MALEEK 03

1.2K 94 4
                                    

❤️❤️_*MALEEK*_ ❤️❤️

*REVISED EDITION*

✍️MRS ABDOOL

*03*

Har cikin zuciyarsa yaji Dadi Don koba komai ta Dan'dani irin embrassment din da tayi masa gaban mutane,

Jiyawa tayi da gudu tafice sbda komai zai iyafaruwa a lokacin, zuwa tayi tasamu wani guri data tabbata bakowa, lokaci guda ta fashe da kuka mai cin rai Don yanda take jin zuciyarta da take yanzu inbata yi kukaba batasan Abinda zaifaru da itaba kuma lalle tasa aikin maleek ne wannan

Kuka takeyi kasharban tana Maida masa maganganu...

Allah ya isa mugu kawai kuma wallahi bazan yafeba saina rama nizaka kunyata gaban alumma, nasan kafi karfina Amma wallahi bazan barkaba koba yanzuba.....

Haka tacigaba da maganganu da sharbar kukan iya karfinta

Muhassin ne zaune  yana karatun magazine don aikinsa kenan latsawaya ko karatun magazine donshi baya San hayaniya Sam ya gwammace ya zo yazauna nan shi kadai, hayaniya yaji da shesshekar kuka ta ishe yasa ya taso don ganin waye,Tana tsaye taji alamar mutum a bayan ta tayi saurin goge hawayen dake fuskarta don kar aga gazawarta tajuyo Don ganin kowaye, lokaci guda shima tafara tsoransa  sbda batasan ko halinsu daya ba,

Takowa yayi kusada ita yana kallon ta up and down cikin sanyi yace wai meyasa kincika surutu ne bakisan Bana son hayaniyaba shiyasa nake zama nan duk Kin bi kin ishe ni da kuka Bana son kuka fa.

Kanta tasauke kasa duk kunya ta dameta Don tasan yaji Abinda tace,

cewa yayi meyasameki haka, Don yasan baiwuce aikin maleek ba

Kamar jira take sauran kwallan datayi kokarin sharrr taji sunfara gangarowa

Dagowa yayi ya kalle ta na yan mintoci,tausayi tabashi baisan sanda yajawota jikinsa tsam ya riketaba,

Zaro ido tayi gabantane nafaduwa faduwa tafara kokarin kwace kanta, shikuwa babu abin yaji don shi agunshi bawani abu bane,
cikin sanyin murya yace kifita harkar MS Don muma hakuri muke dashi  bashida kirki kuma baida tausayi,

Gyada masa kai tayi tana share hawaye
hannu yasa aljihu yazaro hankici ya danka mata a hannu fuskarsa ba walwala yajuya yawuce..

Hankicip din tadago  tana kallo tace kamar duk yafisu kirki Amma ban taba ganin ko murmushi yayiba ko meyasa oho gashikuma Dan iska ne.

Bayan  tawanke fuskar ta karkade kurar pawdern da suka zuba mata, tana fitowa sukayi karo da Aisha tace ai kenake nema, kingade Abinda nake fadamiki ko to wallahi kadan ma kika gani indai maleek ne babu wanda baisan halinshiba ko kallonta ma menaal batayiba ta gaba,

Aisha tamika mata kaya tace gashi jeki canja yanzu nama driver waya yakawo miki, karba tayi ta taje ta canja dawo,

Cikin makaranta suka koma Don basu gama lec ba.

Zaune suka a aji shikuwa Malik da ka ganshi kasan yana cikin annashuwa yau sai murmushi yake shikadai,

muhassinne yace MS whts d gud news al about, nan ya labartamasa Abinda yafaru yace kuma naji Dadi Don Naga abin yamata ciwo.

Kade bari wallahi karta Rena ka Don nasan itama bazata hakura in ba zata ce sai ta rama ne kuma daga Nan reni ya shiga tsakaninku inkuma sonta kake yi kayi magana da wuri kar wani yamaka shigar sauri.

Dindu ya dirka masa abaya yace Allah Shi kyauta duk yanmatana mezanyi da wannan mummunar kucaka da ita gasu subby naki saurare sai ita mtsss yayi tsaki yabargun.

