page 6

3.7K 296 10
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                     06
Da k'yar da rarrashi suka samu ta dena kukan tayi sallolin dasuka gabata da akayi tana bacci abincin ma da aka kawo mata gagara ci tai se kukan zuci datakeyi wanda yafi na zuciya ciwo, ta k'urawa abincin ido amma zahiri ba abincin take kallo tunanine ya lulata wata duniyar ta daban........

"Mesa kike cin abinci da spoon me my meena? Kuma babu tarbiya ko kad'an a yanayin  zaman ki nacin abinci, bakya ganin rashin dacewan hakan?" Wani kallo ta wurga masa a wancn lokacin kantace

"Kaga nifa ban iya kalan jahilcin daka iyaba, yaya zanzo acikin mutane irin wannan na saka hannu naci abinci, kagama bani kunya sannan kazo kanamun hauka akai" Murmushi yae

"My meena yana da kyau ki daraja d'an adam komai k'ank'ancin sa, kasancewar wani lokaci zezo dazaka gane amfaninsa, a wannan lokacin kuma  ba lallai ya kasance yana nan ba, abubuwa da dama game da halayenki suke rikitar dani, idan na d'auki b'angaren yanda kike yarfe manyanki da magana mara dad'i nikanyi fatan Allah ya sanya nini kad'ai kike yiwa hakan dannikam zan jure komai munin abinda zakimun, abinci dakike gani yanada matuk'ar muhimmanci ya cancanci darajawa me yawa wasunki sunacen asibiti sunason cin abincin amma Allah be basu ikon ciba, suna kuma da wadata sunada abincin, dubunki suna cen suna neman na safe babu bare sauran wuni, Akwai malali gashin tinkiya dasuke acikin k'aburburansu suna kuma son su dawo duniyar su k'aru da koda ladan cin abinci da hannu ne su qara dashi amma basu samu ba....ki gane mana my meena!!"  Ture abincin gabanta tayi lallai ta yarda ka kalamansa yanzu yanzu gata da ranta da lafiyarta amma damuwa kurin ta hanata cin abinci...tayi kuka tamkar ranta ze fita da k'yar suka samu tasha tea se kuma sukace a k'ara mata alluran ko kad'an ne sabida sunga tana cikin yanayin tashin hankali....

*****************
     *Bayan kwana bakwai*
Haka meenal ta dangana sabida ta k'ara yardarwa kanta babu wani mahaluk'i daze mayar mata da muhammad d'inta mutumin data haqiqancewa kanta batada wanda take k'auna sama a fad'in duniyar seda *TA FARU* ta kuma *KARE* sannan tasan akwai so a ranta!!! Tun tana samun daman kuka da idanta harta ya dawo sedai kukan zuci duk ta yamutse tayi dana sanin rayuwarta  da abubuwan data aikata agareshi ta tsani kanta har wannan lokacin bata karanta takardan daya rubuta mata ba yaune kuma ake shirin barinta a gidanta domin ta samu daman yin takaba cikin mutunci wannan umarnin mahaifinta ne wannan ya sanya aka qara me gadi d'aya dakuma wata baiwar Allah domin tayata zama wacce take 'yar uwa awurin mahaifinta da kuma 'yarta wacce take kusan sa'ar meenal d'in domin d'ebe mata kewa...yaune take shirin duba wasiyyan mamacin datayi Alk'awarin bi komai nauyin wasiyyar akanta kuwa inshaa Allah....ta sanya a ranta zata yi komenene tamasa abu na k'arshe dayake buri tayi agareshi......

*Ga abinda yace*

Assalamu Alaiki Ameenaty....dukda ina gab da barin duniyar nan hakan baze hanani so dakuma k'aunar kiba, ki sani babu me iko da rayuwata se mahaliccina amma likita ya gayamun kai tsaye huhuna baida wani saura!!!! Ya gama lalacewa kaf my meenal! Wlhy Ameena naso in rayu dake rayuwa me tsayi, nayi mafarkin tsufa in tara zuri'a a tare dake amma Allah be nufa ba, naso in sauke nauyin daban tab'a sauke munba Allah be bani iko ba kimun rai ki yafeni kinji...dalilin rubuta miki wannan shine domin in k'ra jaddada miki k'udiri na son ki auri k'anina Yusuf.... Ko bana raye 'yayan da yusf ze haifa nawane bazan yi bak'in cikiba idan kika hayayyyafa dashi se murna ma har a makwanci na, ma sani ni kika haifawa 'ya'ya bayan rai na, naso ki tsaya mui magana amma naga kin karaya da kala maina....ki daure ki taimakeni kimun wannan.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now