page 8

2.8K 254 16
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                    08
Yusuf yana matuk'ar son budurwarsa dasuke soyayya maryam, bayason abinda ya tab'a ta ko yake shirin tab'ata, sannan baya kawowa rayuwarsa auren wata idan ba ita ba, Meenal bata daga cikin tsarin matayen dayakeso bakuma burin sa bane ya taki takalmin da yayansa ya taka, tsohon takalmin yayansa ba abin takawar sa bane ba, gashi kuma acikin wayar marigayin dake hannunsa yaga saqonnin cin zaragi da wulak'anci da meenal ke aika masa ko bayan aurensu, babu sak'o d'aya dayaci karo dashi da arziqi dukna tsiya ne!!! Besani ba ko hadda bak'in cikinta ya haddasa wa yayansa mutuwa koda yake ya sani itafa mutuwa lokacinr koba ciwo setazo...tunda aka gayawa mahaifinsa one month ake so ai auren ya sanr masa seya saka masa kuka wiwi tamkar wani jinjiri ya hau ban baki da roqon Alfarmar amasa rai yawa wata alqawarin aure shiba yaro bane ba, ganin mahaifinsa baze sauraresaba yaje gidansu Meenal aka tara masa har ita da uwarta yasoma roqon su akan subarshi da zab'in sa...kai tsaye mahaifinta yace yaje zewa nasa mahaifin magana kuma shi ya janye, wasiyya ba tsarin Allah bace ba dan Haka ta hak'ura kawai.....

Meenal tayi kuka tamkar ranta ze fita, ga uwar k'uruciya ace ko shekaru 18 bata cika ba amma har yanzu batada nutsuwa, ta gagara yin karatun ma, saura kwana bakwai birhday d'inta amma harta manta dashi itada take 'yar gata shirin sosai iyayenta ke mata ranar zagayowar ranar haihuwata kuma itace take matsawa akan hakan...tayi magiyar tayi roqon akan acika burin muhammad amma mahaifinta yace batasan girman k'iyayya ba, indai har namiji ze iya cewa da iyayenka baya sanka to babu alkhairi a aurensa kwata kwata.........

Wednesday tazo ta wuce amma sam meenal bata lek'a park ba, hasalima ta soma mantawa dasu Hidar....tana cikin tsananin damuwa har seda sati yazo.....

Tana zaune ita kad'ai a lecture hall bayan an gama lecture kowa ya watse, 2 to 4 sukayi ta tuna da sak'onnin dasuka shigo wayanta bata duba ba, koda ta soma dubawa wani na layin datake amfani dasune d'ayan kuma na bank d'inta ne.....Tasha mamakin jin cewan wai yau ne birhday d'inta suna mata happy birhday, idan da lokacin da muhammad yake rayane shine mutum na farko dake fara aiko mata saqo amma baya hana ta aika masa reply nacin mutun ci, bata mantawa last year ma daya mata sak'o yanda ta kasance a tsakanin su

     *"Koda wane lokaci mukan kasance acikin tsananin murna yayin dukda muka k'ara wasu shekaru a saman namu shekarun.....Tsufa bayida magani wannan ne ya sanya gwara kayi murnar da godiyar Allah daya baka ikon kaiwa wannan lokacin, dubunka suna k'abari suna neman irin damanka ta rayuwa su bautawa Allah su k'ara daga cikin mizanin ayyukansu na Alkhairi kozasu rabauta, haka mutuwa ma batada lokaci sam, kayi murnar shekarunka sun k'aru kakuma ji tsoron dukkanin numfashin d'aya daka zuk'a ka kuma fesar to kuwa tabbas kana k'ara kusantuwa ne da k'abarinka,, acikin murna awa gobe tanadi dan samun tsira. Ina miki fatan Alheri ina miki fatan ki ninka fin abinda kika baiwa baya  a shekarunki cikin Alkhairin Allah.*

Wasu zafafan hawayene suna zuba daga idanta tunawa da reply data bashi....

*"A ido kake nuna kana sona amma nasani k'arya ne, banda haka ranar murnar zagayowar haihuwata kakemun fatan mutuwa? Aniyarka ta bika"* Toshe bakinta tai gudun kada wani yajiyo sautin kukan ta, tasani a park baza'a samu mutane sosai yanzu ba, gashi ba weekends bane ba, wannan ne ya bata daman tattare 'yan komatsanta tana tsananin kuka tabar wurin, k'awarta Zulfa ma tayi aure abinta tun tana india, kuma bata k'asar wayoyinta duk basa tafiya, ga alama ta dena karatun anan tunda dama ba nisa sukayi ba  Yanzu ne suke aji biyu....

**************
     Sosai Meenal keso tayi kuka amma abin ya gagareta, zuwa yanzu fa k'iri k'iri tana ji tana gani zata kasa zubar da k'wallan idanta se kukan zuciya dayafi da fili ciwo.....guri d'aya ta k'urawa ido na kusan mintuna talatin batare data koda k'ifta idanta ba, zuciyar ta har wani zafi take mata tamkar ana hura wuta......Hidar ne ya fad'o ajikinta yana ta kuka

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now