MALEEK 01

2.9K 166 2
                                    

01

Bismillari rahmanir rirahim

Happy New year dearies plss support Me by voting and commenting





"...... dagudu ta karaso babu ko sallama cike da farinciki tana kokarin nunama mahaifiyar wani abu a takarda,

Uwar tsawa tadaka mata tana haba menaal wai yaushe zaki girma kidena wannan dabiar saunawa zance ki nitsu kikuma ringa sallama inazaki shiga gida, marairaicewa tayi tana kiyi hakuri mami wallahi tsabar farincikine, murmushi uwar tayi alamun ta hakuri

Muryar baban sukaji daga bayansu yana haniyar me nakejine saurin juyawa tayi tace abba katayani farinciki nasamu scholarship a makarantar salmal (makarantar da tafi kowace makaranta matsayi a Kaf kasar, ta yayan masu hannu da shuni ce hatta yayan shugaban kasa da jida dukiya can suke)

Farincikine ya lullube uban yana Allah y sa albarka yata kuma Ina farinciki da hakan Ina kuma alfahari dake akoda yaushe.

Kallon mahaifiyarta yayi wadda yaga mud dinta ya canza, yace mekefaruwa ko bakya farincikine bawai haka bane Amma Ina tunanin yanda menaal zatayi cudanya da yayan manyar kasarnan ita bakuma kowa ba ubanta beda komai hasalima ubanta messanger ne,tayi hakuri kawai tayi dede irintasu, ni aganina hakan shine mafita.

Sauke ajiyar zuciya uban yayi Dan shima yasan akwai matsala babba gameda yin hakan Amma mazewa yayi bakomai tartare da hakan muyi mata addua kawai, Amma makaranta bazaafasa taba.......

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune yake kan kujera ta alfarma Sanye cikin suit mai balain tsada da kyau, fuskarnan babu alamar annuri kokadan, Amma hakan baisa mugun kyawun da Allah yayi masa yafito ba dominkuwa kyayyawane nakarshe gashi far sol, dagowa yayi cike da izza da mulki yana nunida hannu akan wani takalmi kirar Italy,

Wanda hakan kenufin shiyake bukata da sauri maid dinsa yayi saurin dauko takalmin cike da girmamawa yaduka domin saka masa, bayan yagama saiga wasu maid din daukeda turarensa dakuma agogonsa da zobbansa na gold acikin trey picking din wanda sukayi masa yayi akakoma da sauran,wanan maid din nasa y kara dauka yamakala masa agogon ya zura masa gobe yakuma fesa masa designers din turarukansa

hair dressers dinsa suka shigo Don dressing masa kai bayan kowa ya kammala duties dinsa,yagama shirinsa tsab mikewa yayi ahankali yana kallon kansa cikin madubi shikansa yasan yayi kyau matuka.

Tafiya yakeyi cikin kasaita ya isa katafaren daining Inda aka jera masa abinci yafi kala goma nuna wa enda yakeso yayi aka kawo masa gabansa yafara ci ahankali gakuma guards dinsa suna jiransa abaya saida ya kammala cin abincin tsab tukunna yamike duk guids din nasa suka biyoshi dede bakin wata kofa duk suka tsaya wani daga cikinsu yabude masa ya shiga Shi kadai.....

Da sallama ya shiga yaganta zaune kan kujera ta alfarma, saida tadau mintina sannan tadaga kai ta kalleshi gaisheta yayi yace zaiwuce makaranta daga masa kai tayi kawai yajuya cikin takaici irinna halin uwarsa da kuma muguwar tsanarta na karuwa...

Fitowa yayi suka Bishi wata shegeyar mota aka dauko kirar Benz mai masifar tsada da kayau baka sai sheki takeyi shiga gidan baya yayi driver ya ja sai kuma mota biyu ta escort daya a gaba daya a baya sukuma suna tsakiya........

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Dasssafe tamike tayi wanka taci abinci, kayan da babanta ya goge mata tadauko tasaka tayi kyau a dede class dinta shima baban nata wanka yayi ya aro motar makwafcinsinsa akan zaikaita makaranta, tashiga suka tafi Don kar arena masa yarinya......

