page 45

4.1K 333 39
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad @ 68billygaladanchi.

*Na sadaukar da wannan shafin gareku mutanen wattpad Allah yabar k'auna*

*Zuwaga reader's, Naga comment naku, kuma ku sani bayau nasabayin rubutu ba bakuma zanbi ra'ayin daba nawa ba dole abinda nake ganin ya dace kuma daidaine shi zanyi, kunawa writer's uzuri please*

*Magana ta tagaba itace akan masu zuwa suna damuna akan wai nice billyn Abdul koba ni bace, so dubu nawa zance bani bace har a shafukan litattafaina barkatai? Harse yaushe zaku fahimci cewar Galadanchi da Abdul sunayene kurun amma ko wanne da muhalinsa, ina mahad'in sunan mutum da kuma anguwa? Nayi bayanin yafi a irga takwara ma tayi a shafin ta, mesa semune zaku tashi hankulan mu da zuwa pc akan wace ce wa acikin mu? Shekaruna sunkai 4 ina rubutu, idan bzan manta ba takwara ma tayi su kuma a media, salon tafiyar rubutun mu ma ba iri d'aya bane shine menene abin matsemu, shekaranjiya wata tazo wai nace da ita ni ba Billyn Abdul bace wai wulak'anci nake mata to k'arya takeso nayi, yakamata ku fahimta acikin writers akwai Billy's da yawa, ga Billy S fari, fa billy Tabacco ga sunan da yawa semune kurun sabida neman fitina zakace k gagara banbance mu, gaskia na gaji da bayani dan Allah kar wacce ta k'ara zuwa akan tambaya na Wacece ni Tsakanin Billy Galadanchi da Billyn Abdul dan kuwa wlhy basuda had'i sunayen nan, The fact that nima sunan mijina Abdul bashi zesa akasa banbance muba danni koda wasa bantaba sanya sunan sa ajikin nawa ba adai rubutun littafi, kar wata ta k'ara cewa na mata wulak'anci, dan duk wacce ta k'ara tambaya na wacece ni acikin biyu wlhy bazan kulataba*
      45.

Kujera meenal taja ta zauna kusada sarauniya hassy sosai tana murmushi, sarauniya ta zuba mata ido ko k'iftawa batayi ba kana kallon fuskar nan zaka hango masifa k'arara a idanuwan ta, gumi kurin take had'awa gata a d'aure

"Yauga sarauniya a kurkurun meenal, daso samune ma yanda kika turo mana k'arti muma mu turo miki su nan su casa mana sarauniyr hankaka me ritaya" ta furta kalaman tana me wadata fuskarta da k'ayataccen murmushi cikeda shak'iyan ci" Harararta Hassy tayi

"Duk ranar dana fita daga nan wurin wlhy Ameena sekin banbance tsakanin aya dakuma tsakuwa,nifa ba kanwar lasa bace ba,yanda kikaga nafiki shekarun nan wlhy nafiki wayau, koda kike murna bana masarauta wlhy na d'ana tarkuna masu tarin yawa akanki, dake da wannan cikin dake jikinki duk se an hallakar daku, ke kinyi kad'an ki haife yaron daze gaje sarautar masarautar hankaka, se yaron 'yata Hidar dan nasan mugun nufin ki akan ki kashe sa ke naki yaron ya gaji sarautar" Murmushin takaici meenal tayi

"Babbar matsalar ku kenan dake shirin hallakar daku, bakunan ku basuda abin fad'a daya wuce son duniya, zuciyoyinku basuda muradin daya wuce ku mulki duniya, ruhin ku baya buk'atar gangar jikinku fiyeda yanda yake so muku duniyar nan da abinda ke cikinta, shin wai kin tab'a zama kin tambayi kanki makomar shuwagaban nin dasuka gabaceki? Dake haka kike wannan furfurar ta saman kanki da kinada shine? Ki sani yanda shuwagaban nin ki suka mutu suka bar duniyar da mulkin da 'ya'yan dasukewa kwad'ayin mulkin da matayensu da komai haka kema da mijinki da sarautar taki da halin dakikawa kanki guzuri zaku gangara ku shek'a lahira gaba d'ayanku, batare da komai ba se farin k'yalle, kamar yanda baki ankara ba sanda kikabar zanin goyo, baki ankara ba sanda kika dena jan gwiwowinki a k'asa, baki ankara ba sanda kika mik'e akan tafukan k'afafunki, baki ankara ba sanda tsayin k'afarki yajaki daga shekarun k'uruciya zuwa na budurci, baki ankara ba sanda kika ganki da arzik'in 'ya'yaye har kika manta kika shiga d'imauta baki ankara ba har bak'ar sumar kanki ta juya zuwa fara da bak'a, haka idan kinyi arziki sumar kan naki bazaki ankara ba zata koma fara tas!! Kokuma bazaki ankara ba zaki wayi gari 'yan uwanki suna kukan  rashinki gaki a kwance me k'arfin iko akanki ya k'wace komai, yaraba rayuwar da ruhinta, ya raba gangar jikin da ruhinta ya raba zuciyar da ruhi sekuma wata bake ba, haka zata faru akaina batare dana ankara ba, haka zata faru akan kowa batare daya ankara ba, idan dazakibi ta tawa dakin rufawa kanki asiri kin k'arisa rayuwar tsufanki cikin bautar Allah mahalicci kin tattare son abinda zaki mutu ki barshi a duniya kin ajiye agefe, ni nan dakika ganni, zuwana acikin gidan sarauta aganina jarabawa ce babba Allah yayimun, musamman sabida yanayin yanda ku azzalumai kuka yawaita a masarautar, na d'auki zuwana a wannan masarautar matsayin k'addarar rayuwa mara dad'i sedai na barwa Allah dankuwa shishi kad'ai yasan manufar sa ta wurgoni acikin wannan masifar, zuwana gidan sarauta na samu darasi me k'arfi na rayuwa, zuwana agidan sarauta na k'ara sanin ciwon kaina, ni Hidar dakike magana d'ana ne kuma inhar muddin ina raye ina tsaye acikin gidannan to kuwa Takawa bashida wani magaji daya wuce Hidar koda kuwa zan haifi 'ya'ya maza dozin so d'ozin ne" Tsaki taja me tsayi

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now