bank'ad'o wani sirri, btada wurin saka tracker se'a jikin madubin Takawa, yanda za'ayi ta samu madubin take tunani, kota yaya abinda takeso tayi ze yiyu? Tasani setasha bak'ar wahala, kuma dolene tasanya wannan abun, sabida dole shine ze bata damar inda yake harta aikata shirinta a part d'insa idan yayi nisa wa wurin. Kanta yayi zafi sosai a wannan karon dan haka ta mik'e tsaye tana zagaye d'akin dayake mallakin a k'ofar kudu dake cikin masarautar Hankaka.... Bazatawa wannan msarautar zuwan banza ba, ya zame mata dole t d'auki qwaqwarn mataki yau d'in nan, kimtsawa tayi ta fito, motarta ta fad'a ta nufi masarautar Gabas.....

*************

   Da sallamarta ta shiga part d'in na Meenal, haka su malmo dayake sun santa suka bata izinin zama a parlor d'in gidan, daganan d'aya ta shiga ciki domin sanar da matar gidan bak'uwar dasukayi......

"Kikace Anty Nusaiba?" Meenal ta tambaya  cikin qosawa da maganar"

"Ea Sawun takawa itace, Anty Talented ce" gyaran kwanciyar ta tayi

"Ta dawo zuwa jibi banida lafiya, kuma kinsan na hana kowa shigowa nan d'akin so bazan iya fitaba ita kuma taje se jibi" Juyawa tayi taje ta sanar da Talented akan Sawun takawa batada lafiya, sedai zuwa jibi. Ba haka tasoba  kuma taji zafin abin amma haka ta mik'e seda ta k'arewa parlon kallo sannan tafita.

    ********
Yauma kamar kullum takawa zaune yana baiwa Meenal Youghurt sabida tunda abin ya faru taki cin abinci takuma dena masa magana, bayason hakan datake masa ko kad'an

"Bazakiyi mun magana ba wai?" D'agowa tayi suka had'a ido ta turo baki har tana juya masa baya hannun sa yasa wurin waist d'inta ya zagaye...so yakeyi yace mata tayi hak'uri amma kalma ce dayake iya gayawa mutum d'aya tal aduniya kuma batanan....

"Ya wuce please" ya iya furtawa  cikin sanyin murya, kallonshi ta k'arayi

"Meye ne?" Ta tambaya cikin wat murya data sakashi d'agowa ya kalleta shima

"Ba kinji haushi ba?" Har yanzu idanta a nasa yake, k'walla ta tattaro ta zubar akan kuncinta

"Ni ka rabu dani" ta furta cikin kasala bacikin fad'aba ko kad'an, ya gani taji zafinsa sosai be dace yana saraki guda ya kai hannun sa jikin mace, amma yarinyar ce batada kunya, ajikinsa ya manna ta

"To ya wuce ai" Kalmar hak'urin ce take masa nauyi....kuka taketayi yana patting bayan ta  hankali haryaji numfashinta ya sauya alamun tayi bacci, kwantr da ita yae, ya kwanta sosai kusa da ita, seda ya tabbatar baccinta me nutsuwa ne sannan yae yunk'urin zare jikinsa anata, rik'oshi tayi tamau yana murmushi dole ya kwanta duk sanda yae yunk'urin tashi seta rik'oshi tamau, harga Allah kuma bacci takeyi.....

**********
  Zubewa kuyangin sukayi sanda Talented tashigo part d'in suna gayar da ita, a dak'ile ta ansa musu ta neki kujera ta zauna

"Sawun Takawan fa?" Ta tambaya tana me k'urawa Malmo na mujiya, sadda kanta k'asa tayi

"Tana nan amma Takawan yana ciki, kuma bazamu iya shigaba kinga" gyaran zamanta tayi

"Zan jirata anan, ku wuce kawai" Barin wurin sukayi dukkansu ta mik'e ita kuma tana nazarin parlor d'in da camera's d'inda akace mata an saka sosai ta gansu sunkai goma a parlor kawai, wazgewa tai karya kasance a ganta, tashiga zagaye kawai, tana nan har kusan awa d'aya

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now