Lecture akeyi Amma takasa fahimtar komai sbda bakin cin duk ya ishe koda aka tashi bata tsaya ko ina ba gida kawai tawuce shima tana isa daki tazarce koda mamy ta tambayeta cewa tayi wai kanta ke ciwo sbda gaba daya maleek ya canza Mata mood adaki ta wuni, daga yamma tadauko littafanta tana karatu Don ita maabociyar son karatuce gurin karfe 9:30 ta tashi ta dauro alwalla tayi shafa'I da wutiri ta kwanta harta kwanta taje ta dauko hankacip dinda muhassin yabata ta dinga kallo  shinshinwa tayi ta lumshe ido sbda tana masifar San kamshinsa yana hannunta ta tuno lokacinda ya rungumeta hannunta biyu tasaka ta rufe idanunta tareda sakin murmushi a haka har barci ya dauketa.

Washegari sai gurarin karfe 10 tashiga skul kodatashiga saitaga su maleek basu zoba tadan ji badadi Don taso ganin muhassin, bayan nan saida tajera kusan kwana biyu bata gansuba gashi bawanda zata tambaya.

Ranar wata Friday suna zaune cikin garden itada Aisha suna yan ciye ciyensu suna nishadi Aisha tazuki juice abikinta garin dariya ta kware juyawatayi ta fesar da nabakin jitayi kamar tazuba ajikin mutum waigawar dazatayi sai taga maleek tsaye shida frnds dinsa tsorata tayi tafara in ina tana

...kaaayii hakuurii wallahi bansan kana gurin ba Dan Allah kaimin rai saiga kwalla a idonta duk ta tsorata

Dauke Kai yayi fuskarsa a matukar daure yace kicire hijab dinki kigogeshi nace

Dan Allah kayi hakuri wallahi bada gangan nayiba tafada tana sakin wani kukan

kinsan nawa suit dinnan take to wallahi sai tasiyeki da gidan ku gaba daya

Rokonsa take tayi Amma yaki ko kallonta

Mikewa menal tayi ta matso kusada shi tace bari na gogema..

Murmushi yayi najindadi tunaninsa tasaduda tafara tsoronshi,

Juice dinda ke hannunta ta watsa masa a fuska gabaki daya tana binsa da harara.

Dagowa yayi a mugun fusace yana kallonta,

Daga masa gira daya tayi tareda sakin wani kayataccen murmushi tana 2,1 Jan hannun Aisha tayi suka bar gun.

Kaitsaye office dinsa yawuce zuciyarsa namasa zafi yana shiga yqa wanke fuskarsa ya bude fridge ya kwankwadi ruwan sanyi yana shanyewa yasake tumbla din yafashe akasa, hannu ya dunkule yadake Bencin dake gabansa yana furzarda iska cikin takaici yace I am gonna deal wit dis chick,

Waya ya buga ma drivern yazo ya daukesa yafasa zaman makarantar

Aisha tace ma menaal kinsan me kikayi kuwa

Kwaraikuwa nasani...

Nizan wuce muhadu gobe sukayi sallama kowa yawuce.

Washegari kimanin karfe Tara tashigo skul Amma basu hadu da Aisha ba Don ita batada lecture ..

Komawa tayi ta zauna a gardens dinda suka Saba zama, gang dinsu idris ta hango suna kusanto ta suna zuwa tagefenta suka yarda bawon ayaba suka wuce basu tasayaba suka ganin haka yasa itakuma bata kawo komai a ranta bayan tagama duk abinda zatayi tamike da shirin tafiya bawon ayabannan tataka suuuu ta zame saidai tajita akasa wani azaba taji akanta Don tayi mugun buguwa, dafe kan tayi kwallan azaba na bin kuncinta, dariya taji an tuntsuredashi daga bayanta tana waigawa taga dinjin jamaa suna kallonta mikewa akunyace ta mike cikin dauriya ta wuce bata kula suba.

Direct office din maleek ta nufa bata ko tsaya knocking ba tabankada kofar kai tsaye tace maleek kake kowa nazone Don bugemaka warning kafita harkata Don wallahi Indai bazaka gajiba karkasa ran nima zan gaji muzuba mugani dani da Kai wazai gaji tana gamawa bata jira ce warsaba tayi gaba tanajin tsanarsa

Dariya ya Tutsireda ita yanacewa I love her courage Amma kinada karfin hali yarinya muzuba mugani....



*OUMM HANEEF*

"MALEEK"Where stories live. Discover now