Adede Inda ake parking motoci suka faka motoci tagani masu masifa kyau da tsada yan manya kowa sai drivern sa ke fakawa dashi suna fitowa itama fitowa tayi tana kallan su, sunata wucewa wasu yanmatane su biyu sai yauki suke suka juyo suna mata kallon wulakanci juyawa sukayi suka fashe da dariya, wucewa tayi bata bi takansu ba Don dama tasan zaayi hakan

Tafiya take tana kalle, bakuma tasan Inda take zuwa ba, gardens taketa wuce masu ban shawa tana kallon tsari dakuma haduwa irinta makarantar wani swimming pool tagani tayi murmushi sbda tana son ruwa , aranta tace wallahi sai na rinka zuwa gurarennan , cigaba da tafiya tayi tana kalle kalle wata kujera ta hango kalkashin da mutum zaune yana latsawaya karasawa kusa da gun tayi ,wata ni'itamciyar iska ce wacce ta gauraye da kamshi turarensa mai dadin gaske saida talumshe ido

Sarai yasan dazuwan mutum Amma ko dagowa beyiba saida tazauna kusa da shi sannan ya dago Dan ganin wani isasshenne ya zauna kusa dashi Don a makarantar inba friends dinsa babu wanda isa

Direct kallonta yayi, dagowa tayi ta saki murmushi Don ganin kyayyawa fuska sa dukda a daure take tamau babu annuri

Cewa tayi sannu Dan Allah inane zankoma cikin skul wallahi narasa hanya ne ni new comma ce kallonta yayi up nd down yayi mata direction da hannu mikewa tayi da murmushi tana godiya ta kama hanyar da nuna mata ya bita da kallo.....

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
ABDULMALEEK MUH'D SALAHUDDEN shine ainihi sunan Shi Amma Mafiyawanci maleek ake kiransa, saurayine mai kimanin shekara 27 fari ne kuma kyayawan gaskene, yataso cikin mulki, kudi, da kuma gatan gasken, mahaifinsa shine shugaban kasar Egypt , su biyu ne gun mahaifiyarsa daga shi sai yarsa maleeka wacce ke auren Dan shugaban kasar Sudan.

Mahaifiyarsa zulaikha matace wacce bazata wuce shekara 50 ba Amma kudi da jindadi da kuma tsabar mulki sunsa Sam shekarun basuyi kama da itaba, matace ita mai tsaurin raayi da Kuma mugunta ga kyamar talaka ga balain izza da girman Kai, yanzu haka ma itake gudanar da mulkin kasar yanda take So..

Maleek tinda yataso baya farinciki da yanda ya iske gidan su sbda baisan dadin uwaba sbda ita mahaifiyarsu Sam batada lokacin jin damuwarsu ko Kuma kusantarsa sabgar mulki ta rufe mata idanu, don haka maleek baitashi cikin farinciki ba, yakuma tashi da wasu irin halaye, tin tasowarsa yake tare childhood frnds dinsa su biyu kowa yasansu tare harshiyasa akecemasu tripet maleek,muhassin, muhsin.

Muhassin shi Dan tsohon shugaban kasane Wanda yarasu a dalilin hatsarin jirgi kuma dukcikin frnds din yafi shakuwa da maleek

Muhsin kuwa Dan hamshaqin Dan kasuwane mai kudin gaske bafiye zama kasar bama Amma dukansu abokanjuna ne.

Baban maleek shine malallakin kamfanin salmal (combination din sunan salahudeen da maleek) wanda kamfanin ya kunshi makaranta, jirginsama jirgin ruwa mall da supermarkets da sauransu...

Itakuwa menaal Abdullahi yar kimanin shekara 18 ce itama subiyune a gun mahaifansu itada kaninta amman kanin yarasu tin yana karami dede rufin asiri sunada shi Don abinci baya gagararsu Don babanta massenger ne wani kanfani  Don su samu rufin asiri.

Wannan kenan.......



Mrs Abdool ce..



Vote and comment

"MALEEK"Where stories live. Discover now