page 15

2.7K 264 10
                                    

     *🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                                  15
Tunda suka iso gidan ake d'awainiya dasu, sedai sunyi rashin sa'a daddy baya nan yana sokoto, hakan ce ya basu damar yiwa matar data karramasu sosai godiya suka tafi akan se washe gari zasu dawo tunda yake yauda yamma zezo, mom tashan mamakin ganin sarakuna agidan nata, ko lapia? Amma tunda me gidan yana kan hanya batada zab'in daya wuce ta hak'ura harya dawo d'in.

**********
    Shiru ba kowa a wurin Meenal se securities dake zagaye da d'akin wanda Takawa ne ya zuba su, tunani take ita meye had'inta da Takawa dazece ze aureta? Idan akan 'ya'yan sane ta dena shiga sabgarsu suma, ba had'in iya babu na baba daga had'uwar park!?? Shikenan sesubi su sanya rayuwarta a uku, meye abunda ma ya had'a yaran da ita? Zata gayawa ubansu yafice mata a rayuwa shida yaransa ita kamma ta tsanesu yanzu.

'''''''''''"" yana dafe da kanshi wayanshi ya soma ruri, alamar shigowar sak'o janyota yae ya bud'e sak'on dayazo direct daga talented

"Munyi nasara plan B yayi working dukda munyi failing A, yanzu Takawa ya buk'aci aurena kuma na nuna mazan iya aurar saba, zanta wasa da hankalinsa karyai saurin harbo jirgina, inshaa Allah bazan tab'a hanaka abinda kake soba, se dole naga bayansa tukunna zan saurara masa" Se sak'o na biyi dayace

"Wannan ka duba da kyau zakaga time da akayi sak'on da komai, jiyane da misalin k'arfe tara na dare, tsakanin Ameena da khaleed, ya kamata ka fita a harkar yarinyar nan" Murmushi yae, shi jiya ai bema aikawa Meenal buk'atar sa ba, Yaushe ma tasan ya buk'aci aurenta hartai magana da khaleed? Kuma da layukansa na Niger khaleed dayaje saudi baya k'asar, murmushi yae daya tsaya iya lab'b'ansa wato ita ga comuputer guru ko? Yafara tunanin dasa hannun talented a lalacewar al'amuran sa zuwa wannan lokacin, tabashi wrong infor kenan kusan so barkatai, amma ba komai muje zuwa.

*Wacece talented Nusy*

    Talented 'yace a wurin Durumbu, da mahaifinta ake zaman fada, kuma kusan kansu d'aya da marigayiya salma, tun tanada shekaru sha hud'u take d'awainiya dason Takawa kuma yasan tana sansa ,babu  kalan fad'an dabasayi da Salma akan sa tunda cenma amma shi bata gabansa, haka tanaji tana gani ya aure salma, gashi durumbu k'ofar kudu yake amma hakan baya hanata zuwa neman sa kullum, tare sukaje waje karatou danmashi militry school yake ita kuma tanada bala'in ilimi akan computer, ga neman infor kullum zaka ganta sanye da madubin ido tana dannan system, duk wani infor ta iya satoshi, ganin yayi aure da dad'ewa amma bata dena mutuncin ta dasuba ya sanya yae tunanin ta hakura da komai, yake kuma ganin tamkar tunda tana sansa bazata tab'a Cutar saba, bashida labarin soyayyar sa ke shirin k'ara birkita k'walwar talented take aikata abubuwa marasa dad'i, a wurin mahaifinta dayake shima acikin mugwayen da ake zargi ta samu labarin yana neman aure, hasashene kurun tae, inda sukayi rashin sa'a ma tasan yusuf da komai nata, yanzu abj take aiki shisa suke da kusanci sosai da Takawa, kuma dai yusuf abokin holewar talented ne, awurinsa talented tasamu tarihin Meenal da wannan taketa k'ok'arin cutar da rayuwar ta ta b'angarori da dama.

    Da sallamarsa ya turo k'ofar d'akin ya shigo, muryarsa kurun dataji seda ta wanzar mata dabmummunan fad'uwar gaba, lokaci d'aya  ta had'e girar sama data k'asa kana ta d'auke idanta daga duban sa. Seda ya kawo daidai gadon sannan yae burki ya kalleta cikin nutsuwa ya furta

"Menene yake damunki kuma?" Ko kallonsa batayi ba, ya k'ara cewa

"Bazaki tamyeni lafiyar yaranki ba?" Wani mugun kallo ta wurga masa

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now