49

2.7K 291 12
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

    Wattpad @ 68billygaladanchi

        49

Tun asuba ya farka dan haka masallaci ya wuce ya gabatar da sallan asuba be dawo ba se 7 bayan daya kammala Azkhar da addu'o insa, koda yazo har hadimai mata sun iso sun kimtsa wuri, an kawo breakfast ma daga gun ummie,wuri suka bashi ya zauna ya ciyar da matarsa yana sanye cikin jallabiya bak'a  me gajeran hannu, bameyin magana se kallon juna dasuke suna sakarwa juna murmushi, Dr. Sunita bata shigoba se wuraren 8:am, bayan sun gaisa ta kalleshi

"Yallab'ai yau zuwan sassafe akai mana ne?" Murmushi yae
."anan na kwana me kika gani?" Rik'e bakinta tae

"Lallai lokaci yayi dazan sallami matar manya suje cen gida su k'arata, sedai kuma yanzu muna buk'atar privacy zamu duba rufewar bakin mahaifar ta idan komai yayi daidai seku tafi gida" jinjina kanshi yae ya mik'e tsaye seda ya k'arewa team d'in kallo mata uku maza shida se ita sannan yayi waje, kasa nutsuwa yae ya k'ara shigowa d'akin, cak suka tsaya da aikin dasuke suna kallon sa, wani tashin hankali ya shiga ganin abinda sukeyi, da sauri yae wurin meenaly yaja zaninta zuwa rufe jikinta a hautsine ya kalli sunita

"Dr. Me hakan yake nufi, bakida hankali ne? Yaya zaki taramun karti suna kallarmun tsiraicin matata ta? Su awa harsun isane saraki ce fa? Akan me za'amun haka" Dafe kanta tae

"Subhanalla Yallab'ai nanfa Teachin hospital ne wa 'yannan student dr. Ne dukansu koyon aiki sukeyi" wata muguwar harara ya wurga mata

"Sesu rasa inda zasuyi practical se akan matana, ke bakida hankalina dazaki janyosu nan, idan bazaki dubata ke kad'ai ba banason aikin, aikin banza aikin wofi kawai" Sanin halinsa ya sanya ta sallami student ita kad'ai ta duba meenaly ta tabbatar komai normal sannan ta sallamesu gaba d'aya cikeda k'osawa da rikicin wannan sarakin mejin hayaki, meenal bata k'ara ganin hak'orin Takawa ba har suka isa gida, b'angarenta yaje da ita da kanshi ya tayata wanka yana mamakin girman cikinta dukda ance d'aya ya fita amma gashinan ya girma sosai, haka aketa shirin bamewa wani magana, duk iya k'ok'arinta naso taga ya sake mata fuska abun yaci tura ya kama yayi kici kicin da fuskar nan kaman be tab'a dariya ba, tarasa dalilin sa na mata wannan fushin ita babu abinda ya had'asu ita dashi kafin shigowar likitoci ma har wasa yake mata tome ta masa? Haka yagama bidirinsa yabar b'angaren nata batare dayace mata kanzil ba, be k'ara waiwayarta ba a wannan wunin gaba d'aya.

**********
   Shirinsa tsaf yae ya kama hanyar  zuwa asibiti gun sarauniya daurama lokacin k'arfe hud'u na yamma ta gota sosai,  yaranta duk suna wurinta har masu aure wani masarautan, gaggaiswa yae dasu kowa haushin sa yakeji, seda yaja kujera ya zauna kusa da ita sosai sannan yace

"Kakus meye labari? Ance haka kawai kika fad'i nace kodai kinyi kallon ne bada niba" d'ago kanta tayi ta kalleshi cikin takaici kafin ta kawar da kanta gefe d'aya batare datace masa ci kanka ba

"Bakyaso kike kallon me gidan ne, kodan banzo  tun jiya ba amarya ce ta rik'eni" Yayar babanshi ce tace dashi

"Takawa bakaga tanajin jiki ba wai? Yanzu ba lokacin wasanni bane ba kanajina ko, idan ba dubiyar Allah da annabi kazoba kazo ka shige fitsararre kawai" Mik'ewa yayi yana shan magani sosai

"Ban gane ba? Idan ke bakisan dalilin ciwon taba nina sani, ki tambayeta labarin caset mana data kalla dana saurare zata gaya miki komai na tabbatar idan ma ita hawan jininta kurin ya tashi ke da ruwa da komai har b'argon jikinki seya tashi kinji ni ba, idan ma bazata baki ba ni inada copie's sunfi dubu ko a motane sena baki d'aya" Rasa tayi meyake nufi da inda ya dosa kallonsa kurun ta tsayayi harseda ya juya yabar wurin, kasa hakuri tayi seda bishi baya ajikin motarsa harya zauna ze rufe murfin tarik'e shi

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now