maleek 5

1K 96 6
                                    

❤️❤️*_MALEEK_*❤️❤️

*✍️MRS ABDOOL*

*REVISED EDITION*

*05*

 

Baiko gama lectures dinba yayi tafiyarsa gida,

Tinda yashiga daki yarufe baisake budewa ba ko abinci beci ba, duk Maids dinsa sundamu Amma kowa na tsoron shiga dakin sa Don ze iya musu rashin mutunci koma mutum ya rasa aikinshi

zaune yake yayi nesa cikin duniyar tunani ya janyo wayarsa yana Kara zooming pic dinda yayi mata bata Sani tana dariya, kura ma pic din ido yayi yana kallon ta bawata fara bace sannan baza ka kirata mai gun kyauba Amma dede masha allah ba mummuna bace Don yafita kyau sosai ba kadan ba, to yaushe wannan mugun son yayi masa kamu haka, Amma inko hakane soyyaya batai masa adalciba data so wannan yarinyar duk cikin yanmatansa, dukda bashi kesonsuba sune suke sonsa hasalima shi baitaba soyyayya ba sbda girman kansa da gadara baze barshi yaso wata ba,

mikewa yayi Jiki ba kwari ga kansa namasa wani mugun ciwo, alwalla ya dauro ya gabatarda salla yana idarwa wani mugun zazzabi ya lullube shi bargo yaja ya rufe kanshi dashi.

Bayan wucewar maleek muhassin yakalle meenal yace haba frnd meyasa kike ma maleek wulakanci, meyasa kika tsane shi wallahi yana sonki sosai,

gabantane yafadi tayi kicin kicin da fuska tace baganeba, yace maleek ya canza daga halayensa wallahi kuma maleek abin tausayine inkikayi duba da yanayin rayuwarsa, da sauri ta datseshi tace ai kafishi zama abin tausayi tinda Kai marayane shi fa?

Bata bari yabata amsaba tamike cikin hanzari tace natafi muhadu gobe

Tinda takoma gida zuciyarta fal tunani me muhassin yake nufi da maleek nasabta kodai shi yadena Sontane kokuwa yana nufin ita kadai kesonshi shi baisan abinda takeyi ba zuciyarta fal da tunani Amma babu mai amsa mata.

Maleek Sai gurin 11 ya tashi yadanji Saukin zazzabin sosai wanka yayi yashirya cikin shadda mai shegeyar tsada Wanda daganinta zaka iya yimata kudi, cikin dinkin tazarce kalar ash wandan tayi masa mugun kyau gawata zanna ya Dora mai muguwar tsada alkalamina baze iya siffanta irin haduwarda maleek yayiba readers kowa ya hasaso iya hassensa,Kai In fact everything about him is expensive his just lookin takeaway bakai masa kallo daya kadauke ido.

fitowa yayi shida excort dinsa wata BMW 2019 latest kalar baka mai sheki Naga anbude masa gidan baya yashige duk inda ya gifta tamkar anyi ambaliyar turare, mota ukku sukayi daya gaba daya baya,

SALMAL shopping mall suka isa yayi order Abinda yake bukata babata lokaci sai gashi Ana zuba kaya niki niki a boot direct unguwarsu meenal ya nufa Don akwai wani guard dinsa da yasa tuni ya nemo masa gidan

Adede kofar gidan suka ja Burki fitowa yayi cikin tafiyarsa ta takama suka nufi kofar gidan knockin akamasa ba jimawa mahaifiyarta ta bude kofar zaro ido tayi Takoma da sauri tace malam zokaga wannan Dan president din Wanda ake nunowa a tv, abba dabema fahimci Abinda akecewa ya Mike yafita shima,

sorosoro yayi bakin kofa ganin Wanda betaba tunani ba, jikinsa na rawa yabude ya masa iso

Aka bashi gurin zama,  zamayayi yana bin ko ina agidan da kallo yana mamakin yadda Dan Adam ze iya rayuwa a gida nan a yanda yasaba ganin nasu gidan kamar a lahira, dukawa yayi har kasa ya gaisheda Abban, yace dama bawani abu yakowani ba akan maganar Minal ne sun dan Dade suna tattaunawa saiga mamy da pure water da Dan lemo a tray, aransa yace ai na sha wannan ruwan har drip sai ansamin, sun gaisa a mutunce kafin daga karshe akafara shigo musu da cartoon din taliya, rice, indomie, bottle water,drinks eggs dade kayan ciye ciye.

godia Abba yashiga zubawa kamar zai Ari baki, daze tafi rafar dubu kudi ya aje musu sunata godia yawuce akan ze sake dawowa.

Suna tafiya abba ya kwashe kudin ya zuba aljihu ransa fes yana murna,

yata nada kashin arziki Dan shugaban kasafa kuce nikam kakata tayanke saka,

mamy tace haba malam banyi zaton haka daga garekaba wallahi kwata kwata banji Dadi ba, Donni bansan son zancen nan kwarya tabi kwarya inji baushe yafi karfin meenal jelar rakumi tayi nisa da kasa kadesake tunani tafice Ranta ba Dadi..

Daga nan makaranta yawuce ransa fes kamar anmasa albishir da aljannan sai fara yake zubawa gashi yayi masifar kyau cikin manyan kaya Abinda mutane basu Saba ganiba,

Direct gun muhassin ya isa sukayi hand shake, muhassin cike da zolaya yace wannan ai ko yauce ranar sai haka , abokina yayade? Yafada cikeda zolaya,muhsin yace ko meenal ta amince ne muhada party yanzu, duk dariya suka tuntsire dashi suna tafawa

Meenal nakomawa gida taga kaya niki niki tace mamy wannan fa daga ina, Kai tsaye tace saurayinkine yakawo,

murmushi tayi tace wai muhassin?

Wani muhassin karki renemin wayo, maleek din fa, saida gaban ta yafadi yaushe maleek yasan gidan mu meye dalilinsa na kawo wannan kayan me yake nufi da hakan, mamy ce ta katse mata tunani da kinga meenal kifita harkar yaran manyan nan kinsan nibanson kwadayi kuma kwadayi babu Abinda yake jajowa se wulakanci kinajina ko ni ayanda muke nagode ma allah tinda bamu rasa ci koshaba bare sutura babu ruwanki dashi kisami dede ke Dan talakawa inafatar kin fahimta, Gyada mata Kai tayi

Abba dake gefe yace ki kwantar da hankalin ki babu namijin dayafi karfin mace inde kinasonsa angama tsiyarta ace bakisonsa kawai, da kyar Taja kafarta tashige daki cike da tunani kala kala tanajin ranta badadi tarasa dalili kuma......

It's all about maleek Ina masoyan maleek let me see ur hands



*OUMM HANEEF*

"MALEEK"Where stories live. Discover now