page 47

2.8K 296 18
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

          47

"Wayyoo Allah na" ta furta acikin murya me nuni da alamar tana cikin azaba, hankalin sane ya k'ara dawowa akanta ya waigo tana kwance a sit d'in baya

"Abokin tafiya, abubuwan sun tafi yanda ya dacene?" Jinjina masa kansa yae

"K'warai kuwa Takawa,babu wata mishkila kuma sojoji sunyi sama da azzaluman" Murmushin takaici yae

"Bani escort mota biyar, ka gayawa me martaba zanje da meenal asibiti ne batada lapia sosai, amma Al-Ameen yana nan" Juyawa yae da sauri aka had'a masa motocin da securities take suka bar gidan zuwa babbar asibitin garin. Emergency aka karbe'su aka shiga bata kulawa na gaggawa, har kusan asuba likitocin basu zauna ba suna kanta, tun tana gane me ake ciki harta shiga d'imauta tafita hayyacinta, Takawa ya kasa zama ya kasa tsayi se zirga zirga yakeyi ga abubuwan daya baro a masarutar sa, ga matarsa kowa ya tambaya sedai suce ya k'ara lokaci ko ace ya kawo wannan allurar ya kawo wancen, hankalin sa kam in yayi miliyan tobaya jikinsa.

Se wuraren k'arfe shida na safe lokacin harya je yayi salla ya dawo sannan Dr. Sunita ta kirashi office d'inta, zama yae ya tattare nutsuwar sa akanta yana so yaji me zatace

"Ranka ya dad'e kokasan cewar matarka maganin zubar da ciki tasha kuma me k'arfin gaske, sa'ar ta d'ayaa bataci da yawa ba da tuni an wuce tarihin k'waik'wayen dake cikinta" kallon ta yae cikeda nutsuwa amma ya kasa furta komai se wasa da yake da harshensa acikin bakin sa seda ta kuma cewa

"Sir koda masaniyar ka take k'ok'arin zubar da cikin ne?" Teburin ya kaiwa wani mugun duka seda ta razana itama, da ya tsansa ya nunata

"Karki kuskura ki k'ara jifana da muggan kalamai nida iyalina, ko shegene cikin bazan zubar ba bare inada igiyar aurenta akaina, zakimun bayanin meya faru ina aka tsaya kokuma sena kai k'ololuwa wurin b'acin rai na firgita naki tunanin" Gyaran murya tae cikeda tsoro kanta had'iye wani yawu me d'aci

"Ranka ya dad'e ba haka nake nufi ba, indan maganin zubar da ciki shitasha kuma me k'arfine sosai sedai beyi tasirin dazeyi aiki nan take ba sabida kad'an tasha, amma kuma yayi b'arna sabida wannan rashin harmu aka yiwa dan na tabbatar abun alfaharin mune ace mun karb'i haihuwar 'ya'yan sarki kuma tagwaye a wannan asibitin, amma cash anyi rashin sa'a cikin ya zube da k'yar da yardar Allah muka samu ceto ran d'aya shima bamuda tabbacin ze tsaya d'in sedai tunda yanada rai akwai bugun zuciya muna kyautata zaton idan tasamu bed rest ze daidaita amma d'ayan kam ya kad'e kaf" Dafe knshi yae sannan ya koma ya zauna jikinsa a mace

"Ki taimakeni Dr. Ki rufamun asiri ki kular mun da matata karki bari wannan cikin ya zube duka, wlhy ina matuk'ar son cikin na jikinta fiye da yanda nakeson tawa rayuwar,kuma ki sani ba ita ta zubar da cikin a abunci wasu mugwaye suka saka mata kodan wannan ki taimaketa dan Allah" Murmushi tayi

"Inshaa Allahu i will do my best sir, karka damu kaji" Jingina yae jikin kujerar

"Zan iya ganinta yanzu?" kallon agogon hannunta tae

"Zaka iya ganinta amma kuma bacci take mun bata allurar bacci sabida ta samu hutu, madam ta wahala fa cikinta ya soma girma sanda ya fita kusan 4month fa ai yayi k'wari" Nisawa yae

"Nasani wlhy, Allah yana gani kuma shine shaidata sena wulak'anta duk wani wanda yakeda hannu acikin wahalarmun da meenaly na" murmushi tayi ya matuk'ar burgeta sekace na sarki ba, sam bashida girman kai akan iyalan sa, ji yanda yake tarairayarta kaman k'wai, mik'ewa yae bayan sallama da godiya yabar d'akin zuwa nata d'akin.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now