page 22

2.8K 278 26
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

               22

Acen ma hakan ce ta kasance, zubewa tayi tana rero uwar gaisuwa

"Allah ya taimaki mahaifiyar me mulkin masarautar Hankaka, Allah ya k'ara girma, ina neman afuwan rashin zuwa in gayar dake kwana biyu, jiki da jini ciwo nayi" Murmushi tayi

"Babu komai 'yata, hakan ma ba laifi bane ki huta shine fatanmu, karki wahalar da jikinki" Murmushi tayi ta sadda kanta k'asa tana me jiran k'ara cewarta.....kyautata mata wurin zama akayi aka wadata gabanta da kayan ciye ciye, ba laifi tad'an tab'a abubuwa sannan tanemi yi mata sallama, ajikinta ta kula kullum zoben hannunta yana nan ko wancen zuwa haka t tarar amma laifin liqawa a wurin wataqil dashi take wanka, Harta mik'e ta k'ara zubewa

"Hajiyar mu aduk b'angaroran masarautar nan nakula nan ne kurun yakeda cikar abubuwan k'awata d'aki na gargajiya, wani lokacin idan na k'ara zagowa zanso kuyangi sumun iso inga kayan tarihi" murmushi Hajiyar rusau tayi

"Da zaki iya k'ara lokaci aida na rakaki da kaina yanzu" k'ara duk'ewa tayi k'asa hannayenta biyu asaman carpet datake zaune  tana me k'ask'antar da kanta

"Ban isa na saka mahaifiyar Hankaka kaf d'inta zagaye ba, tuba nake hajiyar mu, a had'ani da kuyangi" murmushi tayi ta mik'e ta rik'o hannunta ta mik'ar da it tsaye sannan tace

"Nice nake sha'awar yin hakan, kodai kishine abin, kuma me gidan aiya tafi abinsa" murmushi Meenal tayi suka rankaya don zagayen wurin seda suka zaga sosai sannan ta kaita d'akinta cenne yafi abun kallo na gargajiya wannan matar akwai tanadi, duk dukiyar daka b'angaren Dakuna biyune da parlor biyu kcal keda kwalliya irinta zamani duk sauran gargajiya ce, hannunta takai wurin wani abu da ake kira lefe ta shafeshi tare d'ana 'yar matashiyar recoder a d'akin, wacce bazakayi saurin gane waba

"Hajiyarmun ina san wannan abun" murmushi tayi

"Wannan kakatace ta bani akwai wanda mahaifiyata ta bani kizo muje zan baki"

"Laa ba komai hajiya shima me muhimmancine ki ajiye" Batai maganaba suka fito daga d'akin a d'ayan d'akinma tayi nasarar mannawa har wuri biyu

Haka tayi mata sallama sannan ta koma b'angarenta.

************
   Zirga zirga Nusy keyi  tsakiyar d'akinta tamkar me yunk'urin nak'uda tana tunanin yanda akayi Meenal ta ganta, kodai tasan wani abune game da ita? Kai ina bazata sam komai ba, tanayin komai ne cikeda nazari, to kodai kurun taganine btasan ko meye? To ina zata sani tunda ba kowa yasan abunba ma wannan sokuwar, koda yake har yau tana tunanin inda tasan yarinyar kman ta santa, bata tunano komai ba, yanzu ina zata k'ara d'ana masa tracker? Motocin hawan takawa sunkai sha biyar yana masifar san  mota, to Amma akwai motr excort nashi dasam baya fita seda ita haka zatayi, ajikin motar zata saka kurun sabida tanada buk'ara yin aiki a b'angaren sa, dole t d'ana bama bamanta bataso meenal tayi wani dogon sabo da Takawa daze kaita ga kasa  aiwatar da shirinta akan ta, matakin su na farko ze soma aikine daga yau sabida tsaro.

***********
   Washe gari shirin asuba tayi ta jere kuyangi zuwa b'angaren Takawa, Excort nashi ta tarar da fadawansa, malmo ce tace

"Asanar wa Takawa Sawunsa tana nan iso sarkin fadawan Takawa" wani security ne yace

"Yace ya dawo sallah kar wanda ya tashesa se sanda ya fito" Shiru sukayi Meenal kuwa ta taka har inda yake tace

"Zan shige bani hanya" Kwarjini ta masa amma be d'aga ba tace

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now